• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

A taron mu na bana za mu haska fim ɗin ‘Jamilar Jammaje,’ inji Kabiru Jammaje

* 'Zan ƙaddamar da littafin hikaya na Turanci, A Gentle Breeze '

by MUKHTAR YAKUBU
December 2, 2024
in Labarai
0
A taron mu na bana za mu haska fim ɗin ‘Jamilar Jammaje,’ inji Kabiru Jammaje

Malam Kabiru Musa Jammaje

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAKARANTAR nan mai suna Jammaje Academy za ta shirya taron ta na shekara-shekara kwanan nan a Kano tare da ƙaddamar da sabon littafin hikaya na Turanci wanda mamallakin makarantar ya wallafa.

Makarantar, wadda ta yi fice wajen koyar da ilimin Turanci a rassan ta da ke wasu jihohin ƙasar nan, za ta yi taron na bana ne a ranar 26 ga Disamba ɗin nan a wani ɗakin taro a Jami’ar Bayero, Kano, inda za a gabatar da jawabai tare da nishaɗantar da mahalarta.

Shugaban makarantar, Malam Kabiru Musa Jammaje, ya shaida wa mujallar Fim yadda taron zai kasance.

Ya ce, “A taron na bana mun tsara abubuwa da dama fiye da yadda muka saba shiryawa a baya domin kuwa a bikin na bana akwai jawabi na musamman wanda tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, wato Farfesa A. Rasheed, zai gabatar. Bayan shi kuma akwai sauran manyan baƙi da su ma za su gabatar da nasu jawabin.”

Ya ƙara da cewa, “Bayan haka kuma kamar yadda na faɗa maka akwai sabbin abubuwa. To a wannan za mu gabatar da sabon littafin da na rubuta mai suna ‘A Gentle Breeze” wanda yake ƙirƙirarren labari ne na Turanci.

“Ka san a baya an san ni da littattafai da dama na Turanci, amma duk na koyar da adabin Turanci ne. A wannan lokacin ne na rubuta ƙirƙirarren labari. Don haka ka ga wannan ya zamar da taron na daban.

“Sannan kuma akwai fim ɗin Turanci mai suna ‘Jamilar Jammaje’, wanda shi ma za a haska shi a wajen taron.

“Shi fim ɗin ya zo da wani salo na koyar ɗalibai yadda za su koyi Turanci ne, duk da yake wasu sun ɗauka fim ɗin an yi shi ne a kan Makarantar Jammaje, to amma ba haka abin yake ba. Shi fim ɗin an shirya shi ne a kan wata ɗaliba da ta shiga Makarantar Jammaje, kuma a ƙarshe ta ce ita a rinƙa kiran ta da Jamilar Jammaje.

“Amma dai fim ɗin ya ginu a kan wayar wa da ‘yan makaranta kai tunda idan ɗalibi ya zo makaranta, yana buƙatar ka zaunar da shi ka wayar masa da kai a kan yadda zai ci nasara a makaranta.

Kabiru Musa Jammaje tare da Nasiru B. Muhammad, darakta da jaruman fim ɗin ‘Jamilar Jammaje’ 

“To shi abin da fim ɗin ya ƙunsa kenan.

“Kuma baya ga haka akwai mawaƙa da za su zo su baje kolin fasahar su, kamar su Mudassir Ƙasim, Sadi Sidi Sharifai, Abubakar Sani, Ado Gwanja da dai sauran su.

“Kuma za mu gabatar da taron ne a ranar 26 ga Disambar nan da muke ciki.

“Kamar yadda aka saba, ɗaliban makarantar Jammaje Academy za su halarta daga rassan makarantar da muke da shi 35 a duk faɗin ƙasar nan, kuma ban da ma ‘yan makarantar har ma waɗanda za su zo su kalla, za su fahimci irin abubuwan da ya kamata su yi idan sun shigo makarantar.”

Loading

Tags: adabiJammaje AcademyKabiru Musa Jammajetaron shekaraTuranci
Previous Post

Islam ɗiyar marubuci Indabawa ta yi saukar Alƙur’ani

Next Post

Ba zan iya misalta murna ta kan karar da aka nuna mini a bikin ƙanwa ta Sa’adatu ba, inji jarumar Kannywood Raihan Ƙamshi

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post

Ba zan iya misalta murna ta kan karar da aka nuna mini a bikin ƙanwa ta Sa'adatu ba, inji jarumar Kannywood Raihan Ƙamshi

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!