• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

by ABUBAKAR IBRAHIM
June 4, 2025
in Nijeriya
0
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

Minista Idris a tsakiyar 'yan tawagar Cibiyar Kula da Lafiya da Hanyoyin Magance Matsalolin Abinci (C-WINS) a lokacin ziyarar a ofishin sa a Abuja

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta yi alƙawarin tallafa wa kamfen na ƙasa da za a gudanar don yi wa yara rigakafi daga cututtukan ƙyandar jamus (wato measles-rubella), wanda ake shirin farawa a watan Oktoba na bana.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a yayin da tawagar Cibiyar Kula da Lafiya da Hanyoyin Magance Matsalolin Abinci (C-WINS) ta kai masa ziyarar ban-girma a ofishin sa a ranar Talata.

Ministan ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar wajen kula da lafiyar jama’a da kare lafiyar yara, yana mai tabbatar da cewa ma’aikatar sa za ta mara baya wajen faɗakar da jama’a domin tabbatar da nasarar wannan yekuwar.

Ya ce: “Kun zo inda ya dace. Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai tana aikin ta ne don tallafawa da kuma bunƙasa irin waɗannan shirye-shiryen.

“Za mu yi aiki tare da ku da hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar, ciki har da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da kuma kafafen yaɗa labarai na gwamnati, domin tabbatar da cewa ’yan Nijeriya sun samu cikakken bayani game da haɗarin cutar ƙyandar jamus da kuma muhimmancin rigakafin.”

Ministan ya bayyana gabatarwar da C-WINS ta yi a matsayin mai motsa zuciya kuma mai cike da ƙarin haske.

Ya ce: “A yau na koyi abubuwa da dama. Yawancin ’yan Nijeriya, kamar ni kai na, sun san cutar masassarar cizon sauro amma ba su san da ƙyandar jamus da mummunan tasirin ta ba.

“Gaskiya batun cewa za a iya haihuwar yara makafi, kurame ko kuma masu nakasar zuciya sakamakon kamuwa da ƙyanda daga uwa a lokacin ɗaukar ciki babbar masifa ce da ya kamata mu haɗa kai mu daƙile ta.”

Ya ƙara da cewa ma’aikatar za ta haɗa hannu da sauran hukumomin da suka dace wajen tsara saƙonnin faɗakarwa da shirye-shiryen ilimantar da al’umma.

Ya kuma shawarci tawagar da su nemi haɗin kan Majalisar Tarayya domin samun cikakken goyon baya na doka.

Ya ce: “Ba ma so wannan zama ya tsaya nan kawai. Mu mayar da wannan haɗin gwiwa abin da zai ɗore, mai amfani, kuma mai faɗi da tasiri. Rigakafi ya fi magani — kuma wannan fannin ne inda bayani ke ceton rayuka ainun.”

A cikin nata jawabin, jagorar tawagar C-WINS, Dakta Nihinlola Mabogunje, ta jaddada gaggawar wayar da kan jama’a kafin lokacin fara kamfen ɗin.

Ta gabatar da cikakken bayani kan muhimmancin rigakafin daga cututtukan ƙyandar jamus fata, musamman a matsayin da Nijeriya ke da shi wajen yawaitar waɗannan cututtuka.

Dakta Mabogunje ta bayyana cewa Nijeriya tana da kusan kashi 20 cikin ɗari na dukkan cututtukan ƙyandar da ake samu a duniya, inda yankin Arewa-maso-gabas yake ɗauke da fiye da kashi 60 cikin ɗari na waɗanda abin ya shafa a ƙasar nan.

Dangane da ƙyandar jamus, ta bayyana cewa cutar tana barazana musamman ga mata masu juna biyu, domin kamuwa da cutar a watannin farko na ɗaukar ciki yana iya janyo haihuwar jarirai masu nakasa kamar makanta, kurmancewa ko lalacewar zuciya.

Ta tabbatar da cewa rigakafin da za a yi amfani da shi yana da inganci kuma ba shi da wani haɗari ga lafiyar mutum, tana mai cewa tun tuni ake amfani da shi, fiye da shekaru 50 a duniya, kuma ya ceci rayuka sama da miliyan 94.

Ta kuma yaba da aikin Hukumar NAFDAC wajen tantancewa da amincewa da rigakafin domin amfani da shi a Nijeriya.

Ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta jagoranci faɗakarwar a matakin ƙasa domin kawar da ji-ta-ji-ta da ƙarfafa gwiwar jama’a.

Likita Mabogunje ta ce: “Don cimma burin kashi 95 na yawan masu karɓar rigakafi, muna buƙatar saƙonnin da suka dace, masu sahihanci da kuma daidaito, waɗanda za a isar ta hanyoyin da ’yan Nijeriya suke yawan dogaro da su a kullum.”

A martanin sa, Minista Idris ya umurci jami’an sashen sadarwa na ma’aikatar sa da su yi aiki tare da C-WINS domin ƙirƙirar kayan faɗakarwa da suka dace da al’adun jama’a, waɗanda za a yaɗa ta kafafen watsa labarai na gwamnati da masu zaman kan su a dukkan faɗin ƙasar nan.

Loading

Previous Post

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

Next Post

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

'Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh': Yadda lamarin yake

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!