HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin babban sakataren ta, Alhaji Abba El-Mustapha, ta bada umarnin kullewa tare da dakatar da gidan galar da ke New Road a cikin unguwar Sabon Garin Kano daga gudanar da duk wani aiki.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, ya ce, “Abba El-Mustapha ya sanar da kulle gidan galar mai suna ‘Fasaha Entertainment’ ne, biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da hukumar ta karɓa daga wurin ɗaiɗaikun al’umma, ciki har da ƙorafin Hukumar Hisbah da ta aika masa a kan yadda ake zargin gidan da yin abin da ya ci karo da tarbiyyar addinin Musulunci, wanda a cewar sa, yin hakan tamkar karya dokokin da su ka kafa Hukumar Tace Finafinai ne.”
Ya ci gaba da cewa, “Gidan galar zai ci gaba da zama a kulle har sai hukumar ta kammala binciken ta tare da bayyana matakin da ta ɗauka a kai.”
El-Mustapha ya godewa al’ummar Jihar Kano bisa goyon bayan da su ke b

a hukumar sa tare da ƙara yin kira ga al’umma da su ci gaba da sanar da hukumar duk wani abu da su ka gani na faruwa wanda ya karya dokokin hukumar.
Idan ba ku manta ba, Hukumar Hisbah da Hukumar Tace Finafinai sun ƙulla yarjejeniyar yin aikin tare domin cimma nasarorin da gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta saka a gaba na kau da baɗala a Kano.