• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zakaran gwajin dafi: Za a ɗora fim ɗin ‘Mati A Zazzau’ na Rahama Sadau a Netflix ranar 30 ga Disamba

Wannan ba ƙaramin abu ba ne, inji Rahama

by DAGA ALI KANO
December 24, 2023
in Labarai
0
Zakaran gwajin dafi: Za a ɗora fim ɗin ‘Mati A Zazzau’ na Rahama Sadau a Netflix ranar 30 ga Disamba

Rahama Sadau na bada sanarwar ɗora 'Mati A Zazzau' a Netflix

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jaruma kuma furodusa a Kannywood, Rahama Sadau, za ta kafa tarihi a Kannywood inda fim ɗin ta, ‘Mati A Zazzau’, zai kasance shirin Hausa na farko da ya hau manhajar Netflix.

Rahama da kan ta ta bada bayanin cewa za a ɗora ‘Mati a Zazzau’ kan manhajar a ranar 30 ga Disamba, 2023.

Fim ɗin na haɗin gwiwar kamfanin Asmasan Pictures da Sadau Pictures, ya fara fitowa ne tun a ranar 7 ga Fabrairu, 2020 lokacin da aka nuna shi a gidan sinima a Kano. Daga lokacin ba a ƙara jin ɗuriyar shi ba sai yanzu.

A sanarwar da ta bayar a soshiyal midiya, ta ce: “Fim ne mai ƙayatarwa, fim ne mai nishaɗantarwa, sannan kuma shi ne fim na farko da za a fara sakawa a kan manhajar Netflix. Wannan ba ƙaramin abu ba ne. Kada ku bari a ba ku labari.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa kafin dai wannan lokacin, ‘yan Kannywood da dama sun sha son su ga yadda kamfanin Netflix zai karɓi fim ɗin su domin haskawa a dandalin finafinai mafi girma inda za su samu ƙazamar riba tare da sanayya.

Netflix kan sayi fim ɗin Nijeriya a kan zunzurutun kuɗi daga $10,000 har zuwa $90,000.

Mashirya fim a kudancin Nijeriya sun daɗe da samun karɓar finafinan su a Netflix, domin yanzu haka akwai finafinan Nollywood kusan 30 a manhajar.

Fostar ‘Mati A Zazzau’

‘Mati A Zazzau’ zai kasance zakaran gwajin dafi a wannan fage, kuma zai buɗe wa sauran ‘yan Kannywood ƙofar da za su bi a karɓi finafinan su a Netflix.

A da, sun riƙa cin kasuwar finafinan da ake nunawa ta hanyar intanet ne ta manhajar Northflix da kuma kallo.ng.

Ban da Netflix, manhaja ta gaba ita ce Amazon Prime Video. A nan, ba a san wanda ƙarya ƙwarin ba.

Rahama Sadau a cikin ‘Mati A Zazzau’

‘Mati A Zazzau’ ci-gaban shirin ‘Mati Da Lado’ inda bayan Mati ya tsere daga ƙauyen su sai ya isa Zazzau ya shiga faɗi-tashin yadda zai ci gadon dukiyar da uban sa attajiri ya mutu ya bari a hannun abokin sa.

Yakubu M. Kumo ne ya rubuta labarin, Yaseen Auwal ya yi daraktin, yayin da jaruman shirin su ka haɗa da Sadiq Sani Sadiq (Mati), Rahama Sadau (Rama), Hadiza Blell (Madina), Umar Gombe (Garba), Jamila Nagudu (Asabe), Rabi’u Rikadawa (Barau), Aminu Sharif Ahlan (Ilyasu), Tahir I. Tahir (Lado), da Adam A. Zango (Yarima).

Loading

Tags: Mati A ZazzauNetflixRahama Sadau
Previous Post

Ina hamdalar samun ‘ya’ya masu ilimi – Sadiya Garba Yakasai

Next Post

Tsakanin Sa’in Katsina da Shata

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Tsakanin Sa’in Katsina da Shata

Tsakanin Sa'in Katsina da Shata

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!