ALLAH ya yi wa mahaifin jarumin barkwanci a Kannywood, Alhaji Aminu Aliyu, wanda aka fi sani da Baba Ari rasuwa.
Alhaji Aliyu Mika’il Isma’il Adamu Wudil ya rasu ne a jiya Asabar, 18 ga Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 2:30 na dare, a asibitin Nassarawa da ke Kano, bayan ya sha fama da jinya ta kusan tsawon shekara shida.
An yi jana’izar sa a gidan sa da ke Haure Gidan Murtala, Ƙofar Nassarawa, kusa da kamfanin motocin United, kan Titin BUK, cikin birnin Kano, da misalin ƙarfe 9:30 na safe.
Daga nan aka kai shi gidan sa na gaskiya da ke Maƙabartar Ɗandolo da ke Goron Dutse.
Dattijon, mai kimanin shekaru 120, ya rasu ya bar mata ɗaya, Malama Hauwa, da ‘ya’ya 18 – maza 10, mata 8 – da jikoki da tattaɓa-kunne 220.
Wasu daga cikin ‘yan fim da suka halarci jana’izar sun haɗa da Abba El-Mustapha, Jamilu Roja, Abdul Amart, Malam Mansur Kwaram, Auwal B.B. Hotoro, Rabi’u Daushe, Alhassan Kwalle, Aminu Acid, Hamza Dogo, Hamisu Gamu, da Mustapha Bakiki.
Malamai da suka halarta kuma sun haɗa da Sheikh Ibrahim Khalil, Sheikh Ahmad Imam Buhari, Malam Nura, Malam Ƙaribullah na Ƙofar Ruwa, Sheikh Hadi Imam, Sheikh Mustapha Imam da Sheikh Aliyu Sise.
Waɗanda suka kira a waya sun haɗa da Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Ali Isa Jita, Bello Muhammad Bello, Haruna da Hamza Talle Maifata, Ahmad Sha’awa, Mustapha Naburaska da Hauwa Waraka.
Allah ya jaddada rahama a gare shi.
![]()







