• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: Za mu sa ƙafar wando ɗaya da masu sayen ƙuri’a, inji INEC

by DAGA WAKILIN MU
December 20, 2022
in Nijeriya
0
Shugaban INEC, Farfesa Yakubu, ya na gabatar da jawabin sa

Shugaban INEC, Farfesa Yakubu, ya na gabatar da jawabin sa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya da cewa a zaɓen 2023 ta yi shirin yin fito-na-fito da masu sayen ƙuri’a, musamman a ranakun zaɓe.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi ga mahalartan wani taro da ya yi da hukumomin da ke ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe, tsaro, rashawa da cin hanci a ranar Litinin, a Abuja.

Yakubu ya ce, “Mun san abu ne mai wahala sosai, ba mai sauƙi ba, to amma INEC za ta yi bakin ƙoƙarin ganin ta daƙile masu bayar da kuɗi su na sayen ƙuri’u.

“Wasu ba za su ji daɗin wannan kyakkyawan aikin da za mu yi na ƙara tsaftace zaɓe ba. Don haka su ma za su bijiro da na su dabarun. Sai dai kuma INEC za ta haɗa kai da ‘yan sanda, EFCC da sauran hukumomin tsaro domin su taimaka wajen kashe kaifin masu sayen ƙuri’u a wurin zaɓe ko kafin ranar zaɓen.”

Yakubu ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya masu jefa ƙuri’a cewa su tuna ƙuri’ar su fa ‘yancin su ce. Don haka ya ce su yi amfani da hankali da hangen nesa,su daina sayar da ‘yancin su a kan wasu ‘yan kuɗi ƙalilan waɗanda za su kashe a rana ɗaya.

Wasu mahalartan taron

Ya kuma hore su da su kai wa INEC da jami’an tsaro rahoton masu sayen ƙuri’u. Kuma ya yi kira ga ƙungiyoyin rajin kare haƙƙi su saka batun fallasa masu sayen ƙuri’u a jerin ayyukan sa-idon da za su yi kafin da kuma ranar zaɓen 2023.

Hukumomin da su ka shirya taron tare da haɗin gwiwar INEC, sun haɗa da ICPC, EFCC, BBC, Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da Hukumar Ƙayyade Tsare-tsaren Tallace-tallace ta Nijeriya (APCON).

Wakiliyar shugaban EFCC Abdurasheed Bawa, Mrs. Hadiza Gamawa, ta na gabatar da jawabi

Loading

Previous Post

Sirrin kawowar mu shekara 9 da aure: Hira da Yerima Shettima da tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan

Next Post

‘Bakandamiya’ da na ke shiryawa ya fi duk wani fim da aka taɓa yi a Kannywood – Mansurah Isah

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Mansurah Isah

'Bakandamiya' da na ke shiryawa ya fi duk wani fim da aka taɓa yi a Kannywood - Mansurah Isah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!