ƊIYAR marubuci Ibrahim Muhammad Indabawa, wato Hauwa Ibrahim (Islam), ta yi saukar karatun Alƙur’ani mai girma.
A jiya Lahadi aka yi taron saukar a gidan marubucin da ke Sharaɗa, Kano.
Islam ta yi haddar Alƙur’ani ne a makarantar Islamiyya ta Isyaka Rabi’u da ke unguwar Sani Mainagge, kuma an yi taron saukar tare da sauran ‘yan’uwan ta ɗalibai na makarantar.
‘Yan’uwa da abokan arziki da dama sun halarci gidan Indabawa domin taya shi murna.


Malam Indabawa yana ɗaya daga cikin manyan marubuta da suka daɗe suna bayar da gudunmawa a rubutun littattafan Hausa kuma shi ne Jami’in Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Jihar Kano.
![]()







