• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙasashen Larabawa da na Musulmai sun haɗa kai wajen yin tir da hare-haren Isra’ila a Zirin Gaza

by DAGA WAKILIN MU
November 15, 2023
in Nijeriya
0
Shugaba Tinubu a wajen taron na OIC

Shugaba Tinubu a wajen taron na OIC

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TARON Haɗin Gwiwar Ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashen Musulmai ya yi tir tare da nuna rashin amincewa da hare-haren da sojojin Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a Zirin Gaza.

Taron, wanda aka gudanar a ranar Asabar, 11 ga Nuwamba, ya bayyana cewa abin da sojojin Isra’ila su ka yi laifin tsallake ƙa’idoji da sharuɗɗan yaƙi ne, kuma dabbanci ne kan Falasɗinawa fararen hula.

Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na ministan, Malam Rabi’u Ibrahim, ya fitar.

Idris, wanda ya na cikin tawagar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a wurin taron, ya ƙara da cewa kuma an yi kira da a gaggauta gudanar da gagarumin taron duniya, inda za a bijiro da hanyoyin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin Falasɗinu.

Sanarwar bayan taron da wanda shugabannin ƙasashen Ƙungiyar OIC da na Majalisar Ƙasashen Larabawa su ka halarta, an yi kira da a gaggauta tsagaita dukkan hare-haren da sojojin Isra’ila ke kaiwa a Gaza. 

Kuma sun fito ƙarara sun ce farmakin da Isra’ila ke kaiwa kan Gaza ci gaba ne da irin mamayar da ta yi wa Falasɗinawa a 1967 a yankin da West Bank, Masallacin Ƙudus da kuma Arewacin Birnin Ƙudus.

Sannan kuma taron ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya da ta fito da ƙwaƙƙwarar matsaya a ƙarƙashin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya wadda za ta tilasta daina duk wani nau’i da salo na gallazawa da Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa.

Haka nan kuma wannan taro ya nemi Isra’ila ta kawo ƙarshen mamayar da ta ke yi a yankin, domin ya karya ƙa’ida da iyakokin da dokokin ƙasa da ƙasa su ka shar’anta.

Sun ce musamman farmakin ya saɓa wa Ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya mai lamba AES-101.25 na ranar 26 ga Oktoba, 2013.

A wurin taron, shugabannin sun yi kakkausan kira ga Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya cewa “ta gaggauta yin Allah-wadai da dabbacin da sojojin Isra’ila ke kan yi na ruguza asibitoci a Zirin Gaza. Kuma ta yi tir da hana a shigar wa Falasɗinawa da magunguna, abinci, fetur da katse wutar lantarkin da mahukuntan Isra’ila ɗin su ka yi a Zirin Gaza.”

Shugaba Tinubu tare da sauran shugabanni a taron

An zartas da cewa matuƙar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙi yin tir da dabbancin da sojojin Isra’ila ke aikatawa a Zirin Gaza, to tamkar ta halasta mummunan kisan da ake wa fararen hula ne da su ka ƙunshi ƙananan yara, dattawa, mata da kuma ruguza Gaza da ake kan yi.

Sun ce ya zama wajibi Isra’ila ta ɗage takunkumin datse Zirin Gaza da ta yi tsawon shekaru masu yawa.

Sannan kuma taron ya yi tir dangane da yadda wasu ƙasashe su ka riƙa taimaka wa Isra’ila da muggan makaman da ta ke amfani da su ta na kisan gilla kan Falasɗinawa, tare da ruguza masu gidaje, asibitoci, makarantu, masallatai, coci-coci da sauran wuraren more rayuwa.

Shugaba Tinubu tare da wasu daga cikin mahalarta taron

Loading

Previous Post

Ban taɓa ganin irin wannan karramawar da aka yi min ba, inji Rikadawa

Next Post

INEC ta nesanta kan ta daga zargin baddala ƙuri’un zaɓen gwamnan Kogi a Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe, IRev

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

INEC ta nesanta kan ta daga zargin baddala ƙuri'un zaɓen gwamnan Kogi a Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe, IRev

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!