GWAMNATIN Tarayya ta bayyana cewa ranar Litinin, 31 ga Maris da Talata, 1 ga Afrilu, 2025 su ne ranakun hutun Ƙaramar Sallah.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayar a madadin Gwamnatin Tarayya a ranar Laraba.
Ministan ya taya dukkan al’ummar Musulmi murnar kammala azumin Ramalana lafiya.
Haka kuma Dakta Tunji-Ojo ya yi kira ga Musulmi da su rungumi halayen juriya, tausayi, alheri da zaman lumana, kuma su so juna, da yafiya da haɗin kai domin gina al’umma mai zaman lafiya.
Ya yi fatan a yi shagulgulan Sallah lafiya.
![]()






