• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Illar ƙunzugu da tsumma, daga Hadiza Nuhu Gudaji

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
April 7, 2020
in Nijeriya
0
Hajiya Hadiza Nuhu Gudaji a bakin aiki

Hajiya Hadiza Nuhu Gudaji a bakin aiki

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
HAJIYA Hadiza Nuhu Gudaji mace ce wadda ta yi wani babban yunƙuri a kwanan nan na wayar da kan mata game da illar da ke tattare da yin ƙunzugu da tsumma a lokacin al’adar su.
 
Don cimma wannan burin, Hadiza, wadda fitacciyar marubuciyar littattafai ce, ta kafa gidauniya mai suna ‘Wipe Away Kunzugu’ wadda ta himmantu wajen shiga lunguna da saƙo-saƙo, musamman ma a karkara, don yin wannan yekuwa. Kuma ta shiga karkara ne saboda a can ne ake ganin matsalar ta fi zama ruwan dare.
 
Mujallar Fim ta tuntuɓi Hajiyar domin samun ƙarin bayani dangane da manufar gidauniyar tata, da nasarar da aka fara samu da kuma ƙalubalen da su ka fuskanta.
 
Hajiya Hadiza Nuhu Gudaji ta fara ne da bayyana mana dalilin kafa gidauniyar. Ta ce: “Ita dai wannan gidauniyar, na ƙirƙire ta ne domin wayar da kan mata, kuma wannan ya samo asali ne a sakamakon karance-karancen da na yi, na ga irin ƙalubalen da mata su ke samu ta fuskar lafiya da cututtukan da ake ɗauka daga wannan tsumma da mata su ke yin ƙunzugu da shi.
 
“Wannan ya zaburar da ni, na ga ya kamata na ga na yi wani hoɓɓasa ta wannan ɓangaren.
 
“To ina tsaka da wannan binciken sai Allah ya kai ni wani ƙauye. Ina zaune, sai na ga wata mace wai ta zo wajen faccalar ta wai ta ara mata tsumma.
 
“To wannan abin ya ƙara zaburar da ni, don haka na ga lallai ya kamata na yi wani abu cikin gaggawa, don haka na samar da gidauniyar tare da bayar da taimakon gaggawa da kuma wayar da kan mata da su ke yin wannan ƙunzugu ɗin. 
 
“Kuma ka sani, ba fa wai matan ƙauye ne kawai su ke yin wannan ƙunzugu ɗin ba, har na cikin gari akwai masu yi. Don haka matsala ce mai girman gaske.”
 
Mun tambaye ta menene ma ƙunzugun da ta kafa gidauniyar yaƙi da shi?
 
Sai ta ce, “Ƙunzugu ana nufin tsumma da mata su ke yin amfani da shi lokacin al’ada. Kuma mata masu yawa a yanzu su na yin amfani da shi birni da ƙauye.
 
“Don haka ne na ƙudiri aniyar yaƙi da shi.
 
“Kuma shi wannan tsumma, idan za ka yi yaƙi da shi, to mata haka kurum ba za ka je ka ce da su su daina yin amfani da shi ba, bayan ba ka ba su madadin sa ba. Don haka ne sai na ɗauki aniyar bi ƙananan hukumomi ina wayar musu da kai tare da ba su wanda za su yi amfani da shi a maimakon tsumma. 
 
“Kuma ba kawai ana raba musu ba ne, a’a, sai an yi musu bayanin yadda ake yin amfani da shi, yadda idan har abin ya shige su to da kan su za su daina yin amfani da shi wannan tsumma domin lafiyar jikin su.”
 
Shugabar gidauniyar ta yi bayani kan irin nasarar da ta fara samu daga lokacin da ta fara wannan babban aikin.
 
Ta ce: “To gaskiya na samu nasarori da dama, don kuwa mata da yawan gaske sun amfana da kayan da mu ka kai musu, sannan kuma sun ƙaru da ilimin da mu ke ba su dangane da wayar musu da kai da mu ke yi a kan illar ƙunzugu da tsumma.
 
“Kuma alhamdu lillah, maigida na, Nuhu Gudaji, shi ne ƙashin bayan samun nasarar domin shi ne ya ke ba ni duk wata gudunmawa tare da ƙwarin gwiwa har aka samu waɗannan nasarorin.”
 
Dangane da matsaloli kuwa, cewa ta yi: “Akwai matsala ta ƙarancin abin da za mu raba wa su matan idan mun wayar musu da kai, don wani lokacin idan mun tara matan mun yi musu jawabi, to abin da za mu raba musu sai ya zama bai wadace su ba. 
 
“Amma dai ta ɓangaren jawabin, duk su na ƙaruwa domin mu na tafiya ne da mata masana a kan harkar lafiya su na yi musu jawabi. 
 
“Don haka babbar matsalar mu abubuwan da za mu raba musu, su ne su ke yi mana ƙarancin.”
 
Daga ƙarshe ta yi kira ga mawadata da sauran jama’a da su ma su shigo su bada tasu gudunmawar domin kawar da ƙunzugu da tsumma da mata ke yi, domin kuwa duniya yanzu ta yi cigaban da ya kamata mata su daina yin amfani da tsumma a lokacin al’adar su.
Hadiza Nuhu Gudaji tare da membobin gidauniyar ‘Wipe Away Kunzugu’ riƙe da ƙyallen kamfen ɗin wayar da kan mata

Loading

Previous Post

Dokar koronabairus: Kotu ta hukunta jaruma Funke Akindele

Next Post

Gwamnatin Kano ta tsaida shirin ‘Kwana Casa’in’ da na ‘Gidan Badamasi’

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Fostar 'Kwana Casa'in', zango na uku ... wanda aka fara ran Lahadi

Gwamnatin Kano ta tsaida shirin 'Kwana Casa'in' da na 'Gidan Badamasi'

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!