• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Atiku: Zan sayar da tashoshin jiragen ruwa, matatun mai da tashoshin jiragen ƙasa idan na ci zaɓe

by DAGA WAKILIN MU
November 19, 2022
in Nijeriya
0
Atiku Abubakar ya na gabatar da jawabi

Atiku Abubakar ya na gabatar da jawabi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAN takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin cewa idan ya ci zaɓe zai damƙa manyan ayyukan raya ƙasa a hannun kamfanoni masu zaman kan su, ta yadda zai sauƙaƙe wa Gwamnatin Tarayya nauyi da wahalhalun kashe maƙudan kuɗaɗe wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Atiku ya bayyana haka a wani taron ganawa da ya yi da Kungiyar Editoci ta Nijeriya (INEC) a Legas a ranar Laraba.

Ya ce: “Idan ku ka kalli irin gagarumin aikin da ke gaban gwamnati a ƙasar nan, kamar gina tashoshin jiragen ruwa, gina hanyoyin jiragen ƙasa, to ana buƙatar maƙudan kuɗaɗe ne. Kuma kun dai san a yanzu gwamnati ba ta da waɗannan kuɗaɗen.

“Har gara a damƙa waɗannan ayyuka ga kamfanoni masu zaman kan su, a zaftare ko a cire masu haraji. A gina manyan ayyukan da kuɗaɗen su, sannan su kula su karɓi kuɗaɗen da su ka kashe wajen gudanar da ayyukan. To ta haka ne za mu samu cigaba, bunƙasa, samar da ayyukan yi da kuma samun yalwar arziki a faɗin ƙasar nan.”

 A wurin taron dai Atiku ya yi alƙawarin ɗaukar ‘yan sanda 500,000 da sojoji 500,000 aiki idan ya zama shugaban ƙasa.

Ɗan takarar ya kuma ce za a wadatar da su da ingantattun kayan aiki tare da ba su horo domin samar da tsaro, aikin yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce wannan ƙudiri na cikin ajandojin sa biyar muddin ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

Ajandar sa ta biyu kuwa cewa ita ce farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa wanda kowa ya san ya taɓarɓare.

Ya ce: “Na ƙudiri aniyar ci gaba da irin tsarin da mu ka yi tsakanin 1999 zuwa 2007, lokacin ina mataimakin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo. Za mu bai wa kamfanoni masu zaman kan su damar samun sauƙin ayyukan bunƙasa tattalin arziki.”

Daga cikin abin da zai yi wa kamfanonin, Atiku ya ce zai rage masu haraji ta yadda za su riƙa yin manyan ayyukan raya ƙasa, kamar gina tashoshin ruwa, manyan titina, hanyoyin jiragen ƙasa da sauran manyan ayyuka masu cin kuɗaɗe sosai, “musamman tunda gwamnati ba irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe gare ta ba.”

“Saboda zan zaftare wa kamfanoni da masana’antu haraji, ta yadda su kuma za su riƙa gina manyan ayyukan raya ƙasa, waɗanda ke buƙatar kashe maƙudan kuɗaɗe kafin aikwatar da su.”

Atiku ya ce zai rungumi kowane yanki ba tare da nuna bambanci ko fifiko ba. Ya ce fifikon wani yanki da wannan gwamnatin ta riƙa bayarwa wajen raba muƙamai ba zai faru a gwamnatin sa ba idan ya zama shugaban ƙasa.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Aminu Tambuwal, mai suna Mohammed Bello ya fitar bayan ganawar, Daraktan Kamfen ɗin Atiku/Okowa 2023, wato Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, ya jinjina wa NGE da Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Ƙasa (NUJ) wajen jajircewar su domin ganin dimokiraɗiyya ta ɗore a ƙasar nan. 

Ya ce Atiku a shirye ya ke ya fara aiki wurjanjan da zaran an zaɓe ya zama shugaban ƙasa.

Loading

Tags: Aminu Waziri TambuwalAtiku AbubakareditociNGEOlusegun ObasanjoPDPprivatisationZaɓen 2023
Previous Post

Zaɓen 2023: Mun yi shirin yin zagaye na biyu idan zaɓen shugaban ƙasa bai fitar da ɗan takara ba, inji INEC

Next Post

Jarumar Kannywood Halima Atete za ta amarce Asabar mai zuwa

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Amarya Halima Yusuf Atete da angon ta, Mohammed Mohammed Kala

Jarumar Kannywood Halima Atete za ta amarce Asabar mai zuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!