• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 9, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba zan iya misalta murna ta kan karar da aka nuna mini a bikin ƙanwa ta Sa’adatu ba, inji jarumar Kannywood Raihan Ƙamshi

by MUKHTAR YAKUBU
December 3, 2024
in Ranar Murna
0

Daga hagu: amarya Sa'adatu da kuma Raihan

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMAR Kannywood Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi) ta bayyana cewa ba za ta iya misalta irin daɗin da ta ji ba kan irin karar da mutane suka yi mata a lokacin bikin auren ƙanwar ta, Sa’adatu.

Bikin aure ne ƙasaitacce wanda aka daɗe ba a yi irin sa a Kannywood ba.

A wurin taron bikin, mujallar Fim ta lura da cewa kusan duk wata jaruma mai ji da kan ta a cikin masana’antar finafinan ta halarta.

Ganin yadda hotunan bikin suka cika soshiyal midiya da ƙirjin bikin, wato Raihan, har wasu mutane suna zaton ita ce ta yi aure, suna yi mata fatan alheri da addu’ar Allah ya zaunar da ita a gidan mijin ta lafiya.

A tattaunawar ta da mujallar Fim bayan taron, Raihan ta yadda take ji kamar haka: “To da farko dai zan fara da cewa alhamdu lillahi, ina ƙara godiya ga Allah da ya ba ni ikon gudanar da wannan taro, wanda kuma taro ne da ban yi tsammanin zai tafi haka ba, sai kuma abin ya zo ya ba ni mamaki saboda ya tafi yadda ban taɓa tsammani ba.

Raihan a tsakiyar amarya Sa’adatu da ango Abdulrazaq

“Taro ne na shirya na bikin ƙanwa ta wacce nake jin ta tamkar ‘yar da na haifa, don haka taron ba na biki na ba ne kamar yadda mutane suke faɗa, don tun da hotunan bikin suka yaɗu mutane suna ta kira na suna yi mini fatan alheri, su a zaton su auren na ne.

“Wasu suna kira na su tambaye ni, wasu kuma kawai suna yi mini fatan alheri ne, sun zata nawa ne.

“Amma dai gaskiya ita wannan amarya Sa’adatu ƙanwa ta ce, ita ce ƙarama a ɗakin mu. Kuma gaskiya dai ba ni da kamar ta. Ina son ta sosai, don na tashi da ita tun tana ƙarama, kusan zan iya cewa na raine ta.

“Ina alfahari da yarinyar nan Sa’adatu sosai, saboda jinin jiki na ce, kuma ta kasance yarinya mai biyayya daidai gwargwado yadda ko ni na haife ta iya biyayyar da za ta yi mini kenan.

Ƙirjin bikin, Raihan
Teemah Makamashi na yi wa Raihan liƙi a wurin bikin

“Sannan kuma duk wani wanda ya san ta ko yake zuwa gidan mu, to za ka yi alfahari da Sa’adatu, saboda yarinya ce mai biyayya. Wannan ya sa na ga duk abin da na yi mata a cikin sabgar bikin nan ban yi asara a cikin rayuwa ta ba, don duk wani abu da zan yi wa ɗan da zan haifa to shi zan yi mata.”

Dangane da yadda aka tsara bikin kuwa, cewa ta yi: “Shi wannan biki ka san kana yin naka ne, Allah yana yin nasa. Allah ya kawo mini lokacin auren Sa’adatu, sai na ji a rai na ina da buƙatar na tara masoya abokan sana’a ta da ‘yan’uwa da abokan arziki baki ɗaya don su taru su taya ni farin cikin bikin. Kuma suka ba ni haɗin kai, na kusa da na nesa, da dukkan wanda ban yi tsammani ba sun halarci taron bikin kuma sun goya mini baya, sun yi mini kara da taya ni farin ciki ɗari bisa ɗari.

Yayar amarya da ƙawayen ta
Raihan da A’isha Humaira

“Biki ne wanda ya tara dandazon mutane daga garuruwa daban-daban. Mutane sun zo mini daga Abuja, Kaduna, Katsina, Jos, Sokoto, Yobe, Bauchi, Gombe, Zaria, Ƙanƙara da sauran garuruwa da mutane na amana na mutunci da suka zo wajen wannan taron bikin.

“Kuma kamar dai yadda ka gani, shi wannan biki mun ɗauke shi tsawon kwana uku, inda ranar farko muka yi bikin Ƙauyawa wanda muka yi a cikin farfajiyar gidan mu da ke unguwar Dukawuya.

“Sannan kuma a rana ta biyu mun yi bikin Kamun amarya a titin gidan Zoo. Sai kuma taron liyafar cin abincin dare da muka shirya a ranar Asabar, 30 ga Nuwamba.

“Sai kuma ranar ɗaurin auren, wato ranar Lahadi, 1 ga Disamba, inda aka ɗaura auren a gidan kakannin mu, wato gidan Madakin Kano a unguwar Yola. A Masallacin Juma’a na unguwar Yola aka ɗaura.

“Bayan nan mun yi taro na liyafar cin abinci. Sai kuma bayan an kai amarya ɗakin mijin ta su ma dangin miji suka shirya nasu taron bikin.

“To yanzu dai amarya ta tare a gidan mijin ta, ta bar ni da kewa.”

Daga hagu: Mansurah Isah, Teemah Makamashi da Saddika Jibrin Sarki

Ko yaya Raihan ta samu kan ta a cikin ɗimbin masoya da suka halarci taron bikin?

Amsa: “Gaskiya na samu kai na a cikin wani farin cikin da ba zan iya misalta shi a cikin rayuwa ta ba, kasancewar yadda na ga mutane sun yi mini kara, musamman ‘yan Kannywood sun yi mini kara, domin sun yi mini da jikin su da lokacin su da aljihun su, da kuma kalamai masu daɗi, wanda wasu a cikin ‘yan fim ma duk da su aka shirya bikin, wanda kuma sun ba ni gudunmawa tun kafin bikin ya zo, da baki wasu kuma da jikin su da ƙafafuwan su, duk an yi mini kara.

“Babu abin da zan ce sai dai Allah ya saka da alheri.

“Kuma gaskiya na samu darasi sosai. Da man ana cewa sai wani abu na farin ciki ya same ka ko akasin haka sannan kake gane cikakken masoyi. Hakika a wannan biki da ya zo mini, waɗanda ban ma san da cewa ƙaunar da suke yi mini ta kai haka ba, to a wannan bikin na gane cewa ƙaunar da suke yi mini ta wuce yadda nake tunani. Wasu kuma da nake tunani suna ƙaunar tawa, wasu na gane cewa ashe duk abin a baki ne bai kai cikin zuciyar su ba.

“Saboda ni duk wanda bai taya ni farin ciki a wannan bikin ba, gaskiya to ba a cewa komai! Amma dai na san matsayi na a wajen sa.

“Don haka dai har kullum ina ƙara godiya ga Allah, kuma ina alfahari da masoya na, don masoya sun nuna mini ƙauna, saboda su ne ni, kuma ni ce su, idan babu su babu ni.

“Kuma gaskiya iya kara dai an yi mini. Ni da man duk sabga ta idan ta tashi sai an nuna mini kara. Amma saboda yadda nake jin Sa’adatu a rai na, karar da aka nuna mini a bikin ta sai na ga kamar ba a taɓa nuna mini wata kara ba kamar wannan. Don haka ina matuƙar godiya ga dukkan jama’ar da suka halarci taron bikin auren da ma waɗanda suka aiko da saƙon taya murna saboda ba su samu zuwa ba, don haka na ji kuma na ga saƙon ku. Babu abin da zan ce sai godiya.

Amarya Sa’adatu tare da angon ta Abdulrazzaq

“Saboda ko da na ɗauko bikin ina tunanin zan kashe kuɗi na, to ashe ba kuɗi na zan kashe ba, kuɗin masoya na ne.

“Don gaskiya masoya sun taka rawar gani sosai a cikin harkar bikin nan. Sai dai fatan alheri. Ina yi wa duk wanda ya saka hannun sa a cikin wannan harkar ta bikin Sa’adatu, ko da kuɗin sa ko da jikin sa, dukkan su ina yi musu fatan alheri, ina godiya. Kuma dukkan abin da mutum ya fitar, ina fatan Allah ya linka masa babu adadi.

“Na ji daɗi sosai saboda gaskiya an nuna mini kara. Yayye na sun yi mini, ‘yan’uwa na kenan. Su kan su ina godiya a gare su, saboda sun ba ni haɗin kai a matsayi na na ni ce ƙarama a cikin su, to amma an ɗauki ragamar bikin an bar mini kamar an ɗora mini girman, kuma na karɓa, kuma abin ya yi mini daɗi.

“Ina godiya, musamman babban yaya na, Alhaji Rabi’u Sabi’u Cheɗi, da sauran yayye na mata su ma sun taka rawar gani.

“Sai kuma ƙawaye na na kusa sosai da aka yi ta faɗi-tashi da su waɗanda suna da yawa, sun fi ƙarfin a kama suna. Ina godiya sosai, Allah ya bar zumunci, Allah ya haɗa mu a cikin ladar.”

Manyan ƙawayen yayar amarya, su Halisa Muhammad a wajen taron bikin

Loading

Tags: bikin auremurnaRaihan Imam Ahmad Ƙamshi
Previous Post

A taron mu na bana za mu haska fim ɗin ‘Jamilar Jammaje,’ inji Kabiru Jammaje

Next Post

Tsohuwar jaruma a Kannywood, Rasheeda Maisa’a ta cika shekara ɗaya cif a ɗakin mijin ta

Related Posts

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu
Ranar Murna

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu

May 2, 2025
Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu
Ranar Murna

Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

April 25, 2025
Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 
Ranar Murna

Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 

April 20, 2025
Ahlan tare da 'yar sa Hassana, amaryar mako mai zuwa
Ranar Murna

Jarumi a Kannywood, Ahlan zai aurar da ‘yar sa Hassana

February 16, 2025
Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir
Ranar Murna

Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir

December 20, 2024
Mawaƙi Abdul Respect ya zama angon Hassana Abubakar
Ranar Murna

Mawaƙi Abdul Respect ya zama angon Hassana Abubakar

December 16, 2024
Next Post
Tsohuwar jaruma a Kannywood, Rasheeda Maisa’a ta cika shekara ɗaya cif a ɗakin mijin ta

Tsohuwar jaruma a Kannywood, Rasheeda Maisa’a ta cika shekara ɗaya cif a ɗakin mijin ta

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!