A YAU ne mata marubuta su ka yi dandazo a gidan ‘yar’uwar su marubuciya , wato Malama Bilkisu Yusuf Ali, wadda aka ɗaura wa ‘yar ta Sarra Tasi’u Ya’u Ɓaɓura aure a yau.
Sun yi gangamin ne a gidan marigayi Sheikh Imam Dakta Yusuf Ali da ke Tudun Maliki, Kano, bayan an ɗaura auren da misalin ƙarfe 2:30 na rana.

Fitattun marubutan tare da sauran dangin uwar amarya sun taru sosai, inda su ka yi zaman taya murna.
An ci an sha, an ɗau hotuna.
A gobe Asabar kuma ake sa ran za a yi taron Ranar Uwa (Mother’s Day) a Prime Event Centre da Titin Haɗeja, Kano, inda nan ma ana sa ran marubuta mata da dama za su halarta.

Tuni marubuta da sauran abokan arziki su ka yi shirin zuwan wannan rana inda su ka fitar da kalar ankon da za su saka don yi wa Bilkisu kara.


