BURIN mawaƙiya kuma jarumar Kannywood Hajara Idi Moris ya cika, an ɗaura auren ta da sahibin ta Malam Mika’il Nura a yau Lahadi, 4 ga Satumba, 2022.
An ɗaura auren Mika’il da Hajara, wadda aka fi sani da Hajjo, da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ƙofar gidan mahaifin ta mai lamba LM 6, Titin Gwarzo, Tudun Wada, Kaduna, a kan sadaki N50,000.
Abin mamaki, ba a ga ‘yan fim da mawaƙa da yawa a wurin ɗaurin auren ba sai mawaƙa huɗu, wato Ɗanjummai Ceevee, Salisu Autan Jalatu, Ɗayyabu D.Y. da Tahir Ulafa.

Amma kuma mawaƙan asharalle, abokan sana’ar mahaifin amaryar, sun nuna kara, sun halarta, duk da yake mahaifin ta ba ya raye. Ana gama ɗaurin auren su ka ci gaba baje kolin su da waƙoƙin su na asharalle, inda su ka yi wa bikin laƙabi da ‘Artises Day’.
Allah ya ba da zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.
