A YAU Juma’a aka ɗaura auren mawaƙi a Kannywood, Ahmad Usman Adamu, Ahmad Yariman Tiga.
An ɗaura auren Ahmad da abar ƙaunar sa Maryam Bashir (Fulanin Yarima) da misalin ƙarfe 1:30 na rana, bayan sallar Juma’a, a masallacin Juma’a mai suna Muhammad Nasir da ke Kabala Road, Sabon Garin Tudun Wada, Kaduna.
An ɗaura auren a bisa sadaki N200,000.
Bayan ɗaurin aure, an gudanar da walima a gidan su ango da ke Namadi Close, Kaduna. Walimar ta ƙayatar, domin kowa ya ci, ya sha, wasu har guziri suka yi.

Wasu daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Aminu Ladan Abubakar (ALA), Ibrahim Yala, Adamu Kirfi, Nura MC Khan, Umar Ɗanhausa, Abdulrasheed Hasken waƙa, Anas Mai Shadda, Sagir Baban Kausar, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Auwal Hannun Dama, Albashir Yarima, Muhammad Showman, Babangida Afto da Sadiƙu Na Manzon Allah.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.

![]()







