MARYAM Ali Ibrahim Dawayya, ‘yar fitaccen jarumi kuma furodusa a masana’antar Kannywood, Ali Ibrahim wanda aka fi sani da Ali Dawayya, ta cika shekaru takwas da haihuwa.
Domin murnar wannan rana ta musamman, Ali Dawayya ya shirya liyafar cin abinci ga ‘yar sa a gidan abincin sa da ke unguwar Gidan Ɗan Asabe, kan titin Zoo Road a birnin Kano.
An gudanar da taron cikin yanayi na farin ciki, inda ‘yan’uwa, abokai da sauran masu fatan alheri suka hallara domin taya Maryam murna. Mahalarta taron sun yi mata addu’o’in samun lafiya, tsawon rai da albarkar rayuwa.


Da yake bayyana farin cikin sa, Ali Dawayya ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa ni’imar aure da zuri’a da ya yi masa, yana mai bayyana cewa cikar shekaru takwas da Maryam ta yi babban abin farin ciki ne ga iyalan sa.
Ya ce: “Alhamdu lillah, ina matuƙar godiya ga Allah da ya azurta ni da iyali da kuma ‘ya’ya. Ina roƙon Allah ya ƙara mini albarka a cikin su, ya ba ni ikon sauke nauyin da ya ɗora mini na kulawa da tarbiyyar su yadda ya kamata.
“Haka kuma ina godiya ga masoya na, abokai na da duk waɗanda suka taya ni murnar wannan rana ta musamman. Allah ya saka wa kowa da alheri.”

Taron ya gudana cikin walwala da annashuwa, yayin da baƙi suka ci abinci tare da taya Maryam murna.

![]()







