• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Auren Aisha Tsamiya bai mutu ba, inji ‘yan Kannywood

by DAGA ABBA MUHAMMAD
November 20, 2023
in Labarai
0
A'isha Aliyu Muhammad (Tsamiya)

A'isha Aliyu Muhammad (Tsamiya)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

LABARIN da mujallar Fim ta buga jiya cewar auren tsohuwar jarumar Kannywood Aisha Aliyu Tsamiya ya mutu ba gaskiya ba ne, inji ‘yan masana’antar finafinan irin su Ali Nuhu da Abdul Amart Mohammed.

Haƙiƙicewar da su ka yi tare da zurfafa bincike da mujallar ta yi ya sa mujallar ta goge labarin daga gidan yanar ta da kuma soshiyal midiya.

Jim kaɗan bayan ɓullar labarin, makusantan tsohuwar jarumar, wadda ta yi aure a Fabrairu 2023, su ka kira wakilan mu a lokuta daban-daban, su na cewa wannan labarin fa kuskure ne domin kuwa A’isha na zaune daram daƙam a gidan mijin ta.

Waɗanda su ka kira mujallar sun haɗa da Ali Nuhu, Abdul Amart, da Samira Saje.

Dukkan su sun nuna cewa su na da kusanci tare da kyakkyawar alaƙa da Aisha da mijin ta mai suna Alhaji Buba Abubakar, kuma ba su daɗe da yin waya da su ba.

Samira, wadda ke da kamfanin sayar da tufafi na Samsaj Parlour da ke Abuja, ta ce ita a nata ɓangaren A’isha Tsamiya ɗin ce ma ta tura mata da labarin da aka buga tare da bayyana damuwa. Ita kuma ta yi mata alƙawarin za ta tuntuɓi masu mujallar.

Aisha Tsamiya a shagon ta

Wasu daga cikin ‘yan fim ma da su ka kira labarin da “ƙarya” kai-tsaye sun haɗa da Halima Atete, Saratu Abubakar, Masa’uda ‘Yar’agadas da Sulaiman Costume.

Mujallar Fim ta bi dukkan ƙa’idojin aikin jarida wajen tattara bayanai kafin ta rubuta labarin, inda ta samu tabbacin sakin auren daga wasu mutum huɗu, ciki har da ‘yan Kannywood masu sahihin kusanci da A’isha.

Haka kuma wani wakilin mu ya yi ƙoƙarin tuntuɓar ta ta hanyar kiran waya da tura mata saƙon tes, amma babu amsa domin, kamar yadda mu ka ji a jiya, ashe ta tafi Umrah ita da wani ƙanen ta.

Mujallar Fim ta na bada haƙuri ga ma’auratan saboda rashin jin daɗin da labarin ya jawo masu, tare da tabbacin hakan ba zai ƙara faruwa ba.

Mu na yi masu addu’ar Allah ya sa mutu-ka-raba.

An kafa mujallar Fim a farkon shekarar 1999, inda ta zama babbar kafar yaɗa ingantattun labarai da bayanai a kan ‘yan fim, kuma ta taimaka sosai wajen fito da da yawan su a idon duniya.

Ta shafe shekaru ashirin ana buga ta a kan takarda kafin ta bi zamani wajen ci gaba da fitowa a intanet.

A tsawon wannan lokaci ba a san ta da yin ƙage ko yaɗa labarin ƙanzon kurege ba domin masu buga ta ƙwararru ne a fagen aikin jarida a Nijeriya, masu bin diddigi ƙwarai kafin su buga labari irin wannan.

Loading

Previous Post

Mijin furodusa a Kannywood, Fatima Lamaj, ya rasu

Next Post

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)

Fim riga ce ta arziki - Raihan Imam Ƙamshi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!