FITACCIYAR marubuciya, Hajiya Sadiya Garba Yakasai, ta bayyana godiya ga Allah da ya ba ta ‘ya’ya masu ilimi tare da albarka.
Ta faɗi haka ne a tattaunawar da ta yi da mujallar Fim a lokacin bikin saukar karatun Alƙur’ani wanda ‘yar ta Zainab Sani Garba Panisau ta yi.
A ranar Lahadi da ta gabata, 17 ga Disamba, 2023 aka yi walimar wadda ‘yan’uwa da abokan arziki su ka taru domin taya murna.

A lokacin da ta ke yi wa mujallar Fim ƙarin bayani a game da taron, Hajiya Sadiya ta ce, “Ina alfahari da kuma godiya ga Allah da arzikin ‘ya’ya da ya yi mini maza da mata, wanda a cikin su a yanzu mu ka taru domin taya ɗaya daga cikin su murnar saukar da ta yi ta na ‘yar shekaru 17 da haihuwa ta sauke Ƙur’ani, wannan abin alfahari ne a gare ni da Allah nuna mini wannan rana.
“Allah ina ƙara godiya a gare ka da ‘ya’yan da ka ba ni masu albarka, masu ilimi.”

Marubuciyar ta miƙa godiya ga dukkan waɗanda su ka halarci walimar domin taya ta murna duk yake dai ba wata gayyata ta yi ba, amma da su ka samu labari su ka je domin taya ta murna.

