Godiyar Rabbi ce fari,
Kan mu zafi ruwa ɗari,
Wanda ke kaɓakin khairi
Ke ije dukkanin haɗari,
Yana ta ba mu yana ƙari.
‘Yan’uwa sannu barkan mu,
Da ganin yau da rayin mu,
Wasu kan yau fa sun bar mu,
A abokai da dangin mu,
Mu kuwa ga shi ya bar mu.
Kan mu ƙalubalen himma,
Bauta Allah mu yo azama,
Kan baɗi ta yiwu ba mu,
Mun wuce sai mu yi harama,
Duniya ba gida na zama.
Rayuwa duk tsanantar ta,
Sai Musulmi ya jure ta,
Lokaci ne da zai gota,
Rabbana za ya sauya ta,
Haka nan take Sunnar ta.
Ga ni yau ma da saƙo na,
Na yi sauyi na hoto na,
Har zuwa baɗi zai zauna,
In na san jinkiri gu na,
Ko ya zamto na bankwana.
Ba ni wasa da ƙaunar ku,
Daga ni ko ga ni daga ku,
‘Yan’uwa na na ɗauke ku,
Khairi fata na ke gun ku,
Zuciya ta ba ta ƙin ku.
Dukka khairi muna roƙo,
Rabbana mun riƙe ƙoƙo,
Izuwa gun ka mun sheƙo,
Ba mu alheri mai maiƙo,
Shiriyar Ɗaha mui ta riƙo.
Allah sauya dukan ƙunci,
Da zukatan mu yau ke ci,
Rabbi yaye dukan kauci,
Na talauci da yai ɓaci,
A ƙasa har ya yo kwanci.
Sahibi naku ne Nasir,
Ahmad Garba ko sha’ir,
Bai yi nuna fage na shi’ir,
Bai yi kaiwa zuwa mahir,
Kwaikwayo ne yake zahir.
Rabbi ƙaro salatin ka,
Gun Rasulu abin son ka,
Wanda ya ida saƙon ka,
Kai kaɗai mu yi bautar ka,
‘Ali Sahabbai masoyan ka.