JARUMA a Kannywood, Beatrice Williams Auta (Stella Arewa 24) ta bayyana dalilin rashin ganin ta da aka yi a finafinai na tsawon lokaci.
An ɗauki tsawon lokaci ba a ganin jarumar, wadda aka fi sani da suna Stella a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ na tashar Arewa 24, a cikin finafinai, musamman a shirin da aka san ta da shi.
A tattaunawar ta da mujallar Fim, Beatrice ta yi bayani kamar haka: “Ina nan, ba na ja baya ba ne. Na koma makaranta ne, yanzu kuma na kammala, na dawo harkar, tunda har na yi ‘signing contract’ da Arewa 24, don har na je mun yi shutin, ina ganin cikin satin nan zan fara shiga cikin shirin. Da ma makaranta ne ya sa na ɗan ja baya kaɗan.”
Ko yaya jarumar ta ke ganin tasirin ta a yanzu da ta dawo harkar? Sai ta amsa da cewa, “Ni ai a yanzu na dawo da ƙarfi na ne, tunda na zama furodusa, don na shirya wani ‘cooking show’ (shirin girke-girke) mai suna ‘In the Process’. Za a fara nuna shi a ‘African Magic’, saboda haka yanzu na dawo da ƙarfi na. Ni jaruma ce, kuma ni furodusa ce.

“Zan kuma ci gaba da fitowa a cikin finafinan Kannywood, don haka ina tallar kai na wurin sauran furodusoshi. Ina nan ‘available’, duk wanda ya ke son aiki da ni, ina nan ‘very much available’.”
Da mu ka tambaye ta yadda mu’amalar ta ta ke da sauran abokan sana’ar ta a yanzu, sai ta ce, “Lafiya lau, alhamdu lillah, tunda dai ban taɓa samun matsala da kowa ba, ko kuma in ce ba ni da matsala da kowa. Amma yanzu tunda na dawo, da ma can na ja kai ba a cika gani na ba, ina makaranta na zama ‘busy’, tunda yanzu na dawo da ƙarfi na, na gode Allah.”
Saƙon Beatrice ga masoyan ta shi ne: “Su yi haƙuri, na ɗan ja baya, duk da cewa ba da son rai na ba ne, kuma ban sanar da su ba. To yanzu na dawo, su shirya min, ni ma zan shirya masu. ‘I’m back for them’. Kada su gaji da ni, su ci gaba da bi na, su ci gaba da kallo na, su ci gaba da ba ni goyon baya na, sannan kuma su ci gaba da yi min addu’a.”
Haka kuma saƙon ta ga abokan sana’ar ta shi ne: “Manyan oganni na, irin su Ali Nuhu, Adam A. Zango da sauran su, yanzu na dawo. Da ma ina ayyuka da su, yanzu kuma na ƙara dawowa. Ina nan tare da su, don haka a ci gaba da saka ni a cikin ayyuka.
“Sannan manyan daraktoci da furodusoshin da ban taɓa aiki da su ba kuma, wannan lokaci ne da na ke da damar da zan same su in yi aiki tare da su. Ina fatan za su ba ni wannan damar da zan samu yin aiki da su. Na gode.”

