Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon shiri na inshorar lafiya ga masu harkar finafinai ta hanyar haɗin gwiwar Hukumar Tace Finafinai da Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kano (KCHMA), inda aka fara da ɗaukar nauyin kula da lafiyar wasu marasa lafiya shida daga cikin ’yan masana’antar.
An cimma wannan matsaya ne a wani taron haɗin gwiwa da aka gudanar tsakanin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kano (KCHMA) tare da shugabannin ƙungiyoyin masu harkar finafinai a ofishin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano a jiya Juma’a, 5 ga Yuni, 2026.
Da take jawabi a taron, Shugabar KCHMA, Dakta Rahila Aliyu Mukhtar, ta tabbatar da aniyar hukumar ta na yin aiki tare da Hukumar Tace Finafinai domin samar da tsarin da zai kula da lafiyar jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar finafinai ta jihar.
Ta bayyana cewa shirin zai taimaka wajen rage nauyin kuɗaɗen jinya da masu harkar finafinai suke kashewa, musamman waɗanda ke fama da cututtuka masu tsanani da ke buƙatar kulawa ta musamman.

Shi ma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya ce wannan haɗin gwiwa yana daga cikin matakan da hukumar take ɗauka domin inganta walwala da cigaban masu harkar finafinai a jihar.
A nasu ɓangaren, shugabannin ƙungiyoyin Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) da Arewa Films Makers Association of Nigeria (AFMAN), Shehu Hassan Kano da Salisu Muhammad Officer, sun bayyana jindaɗin su tare da nuna cikakken goyon bayan su ga wannan shiri.
Sun yaba wa El-Mustapha bisa ƙoƙarin da ya yi na samar da wannan dama, musamman a lokacin da wasu daga cikin ’yan fim suke fama da matsalolin lafiya.

A wani ƙarin bayani da ya yi a safiyar yau Asabar, Salisu Officer, ya bayyana cewa: “Bisa ƙoƙari da jajircewar ɗan’uwan mu, Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, tare da Shugabar KCHMA, Hajiya Rahila Aliyu Mukhtar, an samar wa masana’antar Kannywood wata gidauniyar jinƙai a fannin lafiya mai suna Kannywood Abba Care.
“Bayan zaman da aka yi tsakanin Hukumar Tace Finafinai, masu ruwa da tsaki na Kannywood, hukumomin biyu da kuma wasu masu fama da rashin lafiya guda shida a cikin masana’antar, an amince da ɗaukar nauyin kula da lafiyar su gaba ɗaya ba tare da sun biya ko kwabo ba.
“Haka kuma, an kafa wani kwamiti da zai tsara hanyoyin da duk ’ya’yan masana’antar Kannywood za su ci gajiyar wannan tsari cikin sauƙi, gaskiya da aminci.”

Officer ya yi kira ga dukkan ’yan Kannywood da su haɗa kai wajen yaba wa El-Mustapha bisa wannan gagarumar gudunmawa.
Ya ce: “Mu tattaru mu yaba wa Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano bisa samar da wannan gagarumar gudunmawa wadda tarihi ba zai taɓa mantawa da ita ba.”

![]()







