• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

by ABUBAKAR IBRAHIM
June 13, 2025
in Nijeriya
0
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya tana ɗaukar manyan matakai domin farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya, dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari, da kuma ƙarfafa dimokiraɗiyya a ƙasar.

A wata hira ta musamman da ya yi da mujallar Forbes Africa yayin bikin Ranar Dimokiraɗiyya, Ministan ya bayyana cewa manufofin sauyi na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur da daidaita tsarin canjin kuɗi, suna daga cikin manyan sauye-sauye a tarihin tattalin arzikin Nijeriya na baya-bayan nan.

Ya ce: “Waɗannan wasu matakai ne masu wahala da dole ne a ɗauka. Sun jawo wahalhalu, amma kamar jirgin sama da ke tasowa, yanzu mun fara samun daidaito. Bankin Duniya ya tabbatar da dawowar cigaban tattalin arzikin mu da ba a gani ba fiye da shekaru goma.”

Da yake magana kan muhimmancin bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, Idris ya ce wannan ba lokacin murna kaɗai ba ne, har ma lokaci ne na nazari kan cigaban ƙasar wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da farfaɗowar tattalin arziki.

Ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur wajen gina muhimman ababen more rayuwa, ciki har da manyan tituna guda biyu da za su haura kilomita 1,700, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗa yankuna daban-daban.

Ya ce: “Manufar ba wai haɗa yankuna ba ce kawai, amma samar da damarmakin tattalin arziki.

“Nijeriya na ƙoƙarin komawa kan sahihiyar hanyar ta. Tana sake zama ƙasa mai daraja a idon duniya.

“Martabar da Nijeriya ke da ita a baya tana dawowa sannu a hankali. Masu zuba jari suna samun ƙarin ƙwarin gwiwa a ƙasar.”

Ya ƙara da cewa sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata sun wuce batun tattalin arziki kawai, domin suna gina tushe ne na cigaba mai ɗorewa, raba dama ga kowa, da ƙarfafa gaskiya da riƙon amana.

Loading

Tags: ForbesAfricaGwamnatinTinubuMohammed IdrisRanar Dimokiraɗiyya
Previous Post

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

Next Post

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!