• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 10, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shiga ta fim ta sa wanda zan aura ya ce na zama karuwa ba zai aure ni ba – Bilkisu Umar Aliyu

by MUKHTAR YAKUBU
June 2, 2026
in Taurari
0
Shiga ta fim ta sa wanda zan aura ya ce na zama karuwa ba zai aure ni ba – Bilkisu Umar Aliyu

Bilkisu Umar Aliyu: "Ko yanzu na samu mijin zan yi aure"

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Bilkisu Umar Aliyu tana ɗaya daga cikin jarumai mata da suke fitowa a fim, kuma ta taka rawar gani a finafinai masu yawa. A cikin tattaunawar da ta yi da mujallar Fim, ta bayyana yadda ta shigo harkar fim, da kuma ƙalubalen da ta samu.

 

FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatu.

BILKISU UMAR ALIYU: To da farko dai ni suna na Bilkisu Umar Aliyu. Ni haifaffiyar Jihar Adamawa ce, a garin Mubi, kuma an haife ni a 1988. Amma dai na tashi a garin Abuja; tun ina ƙarama mahaifi na ya dawo Abuja da zama, don haka a Abuja na tashi har na yi aure. Allah ya nufe ni da samun ɗa namiji. Kuma daga baya muka rabu da miji na.

FIM: A wanne lokaci kika shiga harkar fim?

BILKISU UMAR ALIYU: To da yake ni zan iya cewa ba kai-tsaye na shiga harkar fim ba, domin na daɗe ina hulɗa da su, domin tun ina da aure ina ba da hanyar gida ga ‘yan fim. A lokacin na tambayi miji na a kan zan rinƙa bayar da hayar gidan ga ‘yan fim da kuma kayan sakawa, kuma ya amince. Haka muka kasance suna yin aiki a gida na, ina kuma ba su hayar kaya. Amma dai a lokacin ban taɓa sha’awar yin fim ba. Don ko da aure na ya mutu ban kawo tunanin zan yi harkar fim ba. Sai daga baya da na ga ina zaune haka babu abin da nake yi, sai na fara shiga harkar, domin lokacin ba sana’a nake yi ba, kuma ka san zawarci akwai wahala idan ba ka sana’a. Don haka sai na shiga harkar saboda na ɗebe wa kai na kewa kuma na huta da zaman kaɗaici.

FIM: Da wanne fim kika fara?

BILKISU UMAR ALIYU: To na fara da fim ɗin ‘Rai Dangin Goro’ na Misbahu M. Ahmad, kuma daga nan ana kira na da kaɗan da kaɗan, kuma alhamdu lillah a yanzu duk da ban fi shekara guda da zuwa ba na yi finafinai da yawa, kamar ‘Musaya Tashin Zance’, ‘Wa Ya San Gobe?’ ‘Kurman Baƙi’, ‘Ƙalubale’. Amma dai fim ɗin da na san ya fito da ni duniya ta san da ni shi ne ‘Manyan Mata’ wanda na fito a ƙanwar Lantana Maman Fadila, sai kuma ‘A’isha Humaira’. Haka shi ma fim ɗin ‘Suwaiba’ na fito sosai a cikin sa. Sai kuma tallar “Curry Dahir sa ƙamshin girki” da muka yi ni da Hadizan Saima, wannan ya jawo mini farin jini kuma ya jawo mini ƙalubale. Don na samu masoya masu yawa ana ta buga mini yawa.

Amma ƙalubalen da na samu a lokacin miji na da muka shirya za mu yi aure, har an gaba komai, lokaci kawai ake jira, ya fasa ya ce shi ba zai aure ni ba. Ya ce ya ga tallan da na yi a talbijin, ya za a ce da girman sa da mutuncin sa da kuɗin sa a ce ya auri karuwa ‘yar fim?

Na ce masa ya zai ce da ni karuwa? Sai ya ce ai ‘yan fim daga ‘yan daudu sai karuwai, saboda haka ba zai auri karuwa ba.

To gaskiya maganar ta yi mini zafi, amma daga baya da na ga ni ba karuwa ba ce sai abin bai dame ni ba. Na tuna aure nufi ne na Allah kuma kowa da irin nasa ra’ayin, domin mutane nawa ne suka auri ‘yan fim kuma suke zaune da su? Saboda haka Allah ya haɗa kowa da rabon sa. Tun daga lokacin muka rabu da shi. Amma dai abin ya yi mini ciwo sosai.

Bilkisu Umar Aliyu

FIM: Da kika shigo harkar fim, ya kika samu kan ki a cikin ‘yan’uwa da iyaye?

BILKISU UMAR ALIYU: To, ban fuskanci matsala sosai ba, saboda iyaye na sun rasu duka, kuma ni ka ga ba yarinya ƙarama ba ce, a yanzu ina da shekara arba’in, to ka ga babu wanda zai zo ya ce me ya sa zan yi. Kuma gaskiya alhamdu lillah, a gidan mu sun san ina da tarbiyya kuma ina da kamun kai, don ko ‘yan’uwa na ma da suka fara gani na a fim sun ce na ci gaba da riƙe mutuncin kai na saboda sun san ina da mutunci. Don haka na ɗauki harkar fim da mutunci domin ita tarbiyya daga gida mutum yake zuwa da ita, idan ka ga mutum ya zubar da mutuncin sa a cikin harkar fim, to da man can ba da mutuncin ya zo ba.

Bilkisu Umar Aliyu

FIM: Tunda wani ya fasa auren ki, ko a yanzu kin haƙura da batun auren?

BILKISU UMAR ALIYU: A’a, ban ajiye maganar aure ba, ko yanzu na samu miji zan yi aure. Amma dai abin da na sa a rai na, aure lokaci ne. Saboda haka don wani ya ce ba zai aure ni ba saboda ina yin fim ai ba kowa ba ne yake da irin wannan tunanin. Ni dai ina yin addu’a Allah ya kawo mini miji nagari wanda za mu zauna lafiya har ƙarshen rayuwa ta.

FIM: Madalla, mun gode.

BILKISU UMAR ALIYU: Ni ma na gode sosai.

Loading

Tags: Bilkisu Umar AliyujarumaKannywood
Previous Post

Masu aibanta ni kan Wasila ku tuba ku daina – Ciroma

Next Post

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halima Adam Yahaya za ta aurar da ‘ya’yan ta biyu ranar 26 ga Yuni

Related Posts

Amal Umar:  Abin da ya sa na kai inda nake yanzu
Taurari

Amal Umar: Abin da ya sa na kai inda nake yanzu

June 15, 2026
Yadda mutane suke kallon harkar fim daga waje ba haka take ba – Hafsat Ja’afar
Taurari

Yadda mutane suke kallon harkar fim daga waje ba haka take ba – Hafsat Ja’afar

June 5, 2026
Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan
Taurari

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

August 24, 2025
Jaruma Hauwa Musa Adam
Taurari

Ina son zama mai taimakon al’umma — jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam

August 14, 2025
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Next Post
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halima Adam Yahaya za ta aurar da ‘ya’yan ta biyu ranar 26 ga Yuni

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halima Adam Yahaya za ta aurar da 'ya'yan ta biyu ranar 26 ga Yuni

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!