• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 2, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result

  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Karɓuwa ga jama’a: Ba yi na ba ne – Baba Ɗan Audu

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 23, 2022
in Taurari
0
Rabi'u Mohammed Rikadawa (Dila ko Baba Ɗan Audu)

SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHAHARARREN jarumin barkwanci a Kannywood, Rabi’u Muhammad Rikadawa, wanda aka fi sani da Dila a da, a yanzu kuma Baba Ɗan Audu, ana iya cewa babu jarumin da sunan sa ke yawo ta ko ina kamar sa a cikin wannan shekarar ta 2022. Wannan dalilin ne ya sa mujallar Fim ta nemi jarumin ta tattauna da shi a kan rol ɗin da ya ke takawa na Baba Ɗan Audu a cikin shirin ‘Labari Na’, da yadda ya ke kallon kan sa a yanzu idan ya waiwaya baya.

Ga yadda tattaunawar ta kasance:

FIM: Za mu iya cewa a wannan shekarar kai ne jarumin da jama’a su ka fi magana a kan sa saboda matakin da ka ke takawa na Baba Ɗan Audu a cikin shirin ‘Labari Na’. Me za ka ce game da haka?

RIKADAWA: To, alhamdu lillahi. Ka san kullum mutum kai dai yi ka ke yi, kuma jama’a su ke maganar, kai ba ka ma san za a yi maganar ba. To amma dai kusan abin da hakan ke nunawa jama’a su na fahimta, su na kuma amsar abin da ake yi. Saboda haka ba ni da abin da zan ce a kan wannan abu sai dai godiya ga Allah (s.w.t.).

Saboda gaskiyar al’amari, ba hikima ta ba ce. Wallahi ban sa za a karɓa ba, kawai na dai yi iyakacin fahimta ta. Ka ga ai kamar abincin sayarwa ne: kin tuƙa kin kawo kasuwa, sai ki ka ga ga wata mai abincin can, sai ki ka ga an yi wawan naki, tuwo ki ka sayar, ita ma waccan tuwo ne amma an bar ta da kwantai! Kin ga ai ba dabarar ki ba ce, sai dai ki ce alhamdu lillahi, kuma ki ƙara ƙwazo, kuma ki ƙara burge kwastamomin ki, don su ƙara dawowa gobe. Shi ne kawai.

FIM: Ko ka fuskanci wani ƙalubale a game wannan mataki da ka ke takawa na Baba Ɗan Audu?

RIKADAWA: To, shi ƙalubale, ina ganin kamar an wuce matakin ƙalubale. Menene ƙalubale, da duk abin sa aka yi a ce cacaca-cacaca, a yi ta surutu, a ce waye da sauran su. To zuwa yanzu dai wanda ya fahimta ya fahimta, wanda ba shi da niyyar fahimtar ne, ba ka da wani abu kuma da za ka sa shi dole sai ya fahimta, sai dai kawai kai ka ci gaba da yin ƙoƙarin ka iya ainihin basirar ka. 

Ni ina da wani ‘style’ da na ke yi: idan na karɓi rol zan yi, na kan kalli yanayin sa, idan na kula rol ne wanda za a iya surutu a kai, wurin buga shi, sai ka buga shi ta yadda ga shi dai mutum ka ba shi haushi amma kuma dole ya yi dariya. Na kula kuma a cikin mu ‘yan wasa ba kowa ne ya iya haka ba, to amma sai ka yi ƙoƙari ka buga, ga shi saƙon ne dai, ga shi ya karɓa, ga shi wani ma haushin ya ke ji, to amma kuma dole sai ya yi dariya. In mutum ga shi ka ba shi haushi, amma kuma ya yi dariya, ai ka gama da shi, saƙon ka ke so ya ɗauka, ya kuma ɗauka har ya ɗan murmusa.

FIM: A ɓangaren nasarori kuma fa?

RIKADAWA: Alhamdu lillahi. Ka san ita nasara ta akto haka, da ma ba ta wuce irin wannan karɓuwar ba. Ka yi abu a karɓa. Ita babbar nasara ga kowane akto, duk iya iyawar ka, duk iya yadda ka ke jin kai ka kai akto, idan har ka yi ba a karɓa ba, to wallahi tallahi ya tashi a banza. 

Sannan kuma alhamdu lillahi, sai an karɓa sannan in ma wasu abubuwa ne za su shigo su ke shigowa. Yanzu misali kamar ni, abubuwa da na yi sai ya kasance karɓuwar ta sanya masu tallace-tallace su ka ƙara fesowa, duk wanda ya kwaso tallar shi sai ya ce kai ya ke so ka yi, sai ya ce ai Baba Ɗan Audu ya ke so ya yi masa. Ka ga wannan ita ce nasarar a ciki. Shi ya sa na faɗa maka sai an karɓun sannan za ka iya yin wani abu, in ba a karɓa ba ka yi shirme.

FIM: A baya

Rabi’u Rikadawa a bakin aiki

FIM: A baya an fi sanin ka da suna Dila, sai ga Baba Ɗan Audu ya zo ya danne Dila. Yaya ka ke kwatanta wannan sunan da kuma wancan?

RIKADAWA: Allah shi ne zamani ai. Wancan Dilan a wurin harka aka tsinci sunan, kuma ba ni na ce jama’a su kira ni da Dila ba, saboda rol ɗin da ke ‘playing’, su ka ci gaba da kira na Dila. Ka ga kuma yanzu da aka wayi gari su na kiran Ɗan Audun ba ni na ce su kira ba, kuma in su ka ga Ɗan Audun za su kira. Har yanzu akwai masu kiran Dilan in amsa, in an kira Ɗan Audun in amsa. Da ma abin da ya rinƙa ba ni mamaki game da Dilan shi ne na san dai abin nan na daɗe da yin sa, amma sai ka ga yaro wanda shi kan sa, mahaifiyar sa wanda a lokacin da aka yi shirin na Dila, ba ta wuce kamar shi ɗin ba, amma sai ka ga yaro ya gan ka sai ka ji ya ce Dila, sai in ta mamakin shi kuma wa ya faɗa masa, wataƙila iyayen ke ce masa in an nuno ka a fim ko wani suna ka fito da shi su iyayen nasa da sunan su ke kiran ka, saboda haka shi ma daga nan ya samo ya ke kira. Ka ga duk wannan wani abu ne. Yanzu duk abin mutum ya kira, wanda ya fi kwanta masa a rai, wani shi har yanzu shi Dilan ya ke kallo. 

Ai ko kwanan nan an yi taron ƙaddamar da kamfen ɗin takarar mai neman zama gwamnan Jihar Kaduna a APC, Uba Sani, da aka ba da suna na wurin MC za su gabatar da ni, wurin ba da sunan sai aka sa “Rabi’u Rikadawa (Baba Ɗan Audu)”,  wani jami’i shi da ya karɓa ya ga ni ne da sauran su, ya kira Baba Ɗan Audun, amma sai ya ce, “Amma ni da Dila na san ka.” Ka ga fa shi har yanzu ya na nan a Dila ɗin.

FIM: Menene saƙon ka ga masoyan ka?

RIKADAWA: Su masoya har kullum ina faɗi, in Allah ya sa dama irin wannan ta samu, ni fa ba fa ni ba ne, masoyan ne su ka sa aka kawo inda ake a yau. Domin in da a ce abin da ake yi masoyan ba su karɓa, wallahi ba za a kawo inda ake a yau ba. So, duk abin da aka yi ne, aka soko ka a ciki, sai jama’a su yi ta yam-yam-yam, ana so, ana so, to shi ke nan kai kuma ko kai furodusa, ko kai darakta, da ma abin da ka ke so ka yi abin da ake so, tunda ko ana son Rikadawan nan, ni ma bari in sa shi. Wa ya ja ake son Rikadawa? Ka ga masoya ne, da babu su, da ba a ma saka ka ba. Saboda haka su ne su ke da babban rabo a wannan nasara da aka yi. 

FIM: Mun gode ƙwarai da gaske.

RIKADAWA: Ni ma na gode.

fi sanin ka da suna Dila, sai ga Baba Ɗan Audu ya zo ya danne Dila. Yaya ka ke kwatanta wannan sunan da kuma wancan?

“Wasu su kira ni da Dila, wasu da Baba Ɗan Audu”, inji Rabi’u Rikadawa

FIM: Menene saƙon ka ga masoyan ka?

RIKADAWA: Su masoya har kullum ina faɗi, in Allah ya sa dama irin wannan ta samu, ni fa ba fa ni ba ne, masoyan ne su ka sa aka kawo inda ake a yau. Domin in da a ce abin da ake yi masoyan ba su karɓa, wallahi ba za a kawo inda ake a yau ba. So, duk abin da aka yi ne, aka soko ka a ciki, sai jama’a su yi ta yam-yam-yam, ana so, ana so, to shi ke nan kai kuma ko kai furodusa, ko kai darakta, da ma abin da ka ke so ka yi abin da ake so, tunda ko ana son Rikadawan nan, ni ma bari in sa shi. Wa ya ja ake son Rikadawa? Ka ga masoya ne, da babu su, da ba a ma saka ka ba. Saboda haka su ne su ke da babban rabo a wannan nasara da aka yi. 

FIM: Mun gode ƙwarai da gaske.

RIKADAWA: Ni ma na gode.

Loading

Previous Post

Makarantar Jammaje ta naɗa jarumin Kannywood Abale a matsayin jakaden musamman

Next Post

Safyan S. Fawa: Abin da ya sa na shiga harkar waƙa…

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
Safyan Ahmad (S. Fawa)

Safyan S. Fawa: Abin da ya sa na shiga harkar waƙa...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!