WATA ƙungiyar matasa ta ƙasa mai suna Sir Ahmadu Bello Council of Nigeria ta karrama fitacciyar jarumar Kannywood, Hajiya Amal Umar, da lambar yabo domin ƙara mata ƙwarin gwiwa a kan ayyukan ta na kawo cigaba da kuma ƙarfafa wa matasa gwiwa domin su dage wajen cigaban rayuwar su.
A wata ziyara da shugabannin ƙungiyar suka kai wa jarumar a ofishin ta da ke Titin Sheikh Muhammad Nasiru Kabara a cikin garin Kano a yau Asabar, ƙungiyar ta miƙa kambun karramawar ga jarumar.
Tun da farko da yake bayani a game da zuwan su, Daraktan Gudanarwa na ƙungiyar, Malam Muhammad Abdurrashid, ya ce, “Ita wannan ƙungiya tamu tana ƙoƙarin zaburar da matasa wajen su tashi su nuna ƙwazo don maganin zaman kashe wando, da kuma wayar da kan su a game da illar shaye-shaye da kuma daba da ta’addanci.
“Haka nan yaran da suke jami’a mukan nuna musu illar miyagun ƙwayoyi, da kuma ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen su tashi tsaye wajen yin abin da ya kawo su na karatu.
“Haka nan wannan ƙungiya tana bayar da lambar girmamawa ga matasa da suke nuna ƙwazo waɗanda suka zamo madubi a cikin al’umma.
“Don haka ba mu cika bai wa ‘yan siyasa ba, sai matasa da suke yin ayyukan da matasa suke koyi da su.”
Ya ƙara da cewa: “A wannan gaɓar ne ita Amal Umar ta shigo ciki kasancewar matashiya wadda ta fara fim tun tana ƙarama har ta kawo matsayin budurwa. Kuma a tsawon lokacin da ta yi a wannan harkar ta bayar da gudunmawa da ta zama abin koyi ga matasa masu tasowa wajen nuna ƙwazo da kuma tsayuwa a kan manufa.
“Don haka ne muka taso muka zo har ofishin ta domin ba ta wannan lambar girmamawa. Kuma alhamdu lillah mun samu ƙwarin gwiwa, tunda ta nuna mana cewa ƙofar ta a buɗe take a kan duk wani abu da ya shafi matasa a zo a same ta za ta bayar da gudunmawar ta, za ta kasance tare da mu a ko da yaushe.”
Ita ma a nata jawabin bayan ta karɓi kambun karramawar, Hajiya Amal Umar ta bayyana cewa: “Gaskiya na ji daɗin wannan lambar girmamawa da aka ba ni, domin sun nuna cewar sun zauna sun duba sannan suka zaɓo ni a cikin matasan da suke bayar da gudunmawar su ga cigaban matasa, musamman yara masu tasowa da suke yin wannan harkar, da kuma yanayin yadda suke gani na a soshiyal midiya, shi ya sa suka ga ya dace su biyo ni har inda nake don su kawo mini wannan lambar girmamawa.
“Don haka na ji daɗi sosai. Domin kuwa a ce irin wannan babbar ƙungiya su zauna su nazarci ayyukan da nake yi su gano ni ido ce a cikin a cikin matasa masu tasowa. Suka duba ayyuka na da kuma yanayin yadda nake rayuwa ta, har abin ya jawo ra’ayin su.”
Ta ƙara da cewa: “Ni na ɗauka idan ina yin ayyuka na ni kaɗai nake yi wa kai na kuma ni kaɗai nake ganin abin da nake yi. To amma kawo wannan lambar girmamawa ya nuna ba ni kaɗai nake ganin abin ba, mutane ma suna gani. Don haka na ji daɗi sosai marar misaltuwa.
“Sannan ka ga lambobin yabo da na saba karɓa wanda ake tara mutane ne a bayyana wa duniya. Amma shi wannan tattaki aka yi har ofis aka ba ni. Don haka wannan ya sha bamban da sauran wanda na saba karɓa.
“Don haka ina kira ga mata, musamman waɗanda suke cikin masana’antar Kannywood, su cire tsoro a kan duk wani abu da suka sa a gaba. A duk lokacin da kika saka abu a gaba , to ki sa a ran ki za ki iya kuma ki fara yin sa kai-tsaye, domin sai kin jarraba za ki gano za ki iya.
“Don haka ina ƙara ƙarfafa musu gwiwa da su sa a ran su duk abin da suka sa a gaba to kuwa za su iya.”
![]()







