• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda mutane suke kallon harkar fim daga waje ba haka take ba – Hafsat Ja’afar

'Burin na in yi karatun digiri, a Kannywood kuma in zama darakta'

by MUKHTAR YAKUBU
June 5, 2026
in Taurari
0
Yadda mutane suke kallon harkar fim daga waje ba haka take ba – Hafsat Ja’afar

Hafsat Ja'afar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMAR Kannywood, Hafsat Ja’afar, ba ta wuce shekara ɗaya da rabi a cikin masana’antar ba. Duk da haka, da yake ta shigo da sa’a, zuwa yanzu ta fara haskawa a cikin manyan finafinai. Duk da cewa ba harkar fim ce ta kawo ta Kano ba, da yake ta zo da rabo a cikin masana’antar a yanzu haka ta shiga cikin jerin jarumai mata masu tasowa. Ga tattaunawar ta da mujallar Fim:

 

FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatu.

HAFSAT JA’AFAR: To, farko dai suna na Hafsat Ja’afar wadda ta kasance a masana’antar Kannywood. Amma dai ni haifaffiyar garin Abuja ce. An haife ni a Abuja a cikin shekarar 1997. Na yi makarantar firamare a Abuja, daga nan muka tashi muka koma Sabon Wuse, na yi sakandire a can. Kuma daga nan sai aka yi mini aure. Kuma dai Allah bai sa na haihu ba, muka rabu da miji na. Daga nan sai na dawo Kano.

 

FIM: Ko harkar fim ce ta dawo da ke Kano da zama?

HAFSAT JA’AFAR: Gaskiya ba harkar fim ce ta kawo ni Kano ba. Na zo Kano ne zana jarabawar JAMB inda na sauka a gidan wata ‘yar’uwa ta, kuma daga nan sai Allah ya haɗa ni da wata ƙawa ‘yar fim mai suna Fatima Fulani. A lokacin za su je Arewa24 za a yi hira da su, sai muka tafi tare. To, a nan muka haɗu da su Bilal Jos da wasu mawaƙa. Bayan mun dawo sai muka tafi ofishin su wajen Alhaji Edita. Daga wannan zuwan da muka yi sai kuma na ci gaba da zuwa har muka saba da shi, har ya ce da ni ya kamata na yi harkar fim don za ta yi mini kyau. Gaskiya ni kuma ba ni da sha’awar yin fim saboda ba ita ba ce ta kawo ni Kano.

To, bayan na koma gida suka yi waya da iyaye na, saboda ka san yanayin yadda ake ɗaukar harkar fim, idan ba wanda ya shigo cikin ta ba, daga waje ana yi wa harkar fim wata harka ce ta lalacewa, kuma ba haka ba ne. To, bayan sun yi magana da iyaye na, suka fahimce shi, sai aka bar ni na fara.

Kuma gaskiya ni da waƙa na fara, ba da fim ba. Don ba zan manta ba, mun yi wata waƙa ce mai suna ‘Majanun’. To daga nan sai Yakubu Edita ya saka ni a fim ɗin ‘Baban Yawa’ wanda na fito a matsayin jikar Hajiya, kuma shi ne fim ɗin da na yi na farko.

Sannan na yin fim ɗin ‘Aisha Indo’ inda na fito a matsayin ƙanwar maigidan, sai fim ɗin ‘Biyu Babu’ da na taka rol ɗin ‘yar gida ce amma wadda mahaifin mu ba ya so. Daga nan sai fim ɗin ‘A Cikin Dare’ wanda kusan ni ce ma jarumar fim ɗin. Kuma a yanzu na yi finafinai kamar guda biyar.

Hafsat Ja’afar ta shigo Kannywood da ƙafar dama

FIM: Da yake ba harkar fim ce ta kawo ki Kano ba, kuma kika zama ‘yar fim, ko da kika samu kaki a cikin harkar fim ya Kika ji?

HAFSAT JA’AFAR: To gaskiya ni sai dai na ce alhamdu lillah, saboda duk waɗanda na haɗu da su mutanen kirki ne, kuma babu wanda ya ba ni matsala, domin su ne ma suke nuna mini abin da ya dace na yi kuma suke ba ni goyon baya. Domin ko daraktan da na fara haɗuwa da shi, Tijjani Mai Jama’a, yana nuna mini ƙauna a matsayi na na sabuwar jaruma; bai ba ni matsala ba. Ya bi ni a hankali, har na samar da abin da ake buƙata.

 

FIM: A yanzu da kika shiga harkar fim, ya kuma batun karatu wanda kin zo zana jarabawa ne?

HAFSAT JA’AFAR: Maganar karatu tana nan har ma na samu gurbin karatu na ci gaba da yi a nan Kano, kuma ina da burin na yi digiri in-sha Allahu.

Hafsat tana so ‘yan fim sun tsare mutuncin su

FIM: Ya za ki iya haɗa karatu da harkar fim?

HAFSAT JA’AFAR: Ai shi karatu yana da lokaci, don haka harkar fim ba za ta shafi karatu da nake yi ba. Kuma ka ga ko da ina karatu to ina buƙatar samun sana’ar da zan rinƙa samun kuɗi don gudanar da buƙatu na, don haka zan ci gaba da yin fim kuma ina karatu na.

 

FIM: A yanzu a matsayin ki na ‘yar fim wanne burin kike da shi? 

HAFSAT JA’AFAR: Gaskiya ina da burika da yawa, amma dai duk abin da Allah ya tsara mini shi ne daidai. Amma idan so na ne, ina son na kasance darakta wadda nake ba da umarni, saboda na ɗauki harkar fim a matsayin sana’a sosai shi ya sa nake son na yi daraktin.

Gaskiya ina da burika da yawa, amma dai duk abin da Allah ya tsara mini shi ne daidai. Amma idan so na ne, ina son na kasance darakta wadda nake ba da umarni, saboda na ɗauki harkar fim a matsayin sana’a sosai shi ya sa nake son na yi daraktin.

FIM: A matsayin ki na ‘yar fim, wacce shawara za ki bai wa abokan sana’ar ki?

HAFSAT JA’AFAR: To shawara dai ba ta wuce mu kiyaye sana’ar mu da mutuncin mu ba, domin sai ka mutunta kan ka sannan za a mutunta ka. Don haka ina kira ga ‘yan fim, mu kiyaye mutuncin mu a duk inda muka samu kan mu.

 

FIM: To madalla, mun gode.

HAFSAT JA’AFAR: Ni ma na gode.

Loading

Tags: Hafsat Ja'afarjarumaKannywoodKanotattaunawa
Previous Post

Darakta Ashiru Nagoma ya samu kyautar mashin da kuɗi daga wani masoyi

Next Post

Kannywood ta samu tallafin inshorar lafiya, marasa lafiya shida za su ci gajiya kai-tsaye

Related Posts

Amal Umar:  Abin da ya sa na kai inda nake yanzu
Taurari

Amal Umar: Abin da ya sa na kai inda nake yanzu

June 15, 2026
Shiga ta fim ta sa wanda zan aura ya ce na zama karuwa ba zai aure ni ba – Bilkisu Umar Aliyu
Taurari

Shiga ta fim ta sa wanda zan aura ya ce na zama karuwa ba zai aure ni ba – Bilkisu Umar Aliyu

June 2, 2026
Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan
Taurari

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

August 24, 2025
Jaruma Hauwa Musa Adam
Taurari

Ina son zama mai taimakon al’umma — jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam

August 14, 2025
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Next Post
Kannywood ta samu tallafin inshorar lafiya, marasa lafiya shida za su ci gajiya kai-tsaye

Kannywood ta samu tallafin inshorar lafiya, marasa lafiya shida za su ci gajiya kai-tsaye

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!