Fitacciyar jaruma Fati Ladan da mijin ta Yerima Shettima sun cika shekara 6 da aure a yau Juma’a, 20 ga Disamba, 2019.
An ɗaura auren su ne a Kaduna a cikin 2013.
Kafin auren, Fati ta kasance ɗaya daga cikin manyan jarumai mata a Kannywood.
Ta taɓa yin aure a baya, inda ta samu ‘ya mace.
Mijin ta na da bai so ta shiga harkar fim ba bayan sun rabu, har ya riƙa yi wa furodusoshin da su ka fara yin fim da ita barazanar cewa matar aure, kuma zai ɗauki mataki a kan su.
Bayan shekaru, Fati ta yi aure da Shettima Yerima wanda yanzu shi ne shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa, wato ‘Northern Youth Consultative Forum’ (NYCF).
Fati ce matar sa ta biyu, domin ya na da uwargida.
Zaman auren nasu ya yi daɗi matuƙa, kuma sun samu ƙaruwar ‘ya mace mai suna Humaira kamar yadda mu ka ba ku labari kwanan baya.
Don nuna jin daɗin wannan rana, ma’auratan mazauna garin Kaduna sun yi hotuna na musamman, waɗanda ƙwararren mai ɗaukar hoton nan, Steve Reinz, ya ɗauka.
Sun saka hotunan a soshiyal midiya, inda ɗaruruwan masoya su ka taya su murna.
Ga wasu daga cikin hotunan mun kawo maku.



