FURODUSA kuma jarumi a Kannywood, Mustapha Hussain, wanda aka fi sani da Musty Fashion, ya bayyana farin cikin sa game da irin ƙaunar da abokan sana’ar sa, ‘yan’uwa da abokan arziƙi su ka nuna masa a yau da ya ke murnar zagayowar ranar haihuwar sa.
Da ya ke zantawa da mujallar Fim, Musty Fashion, wanda mazaunin Kaduna ne, ya ce, “Ina matuƙar farin ciki a wannan rana ta zagayowar ranar haihuwa na. Ina kuma godiya ga ‘yan’uwa tun daga ‘yan fim da abokan arziƙi da su ka taya ni murna tare da ‘posting’ ɗin hotuna na a soshiya midiya, tun daga kan su Ali Nuhu, Abba El-Mustapha, Nazir Ɗanhajiya, Abdul M. Shareef da dai sauran manyan ‘yan wasan Hausa da ƙanana. Babu abin da zan ce sai fatan Allah ya bar zumunci, kuma ya ƙara mana lafiya da zaman lafiya a ƙasar mu baki ɗaya.”

Me Musty Fashion zai ce game da harkar sa a Kannywood? Sai ya amsa da cewa, “Wannan shekara ina cikin murna da farin ciki fiye da shekaru da su ka gabata, ganin irin cigaba da na ke samu a ko da yaushe a cikin rayuwa ta, musamman a wannan masana’antar tamu. Idan ka duba, tun daga fari ni ba kowa ba ne, na shigo wannan harkar, tun ina bin ‘yan fim ina neman a kira ni aikin P.A. (production assistant), wato ɗan aike, har ta kai ga yau Musty Fashion ne ya zama jarumi, zan je waje a ce ga wane ya zo, kullum cikin kira waya ta ta ke wajen masoya na, su na gaishe ni, su na min fatan alkhairi. Abin murna ne sosai a gare ni.
“Abu na biyu, na zo na zama ‘continuity’ a wannan masana’anta, wanda ake damawa da ni sosai. Babban abin murnar, yau gani na zama furodusa a Kannywood, al’umma su na ɗaukar miliyoyin su su ba ni na yi masu aikin fim ba tare da sun ji ɗar a zuciyar su ba, kuma cikin ikon Allah na ke gudanar da ayyukan, mu rabu lafiya da kowa, su na murna ina murna.
“Babu abin da zan ce wa Allah sai godiya. Ni sai dai na ce nawa na kyau a industiri. Allah ya sa na gama ‘career’ na lafiya ba tare da na cuci kowa ba.”
Finafinan da Musty Fashiin ya shirya su ne ‘Gadara Series’, ‘Madafar Ƙauna Series’, yanzu kuma ya na kan ɗaukar ‘Yahoo Boys Series’, wanda ya tara jarumai irin su Ali Nuhu, Tahir Fagge, Alhassan Kwalle, Abdul M. Shareef, Bilkisu Shema, Ali Dawayya, Isa Feroskhan, Rayya Kwana Casa’in, da dai sauran su.
