ZAN faɗa maku wani fanni na rayuwa ta da miji na da ya danganci gaisuwa da nuna kulawa, ba don komai ba sai don ina son mu fahimci yanayin yadda kowa ya ɗauke ta ko ya ke yin ta.
Da farko dai, shekarun da ke tsakani na da miji na dai shekara 11 ya ba ni, shekarun auren mu kuwa kusan 21 mu ke nema yanzu. Amma duk wayewar gari sai na gaishe shi, in a waya ne ko in ya dawo gida. Na kan masa nau’i uku na gaisuwa wanda ko wanne da yanayi, lokaci da dalilin da na ke yin sa.
1. Na kan masa gaisuwa ta girmamawa wadda har ƙasa na ke sa gwiwoyi na kafin in gaishe shi, ko in masa gaisuwar ‘yar duƙawa na rage tsawo( in ya dawo daga ofis).
2. Na kan masa gaisuwa irin ta ƙauna wadda ta shafi gaisuwa ta kalamai da ke haɗe da runguma da sumba.
3. Na kan masa gaisuwa irin ta aboki, mu sha hannu mu ware.
Ko a waya na kira shi ko ya kira sai na tabbata na masa gaisuwa da sanin yanayi da lafiyar sa.
Duk da kasancewar sa shugaba na, amma ya kan gaishe ni wadda ya kan bayyana cikin nau’i biyu: 1. Gaisuwa ta ƙauna da tausayi, da 2. Gaisuwa irin ta abokai.
Duk ran da ya riga ni tashi zan ji ya na, “Good morning”, “Good morning” ko “Good morning beautiful. Tashi kar in yi latti.” Zai haɗa da runguma da sumba. Wannan al’ada ce da mu ka jima da saba wa kan mu.
In kuwa dawowa gida ya yi daga ofis mu kan tarbi juna da runguma da sumba (sai in ɗaya ko dukan mu da alwala tare da mu) haɗi da faɗin, “Good to see you”, “Good to see you too”. Mu na idar da wannan sallar da mu ka riƙe ma wannan alwala za mu yi gaisuwa ta soyayya da mu ka saba wa juna.
In kuwa ya yi baƙi su ka jima su na falo bai ji ɗuriya ta ba (kasancewar ya san na kan so zama da hira da shi), zai bar abokan sa ya shigo inda na ke, ya na zuwa zai ce, “Na ji ki shiru ne, na ce barin zo in gaishe ki.” Na kan ce masa, “Godiya na ke da wannan gaisuwa.” Hakan da ya ke ya kan sa na ji daɗi don ya kan tuna ni duk da yake ya na cikin nishaɗi da abokan sa.
Farkon azumi mu kan raba ɗaki don lokacin barci da tashin mu ya kan bambanta sosai, saboda haka na kan riga shi barci da tashi don shi ya na da abokan shan ruwa kuma su kan tsaya don hira kafin su tafi, ni kuwa ina gama Asham na ke barci.
Amma ba ya taɓa wucewa ba tare da ya shiga ya duba ni ba. Ko na yi bacci ko ban yi ba zai shigo ya duba ni. In ya tashi tahajjud duk da na kan riga shi tashi, amma kafin ya soma zai zo ya duba ni don tabbatar da na tashi. In kuwa na ji shi shiru na kan je in duba shi don na san ya makara wajen tashi.
In ban da lafiya ban cika kwana inda ya ke ba don kar zafin jiki na da yawan motsi ya hana shi barci, amma duk dare zai shigo ya duba ni sau biyu don tabbatar da lafiya da yanayin da na ke ciki, wani lokaci ba na ma sanin ya shigo sai dai ya ce, “Na dawo na ji kin samu barci lokaci kaza.”
Wani lokaci kuwa in na gaida shi ya kan ce min ba zai amsa ba sai na tsuguna kafin ya amsa. Nan take ba musu na kan tsuguna har ƙasa in sauya yanayin kalamai na wadda na kan dawo da shi na sarauta, isa da ƙasaita, ya na amsawa tamkar sarki a gidan sa. In na gama ya kan ce, “To ko ke fa!” Na kan bi shi da, “Ina mai biyayya Sardauna, ɗan Alkali, ɗan magajin Malam, jikan Malam, surukin farin Boka”. Yawancin lokuta a wannan gaɓar mu kan tintsire da dariya. Sai ya ce, “To zo nan,” ya jawo ni jikin sa.
Cikin gaisuwar safiya da na ke masa wadda yawancin lokuta in ya dawo daga sallar asuba ne, na kan haɗa da, “Ya Maman ka da Baban ka?” Ya kan ce min, “Su na lafiya, yanzu na gaishe su,” wanda ya ke nufin ya masu addu’a.
Bai taɓa dawowa gida ban gaishe shi na tambayi wunin hidimar ofis, wani mitin da na san za su yi, ko wani ƙalubale da na san su ke ciki ba. Wani lokaci in ya yi kukan wuya a kan wani aiki da su ka yi ko ƙalubale da ya ke da shi da wani, na kan ce masa, “Su bar wahalar min da kai wallah don kar su tsufar min da kai haka kawai”, ko in ce, “In fa wane bai bar damun ka ba zan kai shi ƙara. Haka kawai ina dalili da zai riƙa sa maka ɓacin rai ba dalili?”
Na kan yi hakan don ba shi damar samun natsuwa da nuna damuwa ta ga al’amuran rayuwar sa.
Hakan da mu ke yi ya kan ƙara mana natsuwa, kusanci, nishaɗi da zaman lafiya a tsakanin mu, kuma ya kan tabbatar min da irin tausayi da kulawar sa gare ni.
Saboda haka, a wajen mu, mu mun ɗauki gaisuwa wata ƙofa ce da mu ke nuna kulawa da ƙauna a tsakanin mu, ba ƙofar da in ɗaya bai yi ba an raina shi ko ba a damu da shi ba.
II
Rayuwar aure na da miji na ba daga haka ta soma ba.
Kasancewar jiya na ga wasu su na faɗin kamar a littafin hikaya ko ya mu ke tunkarar matsalar mu in mun samu matsala.
Na farko dai rayuwar auren mu kamar ko wane aure ne, mu na da matsaloli da ƙalubalen da tun shekarar farko ta aure har zuwa yau mu na fuskantar su, mu na da jarrabawar da mu ke fama da ita har yanzu, mu na da bambancin da ke tsakanin mu, mu na da gazawar mu, mu na da ɗabi’u maras kyau da dukkan mu mu ke haƙuri da kawaici a kan juna.
Sai dai alhamdu lillah da agaji da taimakon Allah mun kiyaye kuma mun ƙi mu bari waɗannan abubuwa su yi tasiri a cikin zamantakewar auren mu da zai zama sanadin rashin zaman lafiyar mu. Mun kasance mu kan kalli alheran juna fiye da kallon sharrin juna, mu na haƙuri da juna gwargwadon hali. In mu ka samu matsala ba mu cika barin ta ta ɗau lokaci ba mu shirya ba; hasali ma duk fushi da tutsun ba ya wuce ‘yan awanni zuwa kwana ɗaya zuwa biyu, tsanani uku, nan za mu yi ‘welcome back’ mu ci gaba daga inda mu ka tsaya.
Tun da mu ka yi aure kowa ya san matsayin sa da nauyin da ya rataya a wuyan sa a cikin auren. Ni na ajiye kai na inda Allah ya ajiye ni, shi ya ɗauki kan sa inda Allah ya ɗaukaka shi. Na ɗauki miji na gata na kuma abin rufin asiri na duk da lokacin da mu ka yi aure shekarun sa biyu da soma aikin gwamnati wanda albashin sa a lokacin N18,000, amma ban taɓa raina abin da ya min ko ya ke yi a gidan sa ba, ko in sa hankali a kan abin da wasu ke samu da ba na samu a gidan sa ba, bai taɓa yin wata ɗawainiya a gidan sa na raina ko na ce ta yi min kaɗan ko ba irin abin na ke so ba. Hasali ma na kan ba shi damar zaɓi a kan abin da ya ga zai iya yi. Shi kuma bai taɓa gazawa wajen nuna himma don ganin ya rufa mana asiri daidai abin da Allah ya hore masa a lokacin ba. Duk abin da ya yi na kan amsa cikin farin ciki, yabo da godiya wadda har gobe ina yi.
Duk da yake a lokacin ina da damar da zan iya nemo kuɗi ko tallafi wajen iyaye na amma wallahil azim ban taɓa yi masa kukan irin rayuwar da mu ke ciki ba, kuma ban taɓa zuwa gidan kowa nemo taimako ba, don ba na son abin da zai zubar masa da ƙima ko a ga gazawar sa ko in sa ya ji ya gaza wajen lura da ni a matsayin sa na shugaba kuma jagoran rayuwar mu.
Shi kuwa bai taɓa kashe zuciya ya zama ci-ma-zaune ko ya zama ɗan maula ko ya na da shi ya ƙi yi wa iyalan sa ba, sam, ya san haƙƙin da ya rataya a wuyan sa na iyalan sa da ya na da shi ba bai da shi zai yi ƙoƙari ya ga ya tsira da mutuncin sa a idon iyalan sa. (Wannan ɗabi’ar ta sa na ke ganin sa a matsayin jarumi kuma cikakken namiji, don ya na aiki da hankali, ilimi da ƙarfin da Allah ya yi masa wajen lura da haƙƙin iyalan sa).
Tun farkon auren mu na kan ba shi dukkan girmamawa da ta cancance shi. Na kan masa biyayyar da har gobe ya na iya sa ni ko ya hana ni in hanu, ba musu ko son jin dalili. Ina tuna wani lokaci duk ran da na fita na kan bi gidan mu ba tare da na tambaye shi ba, ni a tunani na ba komai, ashe abin ba ya masa daɗi. Ranar ya ce, “Na hana ki sake zuwa gidan ku sai ran da na ce ko ki ka tambaya.” Haka ba musu ko faɗa na ce, “To.” Ban sake zuwa gidan mu ko tambaya zuwa ba har sai ran da ya yi ra’ayin sa shi da kan sa ya ba ni damar zuwa. Wani lokaci har shi ke ce min, “Kin kwana biyu ba ki leƙa gidan ku ba,” ko ya ce, “An ce Chief (Baba) ya zo. Ki je ki gaishe shi.”
Na kan nemi izini da amincewar sa a kusan dukkan abin da zan yi. Hatta koyar da darussan abinci ba na yi ba tare da neman amincewar sa ba. Ko kwanaki na nema ya ba ni izini, wani abu ya taso, ya ce in haƙura, har na mayar wa wasu kuɗin da su ka biya, amma da ikon Allah na samu abin da ko shekara zan yi ina wannan koyarwar ba zan samu abin da na samu ba. Ko wannan rubutun sai da na nemi izinin sa ya ce sai ya karanta kafin in wallafa.
Ya kan nuna iko da isar sa a kan wasu abubuwan amma ba sa damu na don na san miji na ne kuma ya isa ya nuna wannan isa da ikon a kai na kuma a zauna lafiya. Ba na bijire masa in na ga ya na wannan abin ko in ji haushi don na san namiji ne. Akwai lokutan da ji da nuna wannan isar ne ya ke tabbatar masu da sun isa kuma su ne jagororin tafiyar (ɗabi’a ta kusan dukkan maza ce).
Ba na shiga harkar kuɗin sa, nawa ya samu, ya zan karɓi rabo na ko in masa cuwa-cuwa, ko in damfare shi, ko wa ya ke wa ɗawainiya ko nawa ya ke kashe wa kan sa ko abin da ya ke saya da kuɗin sa. Matuƙar ya na sauke haƙƙin da ya rataya a kan sa ban da matsala a kai, kuɗin sa ne, shi ya nemo abin sa, don haka ya na da ikon yin abin da ya ga dama da su.
Akwai abubuwan da na san ya na haƙuri da ni a kan su kamar yadda ya san akwai abubuwan da na ke haƙuri a kan sa.
Mu kan bai wa juna lokaci. In mu na da mtsala mu kan zauna mu tattauna mu fahimci juna, kowa ya kan amshi laifin sa a inda ya yi kuskure, ya kuma ba da hakuri.
Duk abin da ya ke so ina matuƙar kiyaye yin sa don na san shi ne zaman lafiya da kowane namiji. Bai son ganin ɓacin rai na don ya san gidan baya daɗi in ina tutsu (na iya bori da tutsu har da salo irin na kowace mace!).
Mu kan kyautata zato ga junan mu, mu kan ƙarfafi juna a inda mu ka fahimci ɗaya na buƙatar ƙarfafawa (emotional, mental and financial support).
A kullum mu kan nemi tsari, taimako da agajin Allah a cikin zamantakewar mu don mun san Shi ne kaɗai Ya ke da ikon wanzar da zaman lafiya da jin daɗi a rayuwar bayin Sa.
Rayuwar auren mu irin ta kowa ce da ke tattare da irin nata ƙalubale, jarrabawa da duk wani faɗi-tashi da ba a raba bawa da ita a rayuwa. Bambancin kawai kowa da irin yadda ya fahimci rayuwar aure, ya ɗauke ta kuma ya ke son ya yi ta ko ya ke yin ta.
Mu dai mun ɗauke ta in ba mu gyara ba babu mai gyara mana, in ba mu zauna lafiya ba babu mai zaunar da mu lafiya, in ba mu fahimci juna ba babu mai fahimtar da mu junan mu, in ba mu yi haƙuri da juna ba babu mai yi mana, shi ya sa a kullum mu ke neman agaji da taimakon Allah wajen ganin mun samu fahimta da zaman lafiya a tsakanin mu. Domin mun san ba iyawa, jimawa, ko ƙoƙarin mu ba ne ya samar mana da wannan ni’imar, kyauta da rahama ce daga Allah.
Daga ƙarshe, ina mai godiya ga dukkan addu’o’in da fatan alherin da ku ka yi mana da miji na. Allah ya ba ku fiye da abin da ku ka roƙa mana.
* Hajiya Fatima Chikaire ta wallafa wannan sharhin ne a Facebook a daidai lokacin da ake muhawarar dacewa ko rashin dacewar mace ta gai da mijin ta idan gari ya waye
![]()






