• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba mu janye dakatarwar Adam Garba da Amina Uba Hassan ba – Hukumar Tace Finafinai

by MUKHTAR YAKUBU
June 16, 2026
in Labarai
0
Ba mu janye dakatarwar Adam Garba da Amina Uba Hassan ba – Hukumar Tace Finafinai

Adam Garba da Amina Uba Hassan cikin bidiyon da ya jawo musu dakatarwa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano ta ƙaryata ji-ta- ji-tar cewa wai ta janye dakatarwar da ta ƙaƙaba wa wasu fitattun jaruman Kannywood biyu, Adam Garba da Amina Uba Hassan.

A cikin ‘yan kwanakin nan, wasu rahotanni sun bazu a soshiyal midiya suna iƙirarin cewa an gudanar da wata ganawa tsakanin hukumar da jaruman, inda aka cimma matsayar janye dakatarwar da aka yi musu.

Idan kun tuna, tun a ranar 16 ga Mayu ne hukumar ta ba da sanarwar dakatar da jaruman biyu daga duk wata harkar fim a jihar har tsawon shekara guda, bisa rawar da suka taka a wani bidiyo da hukumar ta bayyana a matsayin wanda ya saɓa wa tarbiyya da kyawawan ɗabi’u.

Hukumar ta bayyana cewa matakin ya kasance wani ɓangare na ƙoƙarin ta na tabbatar da tsaftace harkar shirya finafinai da kuma tabbatar da bin dokoki da ƙa’idojin da ta shimfiɗa domin kare martabar al’umma da al’adun jihar.

Dakatarwar tana nufin an haramta wa Adam da Amina shiga ko gudanar da duk wani aiki da ya shafi shirya finafinai a Jihar Kano na tsawon shekara guda.

Haka kuma, dokar da ta kafa hukumar ta ba ta ikon ɗaukar irin wannan mataki kan duk wanda ya karya ƙa’idojin ta, tare da tanadin hukunci mai tsauri ga masu bijirewa.

Binciken da mujallar Fim ta gudanar ya nuna cewa rahotannin da ake yaɗawa na cewa an janye dakatarwar ba su da tushe, kuma hukumar ba ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da hakan ba.

Da yake magana da mujallar Fim, Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya musanta rahotannin, yana mai cewa: “Ba mu san da irin wannan labari ba. Idan akwai wani muhimmin bayani daga hukumar, za a ji shi ne daga bakin Jami’in Yaɗa Labaran Hukumar, domin shi ne ke da ikon sanar da duk wani matsayi ko sanarwa a hukumance.”

Alhaji Abba El-Mustapha

A cewar sa, har zuwa yanzu, dakatarwar da aka yi wa jaruman biyu tana nan daram, kuma babu wani sauyi da aka samu a kan matakin da hukumar ta ɗauka.

Loading

Tags: Abba El-MustaphaAdam GarbaAmina Uba HassandakatarwaHukumar Tace Finafimai ta Jihar Kano
Previous Post

Amal Umar: Abin da ya sa na kai inda nake yanzu

Next Post

Sa’adatu, babbar ‘yar darakta a Kannywood Ismael Khalil Ja’en ta rasu

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Sa’adatu, babbar ‘yar darakta a Kannywood Ismael Khalil Ja’en ta rasu

Sa'adatu, babbar 'yar darakta a Kannywood Ismael Khalil Ja'en ta rasu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!