• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ɗimbin jama’a tare da Gwamnan Kano suka halarci jana’iza da zaman makokin Hajiya Zainab Naniya, mahaifiyar jarumi Isah A. Isah

by Editors
November 28, 2025
in Labarai
0
Ɗimbin jama’a tare da Gwamnan Kano suka halarci jana’iza da zaman makokin Hajiya Zainab Naniya, mahaifiyar jarumi Isah A. Isah

Taron jana'izar Hajiya Zainab Tijjani Muhammad Naniya. Ita ce a cikin ƙaramin hoto.

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊIMBIN jama’a, ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, suka halarci jana’izar Hajiya Zainab Abdullahi Naniya, mahaifiyar jarumin Kannywood Isah A. Isah, wadda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025.

Kamar yadda mujallar Fim ta shaida maku a ranar, Hajiya ta rasu ne a wani asibiti da ke ƙasar Masar bayan ta yi kwana bakwai a asibitin.

Tun kafin a kai ta Masar ɗin dai, ta ɗauki lokaci tana kwance a asibiti a Kano inda daga baya aka fita da ita zuwa ƙasar wajen.

Hajiya Zainab Naniya, mai shekaru 62 a duniya, ita ce matar Farfesa Tijjani Naniya, mai ba Gwamnan Kano shawara a kan harkokin masarautun gargajiya.

Ta rasu ta bar ya’ya 8 – maza biyar, mata uku; Isah I. Isah ne babban ɗan ta.

Sheikh Ibrahim Khalil yana jagorantar yi wa Hajiya Zainab sallah. A bayan sa, Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran mahalarta sallar ne.

An dawo da gawar Hajiya Zainab Nijeriya a jiya Alhamis, aka yi mata sallah da misalin ƙarfe 1 na rana a masallacin Juma’a na Khalifa Isyaka Rabi’u da ke Titin Malam Aminu Kano a cikin garin Kano.

Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, shi ne ya jagoranci yi mata sallah, yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu daga cikin kwamishinonin sa da sauran manyan jami’an gwamnati suka halarta.

An rufe gawar Hajiya Zainab Naniya a maƙabartar bayan Gwauron Dutse, sannan aka ci gaba da zaman makoki a gidan mijin ta da ke kusa da gidan Khalifa Isyaka Rabi’u a Titin Malam Aminu Kano, inda dubun jama’a suke zuwa domin yin ta’aziyya.

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, yana yi wa Alhaji Isah A. Isah gaisuwar rasuwar mahaifiyar sa

‘Yan fim da dama sun shiga cikin dukkan mutanen da suke halarci jana’izar da kuma gidan gaisuwar. Daga cikin su akwai Alhaji Isma’ila Na’abba (Afakallah), Aminu A. Sharif (Momoh), Aminu Ilu Dambazau Auwalu Ɗangata, da sauran su.

Allah ya ji kan Hajiya Zainab, ya ba iyalai da ‘yan’uwan ta haƙurin jure wannan babban rashi, amin.

Isah A. Isah a gaban kabarin mahaifiyar sa, Hajiya Zainab
Allahu Akbar! Hajiya Zainab tana addu’a a gaban ɗakin Ka’aba

Loading

Tags: Hajiya Zainab Abdullahi NaniyaIsah A. Isahrasuwa
Previous Post

Mawaƙi a Kannywood, Ahmad Yariman Tiga zai angwance a ranar Juma’a 

Next Post

Aure: Ahmad Yariman Tiga ya zama cikakken mutum

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Aure: Ahmad Yariman Tiga ya zama cikakken mutum

Aure: Ahmad Yariman Tiga ya zama cikakken mutum

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!