SABUWAR Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta ɗaya, ta Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Hajiya Ummu Salma Inuwa Fulani, ta ajiye muƙamin ta.
Hajiya Ummu Salma ta sanar da ajiye muƙamin na ta ne a cikin guruf ɗin ƙungiyar na manhajar WhatsApp, a daren jiya Lahadi, 16 ga Fabrairu, 2025 da misalin ƙarfe 10:37.
A sanarwar, Hajiya Ummu Salma ta ce, “Assalamu alaikum. Suna na Hajiya Ummu Salma Inuwa Fulani (P.R.O 1). Ina mai ba ku haƙuri a kan rashin ji na da ba ku yi na tsawon lokaci.
“Wannan ya faru ne saboda yanayin ayyuka na da yawan tafiye-tafiye da na ke yi, ba na samun lokacin gudanar da ayyuka na na PRO 1 ta wannan ƙungiyar.”
Ta ƙara da cewa, “Ina mai neman afuwan ku da kuma sanar muku da cewa na sauka daga wannan kujera ta PRO1. Ina muku fatan alkhairi da samun nasara.”
Hajiya Salma tana ɗaya daga cikin sababbin shugabannin MOPPAN, reshen Jihar Kaduna, wanda Malam Murtala Aniya yake jagoranta.