• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙarairayi 16 a martanin Aliyu Ibrahim Kankara

by DAGA IBRAHIM SHEME
September 28, 2018
in Marubuta
0
Dr. Aliyu Ibrahim Kankara

Dr. Aliyu Ibrahim Kankara

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A RANAR Juma’a da ta gabata, jaridar Aminiya ta soma buga hirar da wakilin ta, Bashir Yahuza Malumfashi, ya yi da ni a kan sabon bugun littafin tarihin Alh. (Dr.) Mamman Shata Katsina mai taken “Shata Ikon Allah!” wanda ya fito kwanan nan. Za ta ci gaba da buga hirar a gobe Juma’a, in-sha Allah. 

Jiya, sai ga martani ya fito daga Dr Aliyu Ibrahim Kankara, ɗaya daga cikin mu huɗu da mu ka yi binciken farko don a rubuta littafin. Ban so in yi cacar baki da Ƙanƙara kan wani abu da ya shafi littafin ba, shi ya sa ma na yi hirar da Aminiya gaba-gaɗi a bisa tunanin ko mutum ba ya ƙaunar Allah idan ya karanta zai yarda da cewar lallai haƙiƙanin abin da ya faru kenan. Haka kuma akwai waɗanda su ka ce mani, “Kada ka kula shi, domin ba matsayin ku ɗaya a idon al’umma ba.”  

To, ba maganar matsayi ba ce, magana ce ta menene mu ka bar wa tarihi; idan na yi shiru kan karan-tsayen da Ƙanƙara ya yi wa gaskiyar abin da ya faru, to ban yi wa tarihi adalci ba. Haka kuma ni ba irin mutanen nan ba ne da za su ga ƙarya muraran su ƙyale saboda wani. Shi ya sa na ga dacewar in nuna wa jama’a cewa akwai ƙarairayi jingim a rubutun na Ƙanƙara, waɗanda na ke so a fahimta. Daga nan, idan mutum ya karanta, sai ya zaɓi na zaɓe! 

Kafin in jero ƙarairayin, ina so in yi shimfiɗa da cewar ba wannan ba ne karo na farko da Aliyu ya fara shara ƙarya game da tarihin Shata ko dangantakar da ya ce wai ya na da ita da mawaƙin. Tun a farkon haɗuwar mu, lokacin da ya kawo mani takardun da ya rubuta kan Shata don in gani, na ga ɗimbin abubuwan shaci-faɗi da ya rubuta waɗanda hankali ba zai iya ɗauka ba, waɗanda ko ɗan ƙaramin bincike ma zai nuna wa mutum cewar ƙarya ne. Irin waɗannan abubuwan, na yi watsi da su a lokacin da na ke rubuta littafin “Shata Ikon Allah!” da aka ƙaddamar a cikin shekarar 2006. Na san Ƙanƙara bai ji daɗin watsi da na yi da su ba, kuma hakan na daga cikin dalilan shi na warewa daga gare mu, mu “marubutan littafin Shata”, ya tafi ya ɗauki littafin mu ya baddala shi ya fito da wani a matsayin nasa (zan yi magana kan wannan a nan gaba, ba a yau ba). 

Na biyu, a zantuttukan sa a soshiyal midiya da hirarrakin sa a rediyo na sha jin irin yadda Ƙanƙara ya ke zubo ƙarairayi game da Shata ko tarayyar da ya ke iƙirarin ya na da ita da Shatan, ba tare da kawo hujjar da za ta tabbatar da hakan ba. Hasali ma dai, Ƙanƙara ya saba da sheƙa ƙarya game da Shata ta yadda har akwai alamun ya yi amanna da cewa ƙarairayin sa gaskiya ne. Shi ya sa a duk inda ya zauna, sai ya dinga zuba ratatata kan tarihin Shata da ba gaskiya ba ne, ya ɗebo dahir ya gwamutsa da ƙirƙira, ya fitar da wata magana wadda yawancin masu saurare ba za su kama ba.

Har ta kai mutane da dama na mamakin yadda za a ce wai mutum mai PhD ne ke magana haka babu kangado, sai ka ce ko sakandare bai gama ba! Irin wannan kame-kamen ne na gani a rubutun shi na jiya mai take irin na taken hira ta da Aminiya, wato “Ni Na Fara Rubuta Littafin Tarihin Shata”, taken da shi kan sa ba daidai ba ne (kamar yadda na faɗa wa Bashir Yahuza bayan na karanta hirar da ya yi da ni). 

Bari mu koma kan ƙarairayin Ƙanƙara. Da farko, ban damu da yaushe ne Ƙanƙara ya soma ƙaunar Shata ba; ko tun ya na cikin ciki ya fara son sa, ba damuwa ta ba ce. Amma wace irin soyayyar ya ke yi masa har ta kasance iyalin marigayin ba su yarda da abubuwan da ya ke yaɗawa game da mahaifin su ba? Sannan wace irin soyayya ce ya ke yaɗawa a hirarrakin sa ta yadda duk manazarcin da ya bincika zai tarar da cewa zuƙi-ta-malle ce wadda ba ta iya tsayawa da ƙafafun ta? Misali, “sai da aljannu su ka yi wa wata ‘yar bori bushara da haihuwar Shata!” “A ranar da aka haifi Shata, an ji kalangai su na tashi a sararin samaniyar garin Musawa!” “Kafin ranar sunan Shata, Shatan ya ɓace daga zanin goyon sa, ba a sake ganin sa ba sai bayan kwana uku!” “Kai, Shata ba mutum ba ne, aljani ne!” Da dai sauran su. 

Bari mu duba martanin Ƙanƙara daki-daki.

1.Cewar Ƙanƙara: “Cikin 1990 na ya kai wa Shata littafin da na rubuta”:

Wannan maganar, da makamantan ta da ya yi a baya, ba gaskiya ba ce. Ba zan ce Ƙanƙara ba ya son Shata kafin haɗuwa ta da shi ba, amma wallahi shi da Shata ba su san juna ba sai da na kai shi wajen Shatan a Funtuwa bayan haɗewar mu. Zurfin hulɗa ta da Ƙanƙara, tare da zurfin sanayya ta da Alhaji Shata da yaran shi, ta isa ta sa in san idan Ƙanƙara da mawaƙin sun san juna kafin haɗuwa ta da Ƙanƙara. Babu wani lokaci da wani daga cikin su ya faɗa mani ya san ɗayan. In da Ƙanƙara ya san Shata kafin in kai shi wurin sa, to da ya faɗa mani. Haka kuma in da Ƙanƙara ya yi wani littafi kan Shata har ya kai masa, to da ya faɗa mani a lokacin da na ce mu je in gabatar da shi ga Shata a cikin 1997. Kuma in da ƘanƘara ya yi littafi kan Shata, to da ya ba ni shi lokacin da mu ka haɗe, mu ka shiga fafutikar tattara tarihin Shata domin yin littafi.

2. “Wai a 1994 Ƙanƙara zai tafi NYSC, ya kai wa Shata littafi”. Wannan ma ƙarya ce ya shirya. Ban san wani labarin Ƙanƙara ya nemo izinin Shata don ya rubuta wa wata ƙungiya a Kano tarihin Shata ba, wanda har ya rubuta ya kai masa da zai tafi bautar ƙasa. A rubutun shi, Ƙanƙara ya ce har ya kammala littafin a 1994, to ya aka yi a 1997 da ya ba ni warƙoƙin da ya rubuta na ga ba su fi shafi 15 na rubutun hannu ba? Shi ne littafin? Ya aka yi bayan haɗuwar mu, mu ka dinga faɗi-tashin bincike don fito da littafin, abin da ya ɗauke mu shekaru? Sannan idan har a 1994 ya rubuta littafin, to daga 1991 da na fara binciken tarihin har zuwa lokacin babu shakka da na samu labarin sa a wajen Shata ko Ya’u Wazirin Shata ko wani yaron Shata. A gaskiya, Ƙanƙara bai rubuta littafi ba a lokacin.

3. “Wai Shata ya umarci Ƙanƙara da ya yi hira da wasu mutanen Legas da ya waƙe”.

Wannan magana ba gaskiya ba ce, domin in da an yi hakan to babu shakka da Ƙanƙara ya je ya yi waɗannan hirarrakin. Tun da mu ka fara bincike kan tarihin Shata har mu ka gama a 2006, Ƙanƙara bai kawo mana hira ko da ƙwaya ɗaya da ya yi da ɗaya daga cikin mazauna Legas da Shata ya yi wa waƙa ba.

4. “Wai a 1995 Ya’u Wazirin Shata ya yi wa Ƙanƙara maganar Ibrahim Sheme”.

A cikin 1995 ba mu haɗu da Ƙanƙara ba, ban san shi ba. Hasali ma dai, sai bayan haɗuwar mu da na ɗauki Ƙanƙara na kai shi wajen Shata sannan ne ya san Ya’u Wazirin Shata. Ni ne na ɗauki Ƙanƙara a mota ta, bayan mun bar gidan Shata, na kai shi gidan Alh. Ya’u na gabatar da shi ga Ya’un. Ko kaɗan Ya’u Waziri da Ƙanƙara ba su nuna wa juna sanayya ba lokacin da na sada su. In da a ce an san Ƙanƙara a fadar Shata, to da shi mawaƙin da shugaban ‘yan amshin nasa sun nuna haka lokacin da na kai Ƙanƙara wajen su.

5. “Wai Ibrahim Sheme ya zauna gida ɗaya da wani Kabiru Ɗan’azumi Ƙanƙara a unguwar Badikko, Kaduna”.

A Badikko, na kama hayar gida sukutum ne (2-bedroom flat da garejin mota da filin tsakar gida). Ban zauna da kowa a gidan ba sai mata ta. Wannan magana shirme ce.

6. “Wai ba Ibrahim Malumfashi ya haɗa Ƙanƙara da Ibrahim Sheme ba”.

Babu shakka, ban taɓa jin ko sunan Ƙanƙara ba sai a bakin Malumfashi lokacin da ya buƙace ni da in haɗu da shi in ga abin da ya rubuta kan Shata. Farfesa Malumfashi na da rai, zai iya tabbatar da wannan magana ko akasin haka.

7. “Wai a 1995 Sheme da Ƙanƙara su ka haɗu har Sheme ya nuna masa aikin littafin da ya yi. Daga nan ba su sake haɗuwa ba sai a 1997.”

Wannan ma wata ƙaryar ce. A 1995, ban taɓa jin sunan Ƙanƙara ba, sai a 1997 lokacin da Ibrahim Malumfashi ya haɗa mu. Kuma tun da mu ka haɗu ba mu taɓa rabuwa ba har lokacin da aka ƙaddamar da “Shata Ikon Allah!” a cikin 2006.

8. “Wai Sheme ya ziyarci Ƙanƙara a ofis ɗin sa a Kaduna Polytechnic a 1997 inda ya nemi su haɗe su yi littafi ɗaya”.

Wannan ma ƙarya ce. Tun lokacin da Malumfashi ya sada ni da Ƙanƙara, ba a yi ko mako ɗaya ba na amince mu ka haɗe. Sannan ban taɓa zuwa ofishin Ƙanƙara a Kaduna Polytechnic ba; wani zuwa da na yi sau ɗaya rak, na je ne domin in taimaka masa kan wata wuta da ya kunno wa kan sa. Matsalar ita ce wata yarinya ɗaliba ta kai Aliyu Ƙanƙara ga hukumomin makarantar, har an kafa kwamitin musamnan ana bincike. Na je ne bisa buƙatar Ƙanƙara in ga ko zan iya sasanta lamarin, a matsayin sa na abokin aiki na kan littafi. A ƙarshe, ba mu samu nasara ba, domin kwamiti ya bada shawarar a kori Ƙanƙara daga aiki. Haka kuwa aka yi, aka kore shi daga aikin koyarwa bisa koken da ɗalibar sa ta yi. Wannan ne ya sa ya koma aiki a wani kamfanin wasu ‘yan ƙasar Chaina masu haƙar ma’adinai a yankin Sakkwato (aikin da Saleh Abu Katsina ya sama masa). Daga can ya ƙuƙuta aka ɗauke shi aiki a matsayin malamin makarantar sakandare (GDSS) ta garin Daudawa da ke Faskari LGA a Jihar Katsina. Malamin Polytechnic ya koma malamin sakandare kenan! Daga nan ne, bayan shekaru, aka ɗauke shi aiki a Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua a Katsina. Nan gaba zan dawo kan ainihin kes ɗin nan da ya sa aka kore shi daga Kadpoly da matsalar da ya samu da Chanis ɗin nan da yadda aka yi ya koma Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma, musamman ma yadda waɗannan matsalolin su ka kawo mana cikas wajen kammala littafin “Shata Ikon Allah!”

9. “Wai matar Ƙanƙara na shaidar…!”

To, ni ban sani ba idan maganar Kassu Zurmi gaskiya ce da ya ce “mutum ba ya shaidar ɗan’uwan shi ko hwada” da kuma faɗar Shata a waƙar Dambu Ɗan Mamman cewa “wace shaidar ɗan ka za yai ma, in ka haɗa duka duk dai Dambu ne?”

Wallahi, ban taɓa zawarcin Ƙanƙara don mu haɗe mu yi littafi ba. Kamar yadda na faɗa, mun haɗe da Ƙanƙara tun a satin farko na haɗuwar mu a cikin 1997. Idan na taɓa zuwa gidan shi, hakan ba ya rasa nasaba da aikin da mu ka tsunduma yi ne, ba domin mu haɗe ba tunda mun riga mun haɗe. Amma shi ya kan zo gida na ya fi sau shurin masaƙi, idan za mu yi tafiya ko idan zai karɓi kuɗi a waje na. Saboda haka maganar wai ina zawarcin sa domin mu haɗe ba gaskiya ba ce.

10. “Wai Sheme ya fito ‘sabon-huji’, ya fito fes, ya kammala karatu na biyu”. A 1997 lokacin da na fara ganin Ƙanƙara har mu ka haɗe mu yi littafi, ni ba sabon yanka rake ba ne wajen kammala karatun digiri na biyu.

Na samu M.A. Journalism Studies daga Cardiff University, a U.K., tun cikin 1994 (shekaru 3 kafin in fara ganin Ƙanƙara a rayuwa ta). A 1997 ina daga cikin manyan editoci a kamfanin jaridar New Nigerian.

11. “Wai Sheme na tura Ƙanƙara ya yi masa hira da jama’ar Shata saboda shi ba ya da lokaci”.

Kamar yadda na faɗa, na fara hira da Shata a 1991 domin rubuta tarihin shi. Shekaru 6 kenan kafin in fara ganin Ƙanƙara. A tsawon wannan lokacin, na yi hira da mutane masu yawan gaske. Misali: Garban Bichi, Indon Musawa, Sa’in Katsina Amadu Nafuntuwa, Amadu Doka, Tukur Othman, Turi Muhammadu, Musa Musawa, Munari Jikar Mairo, Nagwandu Mainama, Laila Dogonyaro, Amadu Doka, Ɗanmaraya Jos, Hakimin Bakori Alhaji Tukur Idris Nadabo, Shehu Maigidaje, Halilu Ahmed Getso, Bala Maikaka, da sauran su da dama. Kuma na yi hirarraki da yaran Shata da su ka haɗa da shugaban ‘yan amshi Alhaji Ya’u Wazirin Shata da shugaban makaɗan kalangun Shata, wato Bawa Dungun Mu’azu. Sannan na je Musawa na yi hira da ‘yan’uwan Shata da abokin sa irin su Mal. Ali Ɗanƙane. Duk wannan ya faru ne KAFIN in ma san wani wai shi Aliyu Ƙanƙara. Sannan bayan haɗuwar mu da shi, na ci gaba da yin wasu hirarrakin. Saboda haka maganar ba ni da lokaci ma ƙarya ce.

Tura Ƙanƙara da na yi zuwa wasu garuruwan, kamar Bauchi da Gombe, da kuma Musawa saboda ya yi mana hira da Magajin Gari Malam Abdullahi Inde da wasu mutanen, duk cikin raba aiki da mu ka yi bayan mun haɗe mun zama mu 4 a aikin. Ba gajiyawa ba ce. Ko ya manta cewar mun raba aiki ta yadda su Yusuf Albasu da Ali Malami su ma za su samo mana wasu hirarrakin, musamman a Kano? Wannan shi ne daɗin haɗewar ai, wato wannan ya kama nan, wancan ya kama can. Hakan ne ya sa ni ne na yi hira da mutane irin su Dauda Mani da Sarki Jinjiri da Goshin Ɗangude ba tare da Ƙanƙara ya sani ba sai daga baya na faɗa masa. Abin lura shi ne duk da yake ina yin hirarrakin nan kamar yadda na lissafa a sama, ai kuma ni ne mai rubuta littafin; ni ne wanda ke karance duk abin da su Ƙanƙara su ka yayumo, in fitar da ma’ana daga ciki, in jera bayanan a cikin littafi inda ya dace; shin ko wannan bai isa aiki ba?

Alhaji Mamman Shata

12. “Wai Ƙanƙara ya haɗa Sheme da wasu mutanen Shata a Kaduna tunda shi bai san su ba”. 

Hankali zai iya ɗaukar wannan maganar kuwa? Mutum ne ya same ka ka na bincike domin rubuta littafi, har ka shafe shekara shida ka na yi. Kuma a Kaduna ka ke zaune. Ka yi tafiye-tafiye a wasu garuruwa. To ya za a ce ba ka ma san mutanen da su ne ka ke samo bayani a wajen su ba?

Ƙanƙara ya ambaci Alh. Nagwandu Mainama, wai shi ya haɗa ni da shi. Wannan ba gaskiya ba ce. Na yi hira da Nagwandu a mayankar da ke Tudun Wada, Kaduna, ba tare da Ƙanƙara ba. 

Kuma ya ambaci Alh. Amadu Doka mai kukuma, wai shi ya haɗa mu. Ka ji tantagaryar ƙarya! Ƙanƙara ya manta cewa Amadu Doka amini na ne na tsawon shekaru tun kafin mu haɗe, sannan ni ɗin nan ni ne na fara kai shi wajen Amadu Dokan har gida, na gabatar da shi? A nan ma dai, ƙarya ce ya yi wa kwalliya domin ya sayar da ita ga wanda bai ankara ba!

 Na yi hira da Amadu Doka domin sakawa a littafin Shata tun a cikin 1993 (shekaru 4 kafin in fara haɗuwa da Ƙanƙara). An buga hirar a mujallar Rana (wadda kamfanin Hotline ke wallafawa) ta ranar 19 ga Oktoba, 1992. A lokacin, ni ne Editan mujallar, kuma ban san wani Aliyu Ƙanƙara a duniya ba. Ya za a yi ka haɗa ni da mutum a 1997 bayan har na yi hira da shi a gidan sa a 1992?

13. “Wai cikin 1998 Sheme ya tafi Funtuwa ya tarar Shata ya kwanta asibiti a Kano”. 

Ban samu Shata domin ya kwanta a asibiti ba. Kamar yadda na sha faɗi, a matsayi na na jagoran rubuta tarihin Shata, na sha zuwa in same shi kan wani abu da ya danganci aikin. Kuma ba lallai ba ne sai na je tare da Ali Ƙanƙara. Lokacin wannan ziyarar da Ƙanƙara ke magana, na je ne domin in yi wata sabuwar hira da Shata kan wasu abubuwa da na lissafa waɗanda jama’a ke magana a kan su, misali batun cewar wai Sule Jikan Korau ya taɓa marin Shata, da batun wai Shata ne ya yi wa Ali Ɗansaraki makaru ya kasa waƙa, da batun Garba Goga ne ya fara kai Shata garin Funtuwa kamar yadda mawaƙin ya ke ambata a Bakandamiya. Kaset ɗin hirar, na ba Ƙanƙara ya rubuta shi a takarda, kuma har yau ɗin nan ya ƙi dawo mani da kaset ɗin. To, a wannan zuwan ne Shata da kan shi ya ba ni labarin su Yusuf Tijjani Albasu da Ali Malami. A lokacin, ni dai ban taɓa jin wai an kwantar da Shata a asibiti ba. 

14. “Wai Sheme ya ɗauki Ƙanƙara tare da wani abokin Shemen mai suna Aimana Datti Usman, su ka tafi Funtuwa”.

Ban taɓa yin aboki mai wannan sunan ba. Ina jin dai Aimana abokin Yusuf Albasu ne da su ka je Funtuwa taro lokacin da na gayyato su daga Kano. Ni Yahaya Umar na ɗauka a Zariya. 

15. “Wai Shata ne ya ce a haɗe a yi littafi daya”. 

Wannan ba gaskiya ba ne. Maƙasudin kiran su Albasu da Malami shi ne a ƙwace littafin su, a kore su, bisa hujjar cewa ba a ba su izinin rubuta littafin ba. Da ni aka yi wannan shiri, ba a gaban Ƙanƙara ba. Ni ne na bada shawarar a yi littafi ɗaya, bayan mun fita waje na duba aikin da su ka yi, na ga ya burge ni matuƙa domin sun yi hirarraki da wasu mutane da mu ke so mu yi hira da su, irin su Abubakar Uwawu, Hassan Hadi, Delun Kunya, Hauwa Maituwo, da sauran su. Shawarar da na bayar cewa a haɗe, ta ba kowa mamaki, har shi kan sa Shatan, domin ba ta cikin shirin da aka yi a makon da ya gabata. Sannan ko kaɗan Ƙanƙara ba ya goyon bayan haɗewar, kawai dai don babu yadda zai yi ne tunda ni ne a matsayin shugaban shi. 

16. “Wai Shata ya manta da littafin da Ƙanƙara ya rubuta wa ƙungiya, shi kuma kawaici ya hana shi magana”. 

Wannan ma wani soki-burutsu ne. Lokacin da mu ka je taron da mu ka haɗe da su Ali Malami da Yusuf Albasu a Funtuwa, an fi shekara ɗaya da haɗewa ta da Ƙanƙara. Wato kenan Shata ya san ni da Ƙanƙara, saboda haka ya yi maganar wani littafin ƙungiya ai bai taso ba. Me ya sa ma a lokacin da na fara kai Ƙanƙara wajen Shata, na ce masa ga wani wanda za mu yi aikin rubuta littafin da shi, ba su nuna sun san juna ba? Dalili shi ne babu wata sanayya tsakanin Shata da Ƙanƙara, sannan Ƙanƙara bai taɓa kai wa Shata littafin da ya ke iƙirarin ya rubuta ba. In da akwai littafin, kuma in da sun san juna, to da tun tuni na sani. Wannan maganar, kawai ƙirƙira ce aljannun da ke damun ƙwaƙwalwar Aliyu Ibrahim Ƙanƙara su ka ba shi, shi kuma ya hau kai ya na ƙoƙarin yaudarar mutane da ita.

 Ina kira ga Aliyu Ƙanƙara da ya nuna guntun rikodin ko ƙwaya ɗaya da ya taɓa yi da Shata, wato wata hira da su ka yi, ko wani hoto da su ka taɓa ɗauka tare, a matsayin nuna sanayyar da ya ke ƙaryar sun yi wa juna shi da mawaƙin. Na san babu. Dalili shi ne, Ƙanƙara da Shata ba su san juna ba kafin in kai Ƙanƙara wajen sa, kuma da na kai shi ɗin, babu wata sanayya da Shata ya yi masa, domin bai taɓa zuwa wajen Shata ba tare da ni ba, sai idan na kai shi. Hasali ma dai, Ƙanƙara bai taɓa yin hira da Shata domin yin littafi ba. Duk abin da ya ke faɗa a bayan rasuwar Shata, ƙirƙira ce irin ta marubucin da ƙwaƙwalwar sa ta motsu, ya na ganin dodon wani abu da ya ke ganin kamar ya taɓa faruwa a rayuwar sa bayan kuwa bai taɓa faruwa ɗin ba.

Zan yi zango a nan. Zan kawo ci-gaban wannan raddi nan gaba kaɗan, domin wannan magana yanzu na fara ta. 

Bissalam.

Loading

Previous Post

Nason Musulunci A Kirarin Hausa: Misalai Daga Kirarin Da Lawal Tsangaya Ya Yi Wa Mamman Shata

Next Post

Manya ɗibar fari: Tarihin Rupert East, tsanin adabin Hausa

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Marubuciya Dakta Aliyah Adamu Ahmad da littafin ta na tarihin Dakta Ripert M. East

Manya ɗibar fari: Tarihin Rupert East, tsanin adabin Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!