• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 24, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za a gudanar da bikin baje-kolin finafinai na Kaduna na Kasa da Kasa karo na tara

by ABBA MUHAMMAD
June 11, 2026
in Labarai
0
Za a gudanar da bikin baje-kolin finafinai na Kaduna na Kasa da Kasa karo na tara

Israel Kashim Audu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Masu shirya Bikin Baje Kolin Finafinai na Kasa da Kasa na Kaduna (Kaduna International Film Festival – KADIFF), ƙarƙashin jagorancin shugaban bikin, Mista Israel Kashim Audu, sun bayyana cewa sun kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin gudanar da bikin karo na tara, wanda ake sa ran zai tattaro manyan masu ruwa da tsaki a harkar finafinai daga sassa daban-daban na duniya.

Bikin na bana zai gudana ne daga ranar 25 zuwa 29 ga watan Agustan 2026 a Jihar Kaduna, ƙarƙashin taken “Cultural Renaissance” (Farfaɗowar Al’adu), da nufin bunƙasa al’adun gargajiya, ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’umma da kuma nuna muhimmancin finafinai a matsayin wata kafa ta isar da saƙonni masu tasiri.

Masu shirya taron sun bayyana cewa an tanadi shirye-shirye masu armashi da suka haɗa da nuna finafinai daga ƙasashe daban-daban, bitocin horaswa ga masu sana’ar finafinai, tarurrukan musayar ilimi da ƙwarewa, da kuma bikin karrama fitattun jarumai da masu ruwa da tsaki ta hanyar ba su lambobin yabo.

A cewar masu shirya bikin, KADIFF na ci gaba da zama wata muhimmiyar gada da ke haɗa masu shirya finafinai, jarumai, masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin haɓaka masana’antar nishaɗi tare da ƙarfafa musayar al’adu tsakanin al’ummomi.

Sun ƙara da cewa bikin na bana zai ci gaba da ɗaukar tutar yaɗa saƙonnin zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasa al’adu, tare da haskaka irin ci gaban da masana’antar finafinai ke samu a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa an kammala dukkan shirye-shiryen taron cikin tsari, yayin da masu shirya bikin ke ci gaba da dakon isowar baƙi da mahalarta daga sassa daban-daban na duniya domin halartar wannan gagarumin taron finafinai na kasa da kasa da ake sa ran zai kasance ɗaya daga cikin manyan al’amuran nishaɗi na shekarar 2026.

Loading

Previous Post

An ƙaddamar da gagarumin shirin sake fasalin ƙungiyar AFMAN

Next Post

Mu ’yan fim za mu tallata Tinubu da APC daga sama har ƙasa – Lawan Ahmad

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Mu ’yan fim za mu tallata Tinubu da APC daga sama har ƙasa – Lawan Ahmad

Mu ’yan fim za mu tallata Tinubu da APC daga sama har ƙasa – Lawan Ahmad

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!