• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tarayya tana goyon bayan shirin fim kan tarihin shekaru 25 na dimokiraɗiyyar Nijeriya

by WAKILIN MU
March 14, 2025
in Nijeriya
0
Gwamnatin Tarayya tana goyon bayan shirin fim kan tarihin shekaru 25 na dimokiraɗiyyar Nijeriya

Daga hagu: Minista Idris tare da Shugaban IPAC na ƙasa, Honourable Yusuf Ɗantalle, a lokacin ziyarar a yau a Abuja

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta bayyana shirin ta na ba da goyon baya ga samar da wani shirin fim mai nuna tarihin shekaru 25 na dimokiraɗiyyar Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Majalisar Tuntuɓa ta Jam’iyyun Siyasa, wato Inter-Party Advisory Council (IPAC), a ranar Juma’a a Abuja.

Ministan ya bayyana fim ɗin, wanda IPAC ce ta yi tunanin a shirya shi, a matsayin muhimmin tarihin tafiyar da dimokiraɗiyyar Nijeriya ta yi a cikin shekaru 25 da suka gabata.

Ya ce fim ɗin tarihin zai nuna nasarori, ƙalubale, da darussan da aka koya a wannan tafiya.

Ya ce: “Na yi farin cikin ganin ƙoƙarin da IPAC da shugabannin ta suke yi wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya, musamman ta hanyar fim ɗin wanda zai zama wata muhimmiyar shaida ta tarihi, domin girmama jaruman siyasar ƙasar mu da kuma nuna jajircewar Nijeriya a harkar dimokiraɗiyya. A kan haka, Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, za ta goyi bayan shirya wannan fim na musamman.”

Ya jinjina wa IPAC kan jajircewar ta wajen cigaban dimokiraɗiyya tare da jaddada muhimmancin haɗin kan jam’iyyun siyasa bayan zaɓe domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da cigaba.

“Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana goyon bayan a yi gasa mai kyau a siyasa, domin dimokiraɗiyya tana bunƙasa ne idan ana samun hamayya mai ma’ana da haɗin kai bisa muradin ƙasa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyun siyasa ba,” inji Idris.

Ya ƙara da cewa ɗorewar tsarin dimokiraɗiyya tana buƙatar haɗin gwiwa daga kowane ɓangare.

Ya ce: “Jam’iyyun siyasa su ne ginshiƙin dimokiraɗiyya; kuma yayin da hamayya take da muhimmanci a lokacin zaɓe, dole ne mu haɗa kai bayan haka don gina ƙasar mu.

“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda babban ɗan dimokiraɗiyya ne, yana mutunta gasa mai tsafta, amma yana kuma fifita haɗin kai da cigaban ƙasa.”

Minista Idris yana ganawa da shugabannin IPAC a lokacin ziyarar

Shugaban IPAC na ƙasa, Honourable Yusuf Ɗantalle, ya ce shirin fim ɗin tarihin zai bayyana cigaban da aka samu a fannonin gina ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da haɗin kan al’umma.

Ɗantalle ya ce: “Fim ɗin, a matsayin wani muhimmin tarihin ƙasa, zai mayar da hankali kan matasa, musamman ‘yan zamani (Gen Z), domin ya zama wata hanyar ilmantarwa da haɗe kan ‘yan ƙasa kan tafiyar dimokiraɗiyyar Nijeriya. Fim ɗin zai ƙunshi fitattun jaruman Nollywood kuma za a shirya shi da na’urori na zamani domin ya dace da matakin inganci na duniya.”

Daga cikin shugabannin IPAC da suka halarci taron akwai Mataimakin Ciyaman ɗin IPAC na Ƙasa Dipo Olayokun, da memba a majalisar, Cif Dan Nwayanwu, da Sakatare na Ƙasa, Maxwell Mabudem.

Shugabannin IPAC tare da Minista Idris bayan zaman da suka yi

Loading

Tags: Honourable Yusuf ƊantalleInter-Party Advisory Council IPACMohammed Idris
Previous Post

Cewar Minista Idris: Wata rana za a yi wa gwamnatin Tinubu sambarka

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta jaddada ƙudirin kare ‘yancin faɗin albarkacin baki da ‘yancin ‘yan jarida

Related Posts

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya tana goyon bayan shirin fim kan tarihin shekaru 25 na dimokiraɗiyyar Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta jaddada ƙudirin kare ‘yancin faɗin albarkacin baki da ‘yancin ‘yan jarida

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!