• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: Mun yi shirin yin zagaye na biyu idan zaɓen shugaban ƙasa bai fitar da ɗan takara ba, inji INEC

by DAGA WAKILIN MU
November 19, 2022
in Nijeriya
0
Barista Festus Okoye ya na gabatar da jawabi ga manema labarai

Barista Festus Okoye ya na gabatar da jawabi ga manema labarai

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta yi shirin gudanar da zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa a 2023 idan hakan ta kama.

Kakakin hukumar, Barista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da editocin jaridu da wakilan kafafen yaɗa labarai a Abuja.

Ya ce da ma a bisa al’ada, INEC na yin irin wannan shiri a duk lokacin da za a yi zaɓen shugaban ƙasa, tun daga 1999.

Okoye ya ce a irin wannan shiri, tun da farko dai INEC za ta ruɓanya adadin ƙuri’un da za ta buga. Wato idan masu zaɓe su miliyan 93 ne, to INEC kan buga miliyan 186, ko da za a kai ga yin zagaye na biyu na zaɓen.

Wani sashe na manema labarai a taron

Ya ce: “Ana bugo ƙuri’un a lokaci ɗaya, saboda dokar ƙasa ta ce a yi zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa idan a zagaye a farko aka kasa samun wanda ya yi nasara. 

“Dalilin bugo su a lokaci ɗaya kuwa shi ne saboda dokar ƙasa ta bayar da ratar kwana 21 kacal tsakanin ranar da aka yi zaɓen farko da kuma ranar da za a yi zagaye na biyu.”

Okoye ya ce hukumar na shirya zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu ne “idan aka kasa samun wanda ya yi nasara a zagaye na farko.”

Ya ce: “Dokar ƙasa ta ce tilas wanda zai yi nasara ya fi sauran ‘yan takara yawan ƙuri’u. Kuma tilas ya samu aƙalla kashi 1/4 na kashi 2 bisa bisa 3 na ƙuri’un da aka kaɗa a jihohi da FCT Abuja.

“‘Yan takara biyu ne za su iya shiga zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa daga cikin jam’iyyu 18 da su ka shiga takara.

“Na farko shi ne wanda ya fi kowa yawan ƙuri’u, amma ya kasa samun aƙalla kashi 1/4 daga kashi 2 bisa 3 na yawan ƙuri’un jihohi da FCT Abuja.

“Sai kuma na biyun wanda zai yi zagaye na biyun, shi ne ya zo na biyu wajen samun kashi 1/4 na kashi 3 bisa 4 na ƙuri’un da aka kaɗa a jihohi da FCT Abuja.”

Okoye ya yi nuni da sashe na 134, ƙaramin sashe na 1 na Dokar Gwamnatin Tarayya, wanda ya wajibta sai wanda ya fi saura fifikon ƙuri’u ne za a ayyana cewa shi ya yi nasara.

Ya ce dukkan ƙuri’un da za a kaɗa da sauran kayan zaɓe su na ajiye a Babban Bankin Nijeriya (CBN).

Ya ce: “Na’urar tantance adadin ƙuri’un da aka kaɗa da tantance masu zaɓe, wato BVAS ne kaɗai ba mu bai wa CBN ajiya ba. Wannan kuwa saboda su na da matuƙar muhimmancin da su na wajen mu, bisa tsauraran matakan kulawar ɓangarorin jami’an tsaro.”

Loading

Tags: Dokar ZaɓeFestus OkoyeINECshugaban ƙasaZaɓen 2023zagaye na biyu
Previous Post

Abin da ya sa aka gan ni kwance a asibiti – Balarabe Jaji

Next Post

Atiku: Zan sayar da tashoshin jiragen ruwa, matatun mai da tashoshin jiragen ƙasa idan na ci zaɓe

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Atiku Abubakar ya na gabatar da jawabi

Atiku: Zan sayar da tashoshin jiragen ruwa, matatun mai da tashoshin jiragen ƙasa idan na ci zaɓe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!