• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 24, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mu ’yan fim za mu tallata Tinubu da APC daga sama har ƙasa – Lawan Ahmad

by MUKHTAR YAKUBU
June 13, 2026
in Labarai
0
Mu ’yan fim za mu tallata Tinubu da APC daga sama har ƙasa – Lawan Ahmad

Alhaji Lawan Ahmad

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR ’yan fim masu goyon bayan jam’iyyar APC, wadda aka fi sani da Triple R Kannywood for Renewed Hope, ta bayyana aniyar ta ta amfani da dukkan ƙarfin da take da shi wajen tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar APC a dukkan matakai gabanin babban zaɓen 2027 da Ke tafe.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Lawan Ahmad, shi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da mujallar Fim a Kano.

Ya ce manufar ƙungiyar ita ce haɗa kan masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood domin tallafa wa manufofin jam’iyyar tare da neman cigaban masana’antar.

Da yake bayani kan asalin ƙungiyar, Lawan Ahmad ya ce ba sabuwar ƙungiya ba ce, sai dai yanzu ne ta fara bayyana kan ta tare da fara gudanar da ayyukan ta a fili.

Ya ce: “Wannan ƙungiya ta daɗe da kafuwa, ba yanzu aka fara ta ba. Ƙungiya ce da aka kafa domin shiga harkokin siyasa ta hanyar da za ta amfani al’umma.

“Mun lura da cewa sau da yawa abubuwan da gwamnati ke yi ba sa isa kunnen talakawa yadda ya kamata, haka kuma ƙorafe-ƙorafen talakawa ba sa kaiwa ga shugabanni. Saboda haka muka ga ya dace mu zama wata gada tsakanin gwamnati da al’umma.”

Jarumin kuma furodusa ya ƙara da cewa ƙungiyar ta buɗe ƙofofin ta ga dukkan masu sana’o’in da suka shafi harkar fim, ciki har da jarumai, furodusoshi, daraktoci, marubuta da sauran ma’aikatan masana’antar.

“Mu aikin mu shi ne isar da saƙo. Saboda haka za mu yi amfani da wannan dama da Allah ya ba mu wajen wayar da kan jama’a da kuma isar da saƙonnin da suka dace,” in ji shi.

Dangane da goyon bayan da suke bai wa APC, Lawan Ahmad ya ce babu wata ɓoyayyiyar manufa a cikin sa.

“Gaskiya ne, wannan ƙungiya ta APC ce, kuma za mu yi wa Shugaba Tinubu da dukkan ’yan takarar APC daga sama har ƙasa aiki da tallata manufofin su. Wannan shi ne matsayar da muka ɗauka kuma muka yi imani da ita,” inji shi.

Ya ce yawancin jaruman Kannywood suna da ɗimbin masoya da ke sauraron ra’ayoyin su, wanda hakan zai taimaka wajen yaɗa manufofin jam’iyyar.

Ya ce: “A matsayi na na jarumi, ina da masoya da dama waɗanda ba ’yan fim ba ne. Wasu daga cikin su za su iya goyon bayan APC saboda amincewar da suke da ita a kai na. Haka ma sauran jarumai suke.

“Bugu da ƙari, muna da damar kai ƙorafe-ƙorafen jama’a ga gwamnati, sannan mu karɓo saƙonnin gwamnati mu isar da su ga al’umma.”

Lawan ya ce ƙungiyar ta tanadi wasu tsare-tsare da shirye-shirye da za su amfani masana’antar Kannywood da al’umma baki ɗaya, ko da yake bai bayyana cikakkun bayanan su ba a wannan lokaci.

Ya ce: “Akwai abubuwa da dama da muka tsara waɗanda lokaci zai bayyana su. Muna son gina ƙungiya mai ɗorewa wadda ko bayan ba mu, za a ci gaba da tafiya da ita. Haka kuma muna son mu zama wata hanya ta kai buƙatu da ƙalubalen da masana’antar Kannywood take fuskanta ga gwamnati domin a nemo musu mafita.

“Mun yi tsari mai kyau wajen zaɓen waɗanda za su kasance cikin wannan tafiya. Duk wanda za mu haɗa aiki da shi sai mun tabbatar da nagartar sa da cancantar sa. Saboda haka, a wannan tafiya tamu babu gurbi ga waɗanda ba su dace ba.”

Loading

Tags: APCKannywoodLawan AhmadShugaba Bola Ahmed Tinubusiyasazaɓen 2027
Previous Post

Za a gudanar da bikin baje-kolin finafinai na Kaduna na Kasa da Kasa karo na tara

Next Post

Maryam, ‘yar jarumin Kannywood, Ali Dawayya, ta cika shekaru 8 da haihuwa

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Maryam, ‘yar jarumin Kannywood, Ali Dawayya, ta cika shekaru 8 da haihuwa

Maryam, ‘yar jarumin Kannywood, Ali Dawayya, ta cika shekaru 8 da haihuwa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!