Allah ya ɗauki ran darakta a Kannywood, Malam Kabiru Shehu Yaro, wanda aka fi sani da Kokobi.
Kokobi ya rasu da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin yau Talata, 5 ga Nuwamba, 2024, bayan gajeruwar rashin lafiya.
Za a yi jana’izar sa a gobe Laraba a gidan sa da ke Zango Road, Tudun Wada, Kaduna.
Allah ya jiƙan shi da rahama.