• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tarayya ta umarci a tura waɗanda haɗarin tankar mai ya shafa a Suleja zuwa manyan asibitoci

by WAKILIN MU
January 19, 2025
in Nijeriya
0
Gwamnatin Tarayya ta umarci a tura waɗanda haɗarin tankar mai ya shafa a Suleja zuwa manyan asibitoci

Minista Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai Alhaji Mohammed Idris, da Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Nentawe Yilwatda, da sauran jami'ai a Suleja

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta bayar da umarnin gaggawa na a tura mutanen da suka jikkata a haɗarin fashewar tankar man fetur da ya faru a Suleja, Jihar Neja, daga Asibitin Suleja zuwa manyan asibitoci domin samun ingantacciyar kulawar lafiya cikin sauri.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai Suleja a ranar Lahadi.

Idris ya jagoranci wata tawaga daga Gwamnatin Tarayya, ciki har da Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Nentawe Yilwatda, domin tantance halin da ake ciki da kuma miƙa ta’aziyyarsu ga Gwamnatin Jihar Neja da mazauna yankin bisa hatsarin da ya faru a Dikko Junction.

“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana cikin matuƙar jimami kan wannan mummunan al’amari. Ya umurce mu da mu zo nan don ganin halin da ake ciki. Mun zagaya ɗakin masu jinya, kuma mun ga waɗanda ke cikin mummunan hali. Muna nan ana duba su, amma abin takaici, ɗaya daga cikinsu ya rasu. Wannan shi ne mutum na takwas da ya rasu sakamakon wannan hatsari. Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da cewa an yi gaggawar tura waɗannan mutanen da suka jikkata zuwa manyan asibitoci,” inji Idris.

Idris yana jajanta wa dandazon jama’a a lokacin ziyarar

Ministan ya yaba da gaggawar Gwamnatin Jihar Neja wajen bayar da taimakon gaggawa ga waɗanda suka jikkata.

Yayin da yake bayyana damuwarsa kan yawaitar fashewar tankar man fetur a ƙasar, inda mutane sama da 265 suka rasa rayukansu a cikin watanni biyar, Idris ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Tinubu ya kafa kwamiti domin bincikar musabbabin faruwar waɗannan al’amura da kuma samar da mafita don hana faruwar hakan a gaba.

“Shugaban ƙasa yana cikin damuwa sosai game da abin da ya faru. Ya kafa kwamitin bincike na musamman don gano musabbabin waɗannan abubuwan. A cikin watanni biyar da suka gabata, mun fuskanci manyan haɗura huɗu: ɗaya tsakanin Ibadan da Ife, wani a Agaie, Jihar Neja, inda mutane 48 suka rasa rayukansu, wani kuma a Jihar Jigawa inda mutane 144 suka mutu, sannan wannan a Suleja inda kusan mutane 80 suka mutu. Idan aka haɗa yawan waɗanda suka rasa rayukansu, sama da mutane 265 ne suka mutu a irin waɗannan haɗurra.

Wurin da haɗarin ya faru

“Kwamitin da aka kafa, wanda ya ƙunshi manyan ma’aikatu da hukumomi kamar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, NEMA, FRSC, NUPRC, da NARTO, zai binciki musabbabin haɗurran tare da bayar da shawarwari don hana sake faruwar su,” inji Idris.

Ministan ya ce, a bisa umarnin da Shugaban Ƙasa ya bayar kwanan nan, Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) za ta ƙara himma wajen wayar da kan jama’a kan haɗarin kwasan man fetur daga tankokin mai da suka yi hatsari domin hana aukuwar irin waɗannan al’amura nan gaba. Ya yi tir da wannan ɗabi’a, yana mai bayyana ta a matsayin abin da ba za a yarda da shi ba.

Tawagar ta fara kai ziyara ta jaje ga Sarkin Suleja, Alhaji Auwal Ibrahim, sannan ta ziyarci waɗanda suka jikkata a Asibitin Suleja da wurin da haɗarin ya faru.

Sauran waɗanda suka kasance a tawagar har da Daraktocin Janar na Gidan Talabijin na Nijeriya (NTA), Abdulhamid Dembos; Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Baba Ndace; da Rediyon Tarayya na Nijeriya (FRCN), Mohammed Bulama.

Loading

Previous Post

Mawaƙiya a Kannywood, Ummi BY, ta yi rashin mahaifi

Next Post

Mahaifin jarumin Kannywood, Baba Ari, ya kwanta dama

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Mahaifin jarumin Kannywood, Baba Ari, ya kwanta dama

Mahaifin jarumin Kannywood, Baba Ari, ya kwanta dama

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!