A YAU Asabar aka ɗaura auren Amina Muhammad, ‘yar fari ta jarumar Kannywood ɗin nan Hajiya Jamila Usman, wadda aka fi sani da Jamila Lasco.
An ɗaura auren Amina ne da masoyin ta Buhari Abdulhamid da misalin ƙarfe 10:00 na safe a unguwar Kargi Bahuri, Zariya, Jihar Kaduna, a kan sadaki N200,000.
Tun a jiya Juma’a, Jamila Lasco ta shirya bikin ranar iyaye mata (mother’s day) a Aso Motel da ke Titin Muhammadu Buhari (tsohon Waff Road), a Kaduna.
An fara bikin da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, har zuwa kusan ƙarfe 9:00 na dare.


Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci bikin sun haɗa da Wasila Isma’il, Malam Hudu Mazaje, Ɗansholi Comedian, Aminu Jahilin Malami, Aminu Haske, Ummi Hutu, Fadeey, Raliya Muhammad, Husna Annuri, Hadizan Baka, Al-Ameen Arewa, Ɗan Ilu, da Ɗan Soja.
Sauran su ne Ibrahim Wassh, Lawandi Lawash, Fanan Buzuwa, Abdullahi Abbas, Maryam Yola, Jamilu Nafseen, Hassan Ramin Kura, Yusuf Gwalmi, Aisha Mando, Nafisa Shoki, Zainab gambo, Nafisa Little, BG Khan da Usman Aphala.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

