ALI Nuhu ya aika da saƙon godiya ga dukkan mutane da ƙungiyoyi da su ka yi masa gaisuwa kan rasuwar mahaifin sa.
Dattijo Nuhu Poloma ya rasu ran Litinin a babban asibitin tarayya da ke Gombe bayan ya yi fama da rashin lafiya na ɗan taƙaitaccen lokaci.
Shekarun sa 79.
Ɗimbin ‘yan fim da mutanen da ba ‘yan fim ba sun yi ta tura saƙon ta’aziyya ga Ali ta hanyar soshiyal midiya, yayin da wasu kuma su ka kira shi a waya, wasu kuma su ka je da kan su har gidan su Alin a Gombe, su ka yi masa gaisuwa.
Ali ya gode wa kowa da kowa ta hanyar taƙaitaccen saƙon musamman da ya tura a shafukan sa na soshiyal midiya.
A saƙon, shahararren jarumin na Kannywood da Nollywood ya rubuta cewa: “Ni da ‘yan’uwa na mu na miƙa saƙon godiya ga dukkan waɗanda su ka yi mana ta’aziyyar mahaifin mu da ya rasu. Mun gode, Allah ya saka da alheri. Na gode da soyayya da ƙaunar da na samu daga gare ku baki ɗaya. Allah ya bar zumunci.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa ban da Ali, wani fitaccen ɗan marigayin shi ne Dakta Kabiru Nuhu Poloma, wanda a zaɓen 2019 ya yi takarar zama sanata daga mazaɓar Gombe ta Kudu a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC amma bai cimma nasara ba.
