ALLAH ya yi wa fitaccen mai sayar da fayafayen Hausa ɗin nan a Kasuwar Barci, Kaduna, Malam Bukar Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bukar Maikaset), rasuwa a yau Alhamis, 19 ga Satumba, 2024.
Ya rasu a asibiti da safe, sakamakon rashin lafiya da ya daɗe yana fama da shi.
Shekarun sa 74. Ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya bakwai.
An yi jana’izar sa da ƙarfe 11 a Kaduna.
Malam Bukar ya shahara matuƙa wajen sayar da kasakasai na waƙoƙin Hausa har ma da na sauran yarurruka a tsawon shekaru sama da talatin.
Shagon sa da ke Titin Ibrahim Taiwo, a bakin Kasuwar Barci wurin zuwa ne ga ɗimbin mutane masu sha’awar waƙoƙi na ji da na kallo a lokaci mai tsawo.
Tsohon soja ne wanda zama ya kawo shi Kaduna inda ya zauna tare da iyalin sa har zuwa ƙarshen rayuwar sa.
Ya taɓa yin harkar kiɗa da waƙa na Turanci lokacin da yake soja da kuma jim kaɗan bayan ya yi ritaya. Daga nan ya shiga harkar kasuwanci.
Ya yi hulɗa da mawaƙan Hausa da dama, irin su Ahmadu Doka, Ɗanlami Nasarawa, Ɗanmaraya Jos, Musa Ɗanbade, yaran Mamman Shata, da sauran su.
Malam Bukar ya kasance mutum mai riƙon addini matuƙa wanda kowa ya san shi da shiga jam’i a cikin kowane hali.
Ɗimbin mutane sun shaida wa mujallar Fim cewa mutumin kirki ne wanda ya zauna da kowa lafiya, kuma ba ya da abokin faɗa ko husuma.
Allah ya rahamshe shi, amin.