A KANNYWOOD, Sayyada Raihan Imam Ahmad, wadda aka fi sani da Raihan Imam (Ƙamshi), ta na cin tudu uku ne: jaruma ce, furodusa, kuma mawaƙiya. Ta na ɗaya daga cikin mata matasa da su ka daɗe ana damawa da su a masana’antar.
Shin wacece Raihan Mujallar Fim ta tattauna da ita, ita kuma ta feɗe mana biri har wutsiya, kamar haka:
FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.
RAIHAN IMAM AHMAD: To, ni dai suna na Raihan Imam Ahmad, wadda aka fi sani da Raihan Ƙamshi. Kuma sunan Ƙamshi daga suna na ne, wato Raihan, fassarar sa da Hausa shi ne Ƙamshi. Sannan kuma ni ma’abociyar son turare ce, ina son turare sosai.
Sannan abin da shafi tarihin rayuwa ta a taƙaice, ni ‘yar Kano ce. Sannan kuma na gabatar da komai nawa na abin da ya shafi karatu da kuma yarinta duk a garin Kano.
FIM: Ta ɓangaren fim kuma yaushe ki ka shiga harkar ?
RAIHAN: E, gaskiyar magana a masana’antar Kannywood zan iya cewa ni ‘ya ce, domin tun ina ƙarama na ke cikin ‘yan fim. Haka na taso har na girma, duk da ma dai ni ba fim ne ya ke ba ni sha’awa ba. Ina son ‘yan fim, amma ni na fi sha’awar waƙa a kan fim.
To, a lokacin can shekarun baya na ɗan yi waƙoƙi na haka, amma ba waɗanda aka sake su a gari ba. Na ɗan yi waƙoƙi saboda sha’awa. Idan na je na buga aba ta zan zo gida na kunna na ji.
To daga baya kuma mutane haka, sai ake ta cewa da ni, “Ki fara yin fim mana,” saboda irin mutane su na ganin ka a cikin ‘yan fim; kawai dai su na ta tunanin ni ba ‘yar fim ba, amma ina da mu’amala da su sosai, don haka kowa sai ya ke ganin na fara fim mana. Ni dai na ke ce musu a’a, don ba zan iya fim ba, na fi sha’awar a bar ni a waƙar da na ke yi, saboda gaskiya ina da jin kunya.
FIM: Duk da yake kin noƙe da farko, ya aka yi ki ka fara fim ɗin?
RAIHAN: To ai ka san an ce yau da gobe. Tun ana yi maka magana, kamar yadda na faɗa maka cewar ni ‘ya ce a cikin ‘yan fim, tun ina ƙarama ta ake son a saka ni a cikin fim, har na zo kuma na kawo kai na saboda wannan maganganun da mutane su ke yi mini na cewar na fara fim. Duk da wani lokacin ya na ba ni sha’awar fa, amma dai na fi sha’war a ce ni waƙa na ke yi. Wannan ta sa yau da kullum aka rinjaye ni na fara da kai na.
FIM: A lokacin da ki ka fara fim, da aktin ki ka fara ko da furodusin?
RAIHAN: Na fito ne a matsayin jaruma, sai daga baya ne na yi sha’awar na zama furodusa. Ta haka sai na ɗauki kuɗi na na bai wa wasu furodusoshin na ce su yi mini fim ɗin, wanda ma ni ba da suna na ba aka yi, don a lokacin ba na so a gane ni na yi.

FIM: Ko za ki iya tuna fim ɗin da ki ka fara fitowa ?
RAIHAN: To fim ɗin da na fara fitowa… wai! Gaskiyar magana ba zan iya tuna fim ɗin da na fara fitowa ba, saboda abin ne da yawa, saboda ni ko finafinan da na yi mantawa na ke yi da sunan su, sai dai zan iya kawo maka kaɗan daga cikin su. Kamar ‘Mugun Miji’, ‘Kai Ne Sanadi’, ‘Ƙawa Ta Kishiya Ta’, ‘So Da Hawaye’, ‘Saura Ƙiris’, da sauran su. Kuma duk yawancin su ina fitowa ne a matsayin jarumar da ta ke jan fim ɗin.
FIM: Kin ce tun ki na ƙarama ki ke cikin harkar. Shin a lokacin da ki ka fara fitowa a cikin fim ko kin samu matsala a gida?
RAIHAN: Ai dole da man in dai mutum ya ce zai yi fim, to ya na da wahala a ce bai samu matsala ba, don haka ni ma na samu ta ɓangaren gida. Da farko lokacin, kamar yadda na faɗa maka a baya, ni ‘ya ce a cikin harkar fim. To akwai yaya ta wacce ita ma da ta fara harkar fim, Amina Imam, wadda duk inda za ta je tare mu ke tafiya da ta, to ita ma sai ya zama ba ta mayar da hankali a kan harkar ba, ta fi mayar da hankali a kan kasuwancin ta. To haka ne tun ina ƙarama ake shiga da ni, sai na tashi a cikin su, na saba da su. Amma duk da haka da na zo gida na ce zan yi fim, sai aka ce mini a’a, ba zan yi ba. Ni kuma ga shi harkar ta shiga rai na a lokacin, a ce za a hana ka akwai damuwa. Har ma aka zaunar da ni da ‘yan’uwa na cewa na haƙura; ni da ake son a ga na yi aure me ya kai ni a ce zan zo na yi harkar fim yanzu? Na ce duk da haka a bar ni, don aure lokaci ne, yin fim ba zai hana ni yin aure ba, rashin yin fim kuma ba zai sa na yi aure ba.
Da haka dai har na kwantar musu da hankali, daga baya su ka karɓi buƙata ta su ka amince. Aka yi mini addu’a da fatan alheri, na je na fara.
FIM: Waɗanne irin nasarori ki ka samu a harkar fim?
RAIHAN: Na samu nasarori waɗanda ba zan ma iya faɗar su ba da baki na ba. Saboda ka san shi fim riga ce ta arziki wadda idan ka na cikin masana’antar, kuma za a kalle ka a matsayin jarumi, to a wurare da dama za ka samu alfarmar da ba kowa ne zai iya samun ta ba. To na samu irin wannan alfarmar sosai. Wasu su na kallon finafinai na ne, wasu sun gan ni na burge su, irin rol ɗin da na ke yi a fim na abin tausayi, ko kuma wani abu. To haka dai na samu nasarori da dama a cikin harkar fim, sai godiya ga Allah.
FIM: A yanzu wane buri ki ke da shi a game da harkar fim?
RAIHAN: Gaskiya ina da buri sosai, saboda kamar yadda na faɗa maka a baya, da ina son a san ni ne, to da zan yi amfani da sunan kamfani na. To a hakan ma ina nan ina shirye-shiryen zama babbar furodusa in-sha Allah, kuma zan shirya finafinai ne da zan saka su a YouTube, sannan kuma zan bada su a gidajen talbijin.
Amma dai alhamdu lillahi, ko a yanzu na cika buri na, tunda na zama jaruma. Sannan kuma ko shi furodusin da na ce zan yi, ko da aure na zan ci gaba da yi da sunan kamfani na.
FIM: Wace irin shawara za ki ba masu harkar fim?
RAIHAN: To ni dai shawarar da zan bayar ba za ta wuce guda ɗaya zuwa biyu ba. Na farko dai, duk wanda zai shigo harkar fim, da ma wanda ya ke cikin ta, ya tsarkake zuciyar sa. Sannan ya saka a ran sa cewa sana’a ya fito ya yi ba wasa ko zubar da mutunci ba. Kawai ya sa a ran sa cewar sana’a ce, kuma ita ya fito ya yi. don haka a kare mutunci, domin shi madara ne, idan ya zube ba a kwashewa. Don haka musamman waɗanda ba su shigo ba, kada su rinƙa ganin wance ta hau mota ko ta riƙe waya, ko ta saka kaya. Ki yi tunanin ke ma daga kin shigo za ki cimma wannan burin, to ba haka ba ne. Ita rayuwa komai a hankali ake bi. Kuma hannayen mu ma ba ɗaya ba ne, wani ya fi wani.
FIM: Madalla, mun gode.
RAIHAN: To, ni ma na gode.

