HANA miji kan ki ko guje ma shimfiɗar sa tamkar ya bar ki da mummunar yunwa ne ko ya miki horo da yunwa ne. Ba shi kan ki tamkar alfarma ki ke masa kuwa tamkar ya bar ki cikin tsananin yunwa ba inda za ki samu abincin face abin da ya ba ki ko ya kawo maki ne, amma kuma da ya tashi kawo maki abincin sai ya shigo maki da ‘yar leda ƙarama a hannu ɗauke da ɗanyen abincin da sai kin yi hidimar dafawa, ga tsananin yunwa sannan ba lallai abin da ya kawo ɗin ya ishe ki ba, sai kuma ya wurga maki shi a fuskar ki ya ce, “Ga shi in ki na so ki ci ɗanyen ko ki dafa damuwar ki”, ya bi da cewa, “Ga shi ba ki da zuciya balle ki haƙura da cin.”
💔Shin za ki iya kwatanta irin baƙin cikin da za ki ji a zuciyar ki?
💔 Shin za ki iya cin abincin nan duba da mummunar yunwar da ki ke ji?
💔 Shin in ki na cin abincin nan za ki ji daɗin sa?
💔 Shin in da ki na da wata mafita za ki ci wannan abincin?
💔 Shin za ki ji haushin mijin ko za ki so shi tunda dai ya ba ki abincin?
💔 Shin ya sauke haƙƙin sa ko bai sauke ba tunda dai ya kawo abinci?
💔 Shin ki na iya kwatanta cutarwar da aka yi ma zuciyar ki da gangar jikin ki?
Duk abin da za ki kwatanta ko ki hararo na wulaƙanci, tozarci a zuciyar ki in miji ya yi maki haka ina tabbata maki gwargwado ko fiye da haka namiji ya ke ji in ki ka ƙaurace ma shimfiɗar sa ko in ya buƙace ki ki yi ta masa wulaƙanci da jan rai da maganganu tamkar alfarma ki ka yi masa ba haƙƙin sa za ki ba shi ba, ko in kin amince yayin abin da ki ka ji a ran ki haka ko fiye da haka zai ji lokacin da ya ke saduwa da ke.
Wannan zai sa ki ƙara gane daga cikin dalilin da ya sa Annabi ﷺ ya ce:
” إزا رعا الرجل امرأته إلى فراشه فأبت فبات غضبان عايها لعنتها الملاءِكة حتى تصبحَ “.
“Idan mutum ya kira matar sa zuwa ga shimfiɗar sa ammata ƙi, ya kwana ya na fushi da ita, mala’iku za su yi ta la’antar ta har sai ta wayi gari.” .
” إزا دعا الرجل زوجته لحاجته فلتأْته وإن كانتْ على التَّنُّور “.
“Idan mutum ya kira matar sa domin buƙatar sa, to (hanzarta) ta je masa ko da ta na gindin murhu ne na tuya.”
Duk abin da ke tsakanin ki da miji ki kiyaye ƙaurace ma buƙatar sa ko ba shi a wulaƙance, domin ya kan cutar da zuciya da jikin miji wadda hakan zai haifar da ƙiyayyar mace a zuciyar miji a zuciyar sa.
Zaman lafiyar ki shi ne yadda ba kya son mijin ki ya bar ki da yunwa ke ma kar ki bar shi da yunwa.
* Hajiya Fatima Chikaire mashawarciya ce kan zaman aure da zamantakewar al’umma