A GOBE Lahadi za a ɗaura auren ‘yar jarumi a Kannywood, marigayi Malam Aminu Muhammad (Mai Chemist), wanda aka fi sani da Kawu Mala a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ na tashar Arewa 24.
Za a ɗaura auren Fatima Aminu Muhammad da Muhammad Sani Munammad a masallacin Abdurrahman Bin Auf da ke kusa da Asibitin Sha-Ka-Tafi, Haye Hotoron Arewa, Ring Road, Ƙaramar Hukumar Nassarawa, a Kano.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa abokin aikin marigayin jarumi Ɗalhatu Musa, wanda aka fi sani da Nuhu Kansila a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’, shi ne wanda ya bada sanarwar gayyatar ɗaurin auren a Facebook.
A cikin sanarwar ya ce, “Allahu Akbar! Allah mai girma, dattijo mai haƙuri, mai tausayi, mai yakana, mai kawaici, mai son taimaka wa marayu da marasa ƙarfi a harkar rashin lafiya, a nan jarin sa, lafiyar sa, lokacin sa, don hidimta wa al’umma ke tafiya. Ga shi yau an wayi gari babu shi, ya koma ga Mahaliccin sa, za a ɗaura auren ‘yar sa Fatima.
“Mun ci burin idan auren ta ya zo, ashe ba zai gani ba. Ya Allah na yi tawassali da ayyukan alherin sa, Allah ya sa ya na Aljanna, amin. Mun yi rashi babba.”
Kamar yadda wannan mujallar ta ba ku labari a lokacin, Malam Aminu Mai Chemist ya rasu ne a ranar Litinin, 8 ga Mayu, 2023 a Asibitin Nassarawa da ke Kano.