• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 8, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rikici tsakanin jarumin barkwanci Ali Maɗagwal da surukan sa ya janyo an hana shi shiga asibitin da matar sa ta haihu

by DAGA ABBA MUHAMMAD
November 14, 2022
in Labarai
0
Ali da Hauwa'u za su Legas cikin jirgin sama jim kaɗan bayan ɗaurin auren su

Ali da Hauwa'u za su Legas cikin jirgin sama jim kaɗan bayan ɗaurin auren su

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WANI rikici ya ɓarke a tsakanin jarumin barkwanci Aliyu Muhammad Idris, wanda aka fi sani da Ali Artwork ko Maɗagwal, da surukan sa a kan aikin fiɗa da aka yi wa matar sa a wajen haihuwa a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna.

Majiya mai tushe ta faɗa wa mujallar Fim cewa a yanzu haka hukumar asibitin ta hana shi shiga asibitin saboda rigimar da ya yi a kan aikin da aka yi wa matar tasa, Hauwa’u Muhammad Bello, a safiyar yau.

Majiyar ta shaida wa wakilin mu cewa Ali, wanda ƙwararren mai zanen fosta ne kuma editan finafinai, ya tada hayaniya ne a asibitin a lokacin da likita ya ga dacewar a yi mata aikin ‘caesarian section’ (CS) domin a fitar da ɗan da ke cikin ta.

Ali ya finjire ya ce ko sama da ƙasa za su haɗe bai yarda a yanka masa mata ba tunda dai haihuwar fari ce inda ake daɗewa ana naƙuda.

Da aka nuna masa cewar matar sa fa ta jima cikin naƙuda kuma har ta fita hayyacin ta, ga shi za ta iya rasa ran ta, sai ya ce idan ma hakan ta faru ai ta yi shahada ne.

Majiyar, wadda ke kusa da surukan Ali Artwork ɗin, ta faɗa wa mujallar Fim cewa jarumin na Kannywood ya yi sa-in-sa da ƙanwar uwar matar sa, wadda mazauniyar Kaduna ce, har ya na faɗin zai dake ta. Ita kuma ta ce “in ya taɓa ta kuwa sai ta kafa masa tarihi”.

Majiyar ta ce saboda hayaniyar da Ali Artwork ya sa a asibitin sai da wasu su ka kama shi da duka, kuma aka fitar da shi daga asibitin da ƙarfin tsiya.

Daga nan sai yayar matar tasa, wadda ta zo daga Kano, ta sanya hannu a takardar izinin a yi aikin.

Likita ya yi wa Hauwa’u aiki, aka samu fitar da ɗa namiji lafiyayye a yau Litinin, 14 ga Nuwamba, 2022 da misalin ƙarfe 6:00 na safe.

Majiyar mu ta ce da gari ya waye yau Ali ya je asibitin ya buƙaci a ba shi ɗan sa ya yi masa huɗuba, abin da da farko yayar matar ta hana amma aka ba ta magana ta amince.

Ali ya yi wa ɗan sa huɗuba, ya raɗa masa suna Muhammad, amma za su riƙa kiran sa da Aryan.

Sai dai kuma da likitoci su ka ji labarin ya zo asibitin sai su ka ba da umarnin kada a ƙara barin sa ya shiga asibitin saboda kada ya kuma ta da hankalin jama’a.

A yau da rana dai mahaifiyar matar Alin, mai suna Amina, ta garzayo zuwa Kaduna daga Kano saboda halin da ‘yar tata ta ke ciki. A yanzu haka ta na asibitin ta na kula da ɗiyar da kuma jikan ta da aka samu.

Wata majiya a asibitin ta faɗa wa wakilin mu cewa yanzu haka ana fama da shawo kan hawan jini da Hauwa’u ta samu sakamakon wannan al’amari.

Majiyar ta ce ko kwabo Ali bai kashe ba kan wannan haihuwar domin kuɗin aikin ma su dangin matar ne su ka biya.

Majiyar ta ƙara da cewa, “Auren ma ya na tangal-tangal saboda wannan matsalar. Mamar Hauwa’u ta ce da zaran ‘yar ta ta samu sauƙi za ta ɗauke ta ne ta tafi da ita Kano. Kuma kila Ali ya ce bai yarda ba, to ka ga komai na iya faruwa daga nan.”

Sai dai kuma Ali Maɗagwal ya ƙaryata duk wannan labarin da ake yaɗawa, musamman da aka ce an lakaɗa masa duka a asibitin.

Da ya ke zantawa da mujallar Fim, ya ce, “Wannan magana ƙarya ne, ba gaskiya ba ne wallahi.”

A kan bidiyon hayaniyar tasu wanda ya ɓulla a soshiyal midiya, Maɗagwal ya ce, “Wannan bidiyon kuma magana ne a kan an ce za a yi aiki na ce ba za yi ba, za ta haihu da kan ta. Kuma likitocin su su ka ba mu zaɓi guda biyu, za ta iya haihuwa da kan ta, ko kuma za su iya yi mata aiki. 

“Sai aka ce in zaɓa, sai na ce a bari ta haihu da kan ta. Wata daga cikin dangin matar tawa ce ta matsa ta ce za ta mutu da sauran su, shi ne mu ke jayayya da su, ina a’a ni ba za a yi mata aiki ba tunda kun ce za ta iya haihuwa da kan ta, ba za a yi mata aiki a je a yanka min mata ba.

“Kuma a jiyan ne ma EDD ɗin ta na haihuwa ya ke cika. Kuma ka ga haihuwar fari ne, kuma haihuwar fari ba da wuri ake haihuwa ba; wasu ma su kan yi kwana biyu, wasu uku ma su na naƙuda.

“Wannan shi ne gaskiyar abin da ya faru. Amma babu wanda ya dake ni. Bidiyon nan ban san su wa su ka ɗauke shi ba.”

Hauwa’u dai ‘yar Adamawa ce wadda ‘yar’auta ce a wajen mahaifiyar ta.

Ali ya fara ganin ta ne a Kano wata rana ta na hanyar dawowa daga Islamiyya, daga nan ya shiga neman auren ta har Allah ya ba shi sa’a.

Mujallar Fim ta taɓa ba da labarin cewa auren su, wanda na fari ne, an ɗaura shi da misalin ƙarfe 2:00 na ranar Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 a masallacin Juma’a na Filin Kashu da ke Unguwa Uku, Kano, a kan sadaki N100,000.

Loading

Tags: Ali ArtworkAsibitin Barau DikkohaihuwaHauwa'u Muhammad BelloKadunaKanoMaɗagwalMuhammad AryanrikiciUnguwa Uku
Previous Post

INEC da hukumomin tsaro sun yi taron gaggawa don hana ci gaba da cinna wa ofisoshin hukumar wuta

Next Post

Manufar aikin kwarmato da na ke yi wa Gwamna Ganduje – Nabraska

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Mustapha Badamasi Nabraska

Manufar aikin kwarmato da na ke yi wa Gwamna Ganduje - Nabraska

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!