• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 2, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tsakanin Sa’in Katsina da Shata

by KABIR UMAR PRO
December 25, 2023
in Tsokaci
0
Tsakanin Sa’in Katsina da Shata

Sa'in Katsina Alh. Amadu Na-Funtua da Alh. Mamman Shata

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A RANAR Litinin, 25/12/2023, Alhaji Amadu Na-Funtua (Sa’in Katsina), ya cika shekara hamsin cif da naɗin shi da marigayi Sarkin Katsina, Sir Usman Nagogo Mai Turawa, ya yi masa.

Makaɗa, maroƙa, mawaƙa babu shakka sun shaida wannan naɗin amma tabbas babu kamar Na Ali Hukumar Waƙa (Shata).

Baba Sa’i da ‘Dillalin Duniya Ƙanen Sasana’ Allah kaɗai ya san tsakanin su domin taren su ta amana ce tun tali-tali.

A wata hira da na yi da Baba Sa’i a cikin shekarar 2019, ya shaida mani cewa lamarin su Allah ne kawai, ba wani mahaluƙi. Domin a zaman da ya yi a Saliyo, Shata ya so ya je har can amma Allah ne bai yi ba. Shatan ya ambaci wani baiti makamancin haka a waƙar sa ta ‘Yawon Duniya Mafarki Ne Alhaji Shata’.

Baba Sa’in ya shaida mani ya na daga cikin mutane ukku da ke sa Shata ya yi abu ko da ba ya so. Sauran biyun su ne Umaru Yaro Funtua da Yusuf Musa Yar’Adua (‘Ɗan London Na Mairo’).

Tsanani da tsabagen jituwa, yarda da amana da ke tsakanin su ta sa Shata ya na da ɗaki a Nasara Club (mallakar Sa’i) wanda ko da ya rasu sai da aka je aka kwashe kayan. Sannan Nasara Club na ɗaya daga cikin manyan wuraren da Shata ke wasa a Katsina idan ya zo.

Fostar cikar Baba Sa’i shekara 50 da samun sarauta

‘Duna na Bilkin Sambo’ ya yi wa Baba Sa’i waƙoƙi da su ka haɗa da: ‘Sasau Na Korau Ɗan Abdu’, ‘Amadu Sa’in Katsinar Mu’, ‘Na Funtuwa Amadu Na Abba’. Ya kuma ambace shi a waƙoƙi da dama; ga kaɗan daga cikin su: ‘Allah Raya Jihar Katsina’, ‘Zakari Magajin Zakari’ (‘Ya’u Magajin Ya’u’), ‘Salele Alhaji Ɗankwari’, ‘Haji Armaya’u Na ‘Yar Salo’, da ‘Jama’iyyar SDO’.

Mai karatu, a daidai nan akwai waƙoƙi da dama, ka zamo cikin masu ƙaro wasu domin lissafin mu ya daidaita.

Sai ya taka muhimmiyar rawa wajen sa Shata ya yi wa mutane da dama waƙoƙi; wasu a gidan shi, wasu a filin ƙofar gidan marigayi Alhaji Sani Mai Sanda, wasu a Nasara Club, wasu a gidan wasan marigayi Yusuf Shema Ɗandoka.

Sai dai duk da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin su bai hana Dodo ya nuna wa Baba Sa’i shi Na Yalwa “mai ban sha’awa ne kuma mai ban haushi ne”. Wata rana an yi sanarwar wasan Shata, aka taru a Nasara Club. Dodon sai ya gudu ya tafi garin Muduru ya ɓoye wa Baba Sa’i da sauran masu son ganin wasan shi. Amma duk da haka sai da Sa’i ya je ya taho da shi.

Tarihin Shata ba ya cika babu Baba Sa’i, haka zalika na Baba Sa’i ba ya cika ba Shata.

Da wannan ɗan taƙaitaccen bayani mu ke ƙara yi ma Baba Sa’i fatan alheri a daidai lokacin da ya cika shekaru 50 da samun wannan sarautar.

Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana, Baba.

* Kabir Umar Saulawa (PRO) ma’aikaci ne a Katsina. Tarho: 07034610481

Loading

Tags: Amadu Na-Funtua Sa'in KatsinaMamman ShatasarautaSarkin Katsina Usman Nagogoshekara 50
Previous Post

Zakaran gwajin dafi: Za a ɗora fim ɗin ‘Mati A Zazzau’ na Rahama Sadau a Netflix ranar 30 ga Disamba

Next Post

Jarumi a Kannywood Abdallah Amdaz zai zama mai igiya biyu Asabar mai zuwa

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Jarumi a Kannywood Abdallah Amdaz zai zama mai igiya biyu Asabar mai zuwa

Jarumi a Kannywood Abdallah Amdaz zai zama mai igiya biyu Asabar mai zuwa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!