• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Amal Umar: Abin da ya sa na kai inda nake yanzu

*Ta ce gwagwarmaya tare da haƙuri ne silar nasarar ta

by MUKHTAR YAKUBU
June 15, 2026
in Taurari
0
Amal Umar:  Abin da ya sa na kai inda nake yanzu

Amal Umar: Buri na in zama fitacciyar jaruma a duniya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Amal Umar Jaruma ce da tauraruwar ta ta daɗe tana haskawa kuma ta kasance tauraruwar Kannywood da Nollywood. Kusan ita ce jarumar da ta samu damar taka tudu biyu tana da ƙarancin shekaru har ta samu damar shiga finafinan Turanci na Hollywood, yayin da a finafinan Hausa na Kannywood ma ana damawa da ita. Ta taka rawar gani a fim ɗin ‘MTV Sugar’, ‘Wings of a Dove,’ da ‘Up North’. Haka kuma a finafinan Kannywood ta yi finafinai masu tarin yawa; kusan ma ba su ƙirguwa. A yanzu fim ɗin da yake haskaka ta shi ne ‘Wata Shida’.

Shin me Amal Umar ta sa a gaba yanzu? Mujallar Fim ta tattauna da ita domin samun wannan amsar, da wasu ma.

 

FIM: Ki gabatar da kan ki ga masu karatu.

AMAL UMAR: To, ni dai suna na Amal Umar, jaruma a Kannywood da Nollywood gaba ɗaya. Kuma na fara harkar fim tun ina ƙarama, don na fara ina da shekara 17 kuma ga shi a yanzu shekaru na na haihuwa ina da shekara 27. Kuma alhamdu lillah na fara daga jaruma, a yanzu na kai matsayin mai shirya finafinai nawa na kai na. To duk da dai akwai matakai da yawa da za ka taka har zuwa wannan matsayin, amma alhamdu lillah zuwa yanzu.

FIM: Tunda kin ambaci matakai, ko ya kika keto rayuwa a cikin matakan da kika bi zuwa wannan matakin da kike kai a yanzu?

AMAL UMAR: To, an sha gwagwarmaya sosai ba ta wasa ba. Misali, wasu suna ganin za ka iya, wasu suna ganin ba za ka iya ba. Kuma akwai abubuwa da yawa da za a saka ka, amma sai a rinƙa ganin ba za ka iya ba. To akwai irin wannan abubuwan da yawa na harkar fim da kowa ya sani. Don haka gwagwarmaya dole duk wani jarumi yana da shi. To duk irin waɗannan suna cikin gwagwarmaya. Kuma dai haƙuri an sha shi, kuma har mun kai inda muke so mu kai.

FIM: A cikin irin gwagwarmayar da kika sha, wanne abu ne da ba za ki manta shi ba?

AMAL UMAR: Gaskiya abin da ba zan manta ba abu ne wanda ya dame ni a rayuwa ta, wanda har yanzu idan na runa ina jin zafin ta, amma kuma ba zan iya faɗar sa a duniya ba, kawai na bar shi a zuciya ta; duk da dai abin ya wuce, amma dai ba zan manta ba, domin shi ne abin da ya fi ɗaga mini hankali a harkar fim, sai dai komai ya wuce a yanzu.

Amal Umar

FIM: Kin yi finafinai masu yawa. To za ki iya tuna fim ɗin da ya fito da ke?

AMAL UMAR: To ni gaskiya zan iya cewa fim ɗin da ya fito da ni duniya ta san da ni ba fim ɗin Kannywood ba ne, saboda lokacin da na shigo Kannywood da shekara ɗaya sai na samu aka ɗauke ni a wani aiki, maigida na Yakubu Muhammad ya yi mini hanya na tafi Legas na yi wani fim International Movies. To bayan fitowar fim ɗin sai suna na ya ɗaga kuma a fim ɗin na fara samun manyan kuɗi, kuma a fim ɗin fuska ta ta fito aka san ni. Saboda a lokacin ma akwai mutanen da ba sa tunanin ni ‘yar Arewa ce. To sai daga baya aka fara gane ni ‘yar Kannywood ce.

FIM: To a ɓangaren finafinan Hausa kuma, da wanne kika yi suna?

AMAL UMAR: A ɓangaren finafinan Hausa akwai finafinai da yawa. Amma dai akwai fim ɗin da na yi farkon shigowa ta, ‘Rabu Da Maza’. Shi wannan fim ɗin shi ne ya fito da ni aka fara sani na a matsayin jarumar Kannywood. Sai dai kuma duk fim ɗin da na yi ana gani na a matsayin na shahara. Amma dai a yanzu ba a can baya ba. A wannan lokacin, babu fim ɗin da ya sa na ƙara samun karɓuwa da shahara kamar fim ɗin ‘Wata Shida’, saboda duk inda na je ana kallo na a matsayin jarumar fim ɗin ‘Wata Shida’, sai ka ji ana cewa, “Ina Lailu? Amira ta Lailu!” Maza da mata haka ake kira na.

FIM: Harkar fim ta kai ki ga samun matsayi na rayuwa da dama. Ko ya za ki kwatanta irin tasirin da harkar fim ta yi miki?

AMAL UMAR: To ka ga dai ni babu abin da zan ce da harkar fim. Domin daga farawa ta zuwa yanzu harkar ta sa na samu kuɗi nawa na kai na, kuma ina taimaka wa ‘yan’uwa na da ma wasu na waje. Harkar fim ta sa na mallaki gida nawa na kai na. Harkar fim ta sa na mallaki abubuwa da yawa. To babu abin da zan ce sai godiya ga Allah.

Amal Umar da Umar M. Shareef ne jaruman sabon fim ɗin ta mai suna ‘Majnoon’

FIM: Kowane ɗan’adam ya kan sa buri a kan abu da ya sa a gaba. Shin menene burin da kike so ki cimma a harkar fim?

AMAL UMAR: Gaskiya a yanzu burin da nake da shi ya cika. Saboda abu uku na so a fim. Farko na so na zama jaruma. Na dawo na so na zama furodusa. Na zo kuma daga baya ina son na zama mai ba da umurni.

To yanzu a cikin abubuwan nan guda uku da na faɗa maka, ka ga na yi kamfani nawa na kai na. Ka ga na yi aktin na zama jaruma ba ma a Arewa kaɗai ba har da Kudu. To yanzu kuma na ƙarshe da ya rage mini shi ne na zama mai ba da umurni. Shi ma kuma a yanzu ana kan hanya.

FIM: Tunda kin kai ga cikar burin ki a yanzu ina kika sa gaba?

AMAL UMAR: To inda na sa gaba a yanzu shi ne na ga finafinan da nake yi ya zama international film, yadda zan zama fitacciyar jaruma a duniya, yadda idan hakan ta kasance, to buri na ya gama cika.

Amal Umar a Madina

FIM: Ana kallon ki a matsayin wata jaruma mai jan aji, wadda ba ta cika magana da mutane ba. Yanayin ki ne haka, ko dai jan aji ne?

AMAL UMAR: Gaskiya ni idan aka ce da ni jaruma mai jan aji, a nan ba a yi mini adalci ba, saboda ni ina ƙoƙarin na ga na yi faran-faran da mutane. Sai dai kawai a cikin wani abu da bai shafe ni ba ne ba zan shiga ba. Amma dai gaskiya ina ƙoƙarin na ga na yi mu’amala da mutane yadda ya kamata.

FIM: Me ya fi burge ki a cikin harkar fim?

AMAL UMAR: Babu abin da ya fi burge ni kamar na ga mun zo wajen aiki muna mu’amala cikin jin daɗin da kwanciyar hankali, har ma ba ma so mu rabu saboda jin daɗi na zama tare. Don haka ni na ɗauki ‘yan fim a matsayin ‘yan’uwa na. Shi ya sa nake jin daɗin zaman mu tare, idan aka zo za a rabu sai na ji babu daɗi. Don haka wannan abin ya fi burge ni.

FIM: To, madalla, mun gode.

AMAL UMAR: Ni ma na gode sosai.

Shigar Amal Umar a bikin African Magic Viewers Choice Awards (AMCA) na bana ya ja hankalin jama’a sosai

Loading

Tags: Amal Umarjarumatattaunawa
Previous Post

Maryam, ‘yar jarumin Kannywood, Ali Dawayya, ta cika shekaru 8 da haihuwa

Next Post

Ba mu janye dakatarwar Adam Garba da Amina Uba Hassan ba – Hukumar Tace Finafinai

Related Posts

Yadda mutane suke kallon harkar fim daga waje ba haka take ba – Hafsat Ja’afar
Taurari

Yadda mutane suke kallon harkar fim daga waje ba haka take ba – Hafsat Ja’afar

June 5, 2026
Shiga ta fim ta sa wanda zan aura ya ce na zama karuwa ba zai aure ni ba – Bilkisu Umar Aliyu
Taurari

Shiga ta fim ta sa wanda zan aura ya ce na zama karuwa ba zai aure ni ba – Bilkisu Umar Aliyu

June 2, 2026
Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan
Taurari

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

August 24, 2025
Jaruma Hauwa Musa Adam
Taurari

Ina son zama mai taimakon al’umma — jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam

August 14, 2025
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Next Post
Ba mu janye dakatarwar Adam Garba da Amina Uba Hassan ba – Hukumar Tace Finafinai

Ba mu janye dakatarwar Adam Garba da Amina Uba Hassan ba – Hukumar Tace Finafinai

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!