• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Kano ta tsaida shirin ‘Kwana Casa’in’ da na ‘Gidan Badamasi’

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
April 7, 2020
in Labarai
0
Fostar 'Kwana Casa'in', zango na uku ... wanda aka fara ran Lahadi

Fostar 'Kwana Casa'in', zango na uku ... wanda aka fara ran Lahadi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
GWAMNATIN Jihar Kano ta umarci tashar talbijin ɗin nan mai farin jini ta Arewa24 da ta dakatar da nuna wasu shirye-shiryen dirama masu dogon zango guda biyu da ta ke nunawa, wato ‘Gidan Badamasi’ da kuma ‘Kwana Casa’in’.
 
Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta jihar ce ta aika wa gidan talbijin ɗin da umarnin a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 7/4/2020.
 
Shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), shi ne ya rattana hannu a kan takardar.
 
Dakatar da waɗannan finafinan ya faru ne saboda hukumar ta ce ba ta duba su ba ake haska su.
 
Hukumar ta ce ƙin ba ta wasannin domin ta tace su ya saɓa wa dokar ta.
 
Ta nemi a dakatar da haska su har zuwa lokacin da aka cika ƙa’idar ta.
 
Su dai waɗannan finafinai biyu, su na da ɗimbin masu kallon su a duk faɗin duniya saboda tasirin su ga masu kallo. 
 
A yanzu babu wani wasan talbijin da ake kallo a arewacin Nijeriya da duk inda ake jin Hausa kamar su. 
 
A cikin wannan satin ne aka shiga zango na biyu na shirin ‘Kwana Casa’in’, to amma tun da aka fara nuna shi jama’a su ka fara yin ƙorafi dangane da yadda salon sa ya canza.
Takardar da Hukumar Tace Finafinai ta tura wa Arewa24
Mujallar Fim ta fahimci cewa da man ko a can baya ana ganin kamar shirin ya na tona asirin gwamnati ne, don haka ake ganin babu mamaki idan gwamnatin Kano ta yi amfani da hukumar tace finafinan domin a dakatar da shi. 
 
Mujallar Fim ta tuntuɓi wani jami’in Arewa24 ya furta wani abu a kan wannan abu da ya faru, sai ya ce ba hurumin sa ba ne amma hukumar gidan ce za ta ce wani abu.
 
Ya zuwa lokacin wallafa wannan labari dai hukumar gidan talbijin ɗin ba ta ce komai ba dangane da wannan dokar da aka ƙaƙaba mata.
 
Abin da jama’a su ka zuba ido su gani shi ne yadda wannan doka za ta yi tasiri a kan gidan talbijin ɗin, wanda ake ganin kamar ya fi ƙarfin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.

Loading

Previous Post

Illar ƙunzugu da tsumma, daga Hadiza Nuhu Gudaji

Next Post

Baba Ari ya samu tagwaye

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Baba Ari, murmushi har kunne, tare da tagwayen sa da wani yayan su

Baba Ari ya samu tagwaye

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!