• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An ɗaura auren Fatima ‘yar Ado Gidan Dabino

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 3, 2023
in Ranar Murna
2
Fatima Ado Ahmad Gidan Dabino a wajen taron addu'a na musamman kafin a kai ta gidan miji

Fatima Ado Ahmad Gidan Dabino a wajen taron addu'a na musamman kafin a kai ta gidan miji

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A RANAR Asabar, 2 ga Satumba, 2023 aka ɗaura auren ɗiyar fitaccen marubuci kuma jarumi, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, wato Fatima Ado Ahmad Gidan Dabino, da angon ta, Bello Umar Kawaji.

An ɗaura auren da misalin ƙarfe 11 na safe a Masallacin Juma’a na Al-Furƙan da ke unguwar Nassarawa GRA, Kano, a kan sadaki N100,000, kuma an biya lakadan kuma wakilin waliyyin amarya, Alaramma Muttaƙa Sani ya karɓa.

Uban amarya (na 2 daga hagu) tare da jama’a a wajen ɗaurin auren

Wakilin mujallar Fim ya ruwaito cewa taron ɗaurin auren ya samu halartar manyan mutane kama daga sarakuna da marubuta da kuma ‘yan siyasa.

Waɗanda su ka halarta sun haɗa da Farfesa Abdalla Uba Adamu, Farfesa Yusuf Adamu, Dakta Tahir A. Ahmad Sarkin Dawaki Maituta, Kabiru Assada, Aminu Ladan Abubakar (Ala Waƙa), Zaharaddin Ibrahim Kallah, Mai Unguwar Mandawari Alhaji Ibrahim Muhammad Madawari, da Khadil Imam.

Ado Gidan Dabino tare da Farfesa Yusuf Adamu (a damar sa) da Aminu Alan Waƙa (a hagun sa) da sauran jama’a

Tun kafin ranar ɗaurin auren an shirya wa amarya Fatima taron saukar karatun Alƙur’ani da addu’o’i, sannan bayan an ɗaura da yammacin ranar Asabar ɗin an yi taron addu’a na musamman a gidan Ado Ahmad Gidan Dabino domin Allah ya kawo zaman lafiya a tsakanin ango da amarya kuma ya tsare su daga dukkan fitintinu na zaman aure.

Allah ya tabbatar da hakan, amin.

Farfesa Abdalla a tsakiyar mahalartan ɗaurin auren
Malam Ado Ahmad Gidan Dabino tare da Kabir Assada (mai farar babbar riga) da sauran mahalarta ɗaurin auren Fatima
Amarya da ‘yan’uwa da ƙawaye a wajen taron addu’ar musamman
Amarya da sauran mata su na karatun Alƙur’ani
Ado Gidan Dabino da iyalin sa a lokacin addu’ar musamman da aka yi a gidan sa
Ado Ahmad Gidan Dabino tare da amarya Fatima bayan addu’ar musamman ta auren ta

Loading

Previous Post

‘Yan Kannywood sun kai wa Ganduje da Minista Hannatu Musawa ziyara

Next Post

Jarumi Aminu Asid na so a saka ‘yan Kannywood cikin shirin gwamnati na tallafa wa jama’a

Related Posts

Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida
Ranar Murna

Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida

June 29, 2025
Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani
Ranar Murna

Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani

June 19, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu
Ranar Murna

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu

May 2, 2025
Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu
Ranar Murna

Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

April 25, 2025
Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 
Ranar Murna

Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 

April 20, 2025
Next Post
Aminu Ilu Dambazau (Asid)

Jarumi Aminu Asid na so a saka 'yan Kannywood cikin shirin gwamnati na tallafa wa jama'a

Comments 2

  1. Hadiza Muhammed says:
    2 years ago

    Masha Allah 🤗 Allah ya bada zaman lafiya, Allah yasa albarka a wan nan auren

  2. Shuaibu Shehu says:
    2 years ago

    Comment: Ya Allah ka yi wa auren albarka amin. IN DA SO DA KAUNA…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!